Chapter Thirty-Six

1.6K 182 125
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!!

A private jet din Marigayi mahaifin Sadiq suka je Dubai.

Yazeed, Nabeeha, Hafsat da yaranta, Faisal, Sadiq, Hanifa da Asma'u.

Gidan Nana Fatima suka fara sauka, anan suka tarar da Jamila da yaranta wanda sunyi sati daya a Dubai. birthday din Asma'u ne ya hana su komawa Ingila, they will return after they celebrate it.

Hanan ce kawai bata iso ba.. Itama tana jirgi a lokacin da suka iso.

Hanifa really enjoyed their company especially because of yadda suke ta nan-nan da ita, Motsi kadan sai Nabeeha (her gynecologist) ta tambaye ta if she is okay ko akwai inda yake yi mata ciwo. Babu shakka dangin su Sadiq are overly nice and she is very lucky to be blessed with inlaws like them.

A nan gidan Nana Fatima suka ci abinci suka huta sannan suka wuce Suite din Daddy da yake Burj al Arab dukda ba su duka suka tafi ba.

Jameela da Hafsat dai zaman su suka yi a gidan Nana Fatima..

Ita kuwa Asma'u dayake tana so ta kasance kusa da Faisal ne tace itama Suite din Daddy zata zauna.. besides she is the celebrant kuma dama a Burj al Arab din za'ayi celebrating birthday din.

Ita kuwa Nabeeha mijinta Yazeed ta bi yayinda Asma'u tayi forcing Hanifa ta bi Sadiq.

A lokacin da suka iso Suite din Daddy kuwa Sadiq yayi expecting Hanifa zata zauna tare da Asma'u tunda dai they have never shared a room together, ita kanta Hanifa tayi tunanin hakan amma Asma'u ta ziga ta akan ta zauna tare da Sadiq coz it will be a good opportunity for her na ta cigaba da executing plan dinta..

Sadiq yana ji yana gani aka bashi daki daya da Hanifa yayinda aka ba su Yazeed daya sai Faisal ya dauki daya sai kuma Asma'u da Hanan will share a room idan ta iso.

Hakan dai bai yi ma Sadiq dadi ba don kuwa bai taba sharing daki da wani ba balle kuma mace... He has got to pretend yet again a gaban 'yan uwan shi!

Ita kanta Hanifa ta kula bai so da zasuyi sharing daki ba amma kuma ya zata yi? she wants to get closer to him and this is surely the perfect way to do that.

Tun a gidan Nana Fatima suka yi akan zasu je su huta kafin qarfe goma na dare inda zasu fito suyi get together har zuwa 12:00am that will mark Asma'u's Birthday.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI AMINU ABDULLAHI ALEIRO SUITE
BURJ AL-ARAB DUBAI

Wuraren qarfe takwas da rabi Hanifa tana tsaye a gaban gadon dakin su tana kallon kayan da ta baza a kan gadon yayinda take qoqarin zaben wanda zata sa..

A wannan lokacin Sadiq baya dakin.. Kai shi tunda aka basu dakin bai shiga ba, Dayake Faisal has been going up and down trying to make sure everything is in order ne yayi offering ya taimaka mishi and they have been on that.

After so much deliberation ne tayi settling for wata long white material shirt da black jeans.. A dalilin tana dan jin sanyi ne ta fitar da wata loose sweater fara..

Daga nan ne ta kwashe duka kayan da ta baza a kan gadon ta wuce da su dressing room. Ko da na bi ta gani nayi tayi shirin wanka sannan ta shiga bathroom.

Wuraren qarfe tara da minti biyar ne ya shigo dakin.. Kai tsaye na ga ya zauna a kan kujera tare da nade qafafuwan shi a cikin kujerar. Riqe yake da wayar shi yana latsawa yayinda na ga kamar yana cikin damuwa.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now