Chapter Three

1.1K 156 35
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALIYU BUGAJE (PAAPA)??

Alhaji Muhammad Bugaje ya kasance mutumin qaramar hukumar Bugaje ne a cikin garin Katsina. Da shi da mai dakin shi Hajiya Aminatu sun haifi yaro daya kacal, Aliyu.

Aliyu ya taso cikin gata domin kuwa mahaifin shi yana da arziki.. Sana'a ita ta kai mahaifin shi garin Kano wanda a nan garin Kano aka haife shi. Alhaji Muhammad ya kasance yana da kamfani na siyar da Rodi.. a wannan lokacin duk fadin arewa babu kamfanin da suke sayar da rodi mai kyau kamar nashi.. Yayi fice sossai a wannan sana'ar domin kuwa daga qasashen turai yake shigowa da su don haka akwai guarantee na lallai kayan shi masu quality ne.

Aliyu dai tunda ya taso yake son harkar business kamar yadda ya ga mahaifin shi yana yi.. don haka ne ko da ya kammala secondary school dinshi a nan cikin garin Kano sai kawai mahaifin shi ya tura shi qasar America inda ya karanci Business administration a Stanford University.

Aliyu dai bai bar qasar America ba har sai da yayi masters dinshi.. A lokacin da ya dawo ne ya fada kamfanin mahaifin shi.. Sossai ya kawo musu canji a kamfanin tun daga administration na kamfanin har zuwa marketing and customer service. Kasuwan su ta qara budewa sossai domin kuwa ya shigo musu da tsare-tsare da hanyoyin da suka bunqasa yanayin hada-hadar su da customers dinsu.

Har a wannan lokacin siyo Rodi suke yi daga qasashen qetare sannan su siyar... dukda suna samun riba, Aliyu ya zauna yayi analysis ya ga idan suka fara qera rodin da kan su a nan gida Nigeria lallai zasu fi samun riba fiye da yadda suke samu idan sun shigo dasu daga qasashen waje don haka ne ya duqufa research akan how to make this possible.. ya gano qasar China sun fi kowa iya harkar steel Rods don haka ne yayi proposing ma mahaifin shi plan dinshi wanda nan da nan ya amince.

Aikuwa ba tare da bata lokaci ba Aliyu yayi consulting daya daga cikin distributors dinsu na can qasar China din yayinda suka yi mishi marhabun... sun gayyace shi zuwa qasar inda zai shiga wata makaranta da zai samu qarin ilimi- it was more like an engineering school.. Aliyu dai sai da yayi tsawon shekara uku da rabi yana wannan makarantar. Dayake yana da bala'in qwalwa, nan da nan ya shanye komai.

Dayake duk harka ce ta kudi, bayan ya kammala karatun ya samu knowledge akan manufacturing process din ne suka bashi ma'aikata wadanda zasu koma Nigeria tare suyi training ma'aikatan su amma da sharadin zasu dinga biyan su salary da allowances kamar yadda suka buqata..

It was a bit expensive and big capital project toh amma kuma idan suka jure zasu mori abun a nan gaba..

Nan da nan aka zuba ma'aikata graduates wadanda suka samu training mai kyau daga wurin Chinese din.. cikin ikon Allah kafin shekara ta zagayo tuni aiki ya fara with full force. Sai sukayi renaming sunan kamfanin to Bugaje welding rod Manufacturing industry.

A haka dai suka cigaba da kasuwancin su yayinda kamfani yake ta bunqasa.

Aliyu dai tun yana Secondary school yake son wata yarinya a layin su. Aisha ta kasance 'yar gidan Alhaji Malik Zayyad. Asalin shi dai dan qasar Morocco ne wanda aiki ne ya kawo iyayen shi Nigeria har yayi aure a qasar ya haifi yara.

Aisha dai kyakyawar yarinya ce fara sol.. duk gidan ita ta biyo kamarnin mahaifinta don haka ita ce tayi kama da larabawa Morocco sossai saidai tun tana yarinya take fama da ciwon asthma- irin mai qarfin nan. idan ta tashi mata sai tayi kamar zata mutu.. a haka dai ta cigaba da rayuwa under special care har ta girma.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now