Chapter Thirty-Two

1.3K 179 104
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

A yau Monday, Zaune take a kan gadon ta wuraren qarfe bakwai na safe tayi tagumi.

Kamar dai yadda Hanifa tayi insisting, ranar Saturday da daren ta dawo gidan.. Ko da ta dawo ta leqa sashen Sadiq don ta qara bashi haquri ta lallashe shi amma bata gan shi ba kuma Rabi'u ya tabbatar mata da cewar yana nan. Bata tsananta neman shi ba don kuwa bata so ya ga kamar ta takura mishi.. as it is dole ta lallaba shi kamar qwai.

Washegari ranar Sunday ma haka throughout bata gan shi ba kuma har Rabi'u ta qara tambaya yace mata bai fita ba.. it means he is in a hidden place a cikin gidan kenan ko me??? is Sadiq hiding away from her???

Hanifa dai tsakanin shekaran jiya da jiya tayi tunani kala-kala na yadda zata bullo ma al'amarin Sadiq. Another thing is Paapa, she learnt that Paapa shi ya hada auren su purposely don Sadiq ya hora ta kuma ya sake ta afterwards.. tabbas if she had known before she fell in love with Sadiq da ta ji haushi amma a yanzu Paapa yayi deserving a special appreciation from her because it's the best gift da ya taba bata a rayuwa. She wanted to call him amma kuma Sadiq bai bata wayarta ba tukun don haka ne ta bari idan ta karbi wayarta sai ta kira shi...

A yau din ko da ta idar da Sallan asuba ta zauna jiran lokacin tafiyar shi ofis.. ta tabbatar she will see him shiyasa ma bata koma bacci ba!

Tunani kala-kala take yi a game da abubuwan da suke faruwa a rayuwarta.

Hanifa bata taba sa ran cewar lokaci zai zo da zata mace a soyayyar namiji ba, bata taba sa ran lokaci zai zo da tana neman abu amma zai gagareta samu ba.. Soyayyar Sadiq take nema ido rufe amma tana gani kamar bazata samu ba.. She can't give up, atleast not until before nine months dinnan ya wuce!

For only God knows how many times now ta qara shafa cikinta yayinda ta saki ajiyar zuciya.. Ko bata ce komai ba na tabbatar tana sa ma cikin albarka ne coz if not for it da yanzu tana Kano..

Gani nayi ta kalli agogo da sauri sannan ta sauka daga kan gadon tace "I need to get something for him to eat"

Ni kuwa nace me zaki bashi Hanifa.. ni dai na san baki iya komai ba!! ah toh...

Gani nayi ta dauko Hijab din Sallanta ta sanya. Tayi hakan ne don ta rufe nightie din jikinta tunda Sadiq baya so.

Aikuwa tana fitowa daga dakinta ta ga ko ina tsab.. da alama dai anyi aiki, aikin ma irin na professionals dinnan.. Sai qamshi ke tashi daga kowanne lungu na gidan! kenan he has brought in the workers kamar yadda Naana ta umurce shi??

A lokacin da ta wuce zata je kicin kuwa har ta wuce Dinning room sai ta dawo a dalilin abu biyu.. Na daya qamshin turaren shi da ta ji wanda ya tabbatar mata da lallai yana ciki.. Na biyu kuwa muryar mace ta ji tana ta zuba zance kamar ana mata Oral interview..

toh fa..

Aikuwa tana leqawa zuciyarta ta buga a dalilin abinda ta gani..

Zaune yake a kan kujera yana murmushi yayinda wata Farar yarinya kyakyawa sanye cikin kayan Chefs take tsaye a gefen shi tana magana..

Abinci yake ci amma he was listening attentively to the Chef.. Yanayin shi ya nuna cewar he is finding what ever she is saying funny and interesting... Abinda ya qara bata mamaki kuma for the first time ta ga Sadiq yana cin abinci a gidan and from the looks of it, he is enjoying it.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now