Chapter Fourty-One

1.6K 186 119
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUNZA OIL & GAS NIG LTD
ABUJA-CENTRAL

Zaune take a kan daya daga cikin executive chairs na Conference room din yayinda ta sa mishi idanuwa babu qyaftawa.

Sadiq ne a tsaye yana magana cikin harshen turanci wanda idan kana sauraro zaka rantse wani bature ne yake magana.

Ni kuwa nace ai dole.. mutumin da aka haifa a qasar America ya girma a can!

Gaba daya heads of Units na kamfanin suna zaune sai kuma Faisal da wasu larabawa su hudu wadanda nake kyautata zaton sune baqin kuma new clients din kamfanin.

Hanifa wadda take ta kallon mijin nata sai admiring dinshi take yi yayinda take ta murmushi.. she just cant believe the handsome and good looking man standing inches away from her is her husband.. Babu shakka tana cikin matan da suka yi sa'a a duniya!

Abinda ya qara birgeta shine tunda ya fara bayani bai juya ya kalli slides din da na'urar projector take haskawa a makeken wall na conference room din ba.. he was actually saying everything from his head and the way he was breaking down facts and figures, its evident that he is a professional business analyst..!

Cikin qanqanin lokaci ne yayi ma larabawan bayanin duk wani abinda suke buqatar sani daga wurinshi wanda they were very impressed and satisfied..

Hanifa wadda cikin dan qanqanin lokaci hankalinta yayi nisa bata san har ya gama bayanin shi ba kawai sai ji tayi yace "Mrs Bunza is there anything you want to say to our clients??"

A rude ta kalle shi tace "uhm, sorry??"

Sadiq dai tsokanar ta kawai dama yayi niyyar yi.. Ya kula she was completely lost a kallon shi wanda har Unit heads dinshi sun kula da hakan shiyasa yayi interrupting dinta just to bring her back to reality..

Murmushi yayi yace "I said do you have anything to add??"

Ita kanta ta san tsokanar ta yake yi.. toh me zata ce musu when she is sure he has said it all.. besides ita me ta sani??

Gani nayi ta girgiza kai tana murmushi... ahankali na ji tace 'let's do this Mr Bunza'

Kai tsaye tace "Yes I do"

"Okay Go ahead" ya fada yayinda ya janyo wani file yana qoqarin budewa..

"I love you"

Gaba daya suka fashe da dariya yayinda Sadiq yayi saurin dago kai ya kalle ta yana mamaki..

Kashe mishi ido daya tayi tare da blowing mishi kisses tana murmushi...

Gani nayi ya sa hannu ya cafke yayinda ya shafa qirjinshi daidai inda zuciyar shi take tare da lumshe idanuwa yana murmushi yace "I love you too my Angel"

all of that didn't go unnoticed by everyone...

Gaba dayan su sai dariya suke yi suna ta qus-qus. Babu shakka an samu abin magana yau din. Dama fa tun daga yadda suka shigo kamfanin a yau ake ta qus-qus.. basu taba ganin ogan nasu a irin mood din da ya shigo yau ba.. tabbas a gaida Hanifa don kuwa she has done wonders akan Sadiq!

Faisal ma mamaki ne ya cika shi, wai yau a gaban mutane Sadiq yake zabga soyayya.. Tabbas Hanifa tayi qoqari.. she has completely changed the stone-hearted guy to a big time Romeo... Unbelievable!

"Well, in the absence of anything I think.. "Ya kalli Faisal yace "...we should round up and prepare the documents for signing right?"

Faisal ya girgiza kai yace "yes we should.." ya kalli kowa yace "on this note we've come to the end of this meeting.. thank you all for attending"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now