Chapter Thirty-Three

1.3K 182 163
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

Zaune suke a ofis din Hafeez wanda ya kasance nashi a da yayinda suke hira.

"I swear bro I still can't believe we bagged the deal.. like are you for real??? more than sati daya fa kenan muna fama da inyamuran nan amma ka ga daga zuwanka kayi musu dalla-dalla nan da nan suka amince... wow, wow, wow. Na san idan Paapa ya ji labari zai yi mamaki sossai"

Asali dai Paapa yayi tafiya zuwa qasar Cameroon a dalilin wani business deal da zai tattauna da wasu clients a qasar.

Tun lokacin da Sadiq ya dawo da martabar Bugaje industries sossai kamfanin yake samun contracts ba a nan Nigeria ba kawai, har daga qasashen Africa.. don haka kasuwa ce ta bude musu sossai. Wannan ne ya sanya Paapa yake yawan tafiye-tafiye.

Tun bayan da Sadiq ya bar kamfanin Hafeez yayi qoqari sossai domin kuwa yana ta bagging ma kamfanin deals masu kyau, yawancin deals din da suke samu a qasashen da Paapa yake zuwa ma duk shine yake samo musu ta online da kuma contacts.. Gaba daya kowanne ma'aikaci na kamfanin yayi doubling efforts dinshi.. it's more like they are all trying to keep the promise they made to Sadiq lokacin da zai bar kamfanin akan they won't let Paapa down and they will strife to make the company become one of the best in Africa.. and yes, they are actually doing a great job.

A yanzu haka dalilin da ya sanya Hafeez ya kira Sadiq, wani deal ne ya samu a wurin wasu inyamurai daga Anambra State.. Kusan sati daya kenan Hafeez yana fama da su don kuwa tun Paapa yana gari tare da shi ake ta qoqarin sealing deal din amma abu ya gagara.. Mutanen suna da son kudi sossai sannan sun qi kwantar da hankalinsu su fahimci cewar Bugaje industries ba iri daya bane da kamfanonin su na kudu da suka saba cudanya da su.. Ko da Paapa zaiyi tafiya ya ce ma Hafeez idan deal din bazai yiwu ba kawai a fasa kowa ya huta amma kuma Hafeez took it as a challenge na lallai he has to find a way to convince them to do business with them.. At the point da ya fara tunanin giving up ne ya tuno Sadiq.

Four days ago da ya kira shi yana Egypt don haka ne yace he should arrange a meeting with them yau and shi kuma he will try and come.

Ma'aikatan Bugaje industries kuwa sai ganin Sadiq suka yi kamar daga sama.. aikuwa ihu suka dinga suna murna. Gaba daya suka taru a hall din qasa suka rufe shi yayinda yake ta tambayan su how they've been and shima ya gaya musu how he is doing.. they were very happy to see him, haka shima he was so happy.. Babu shakka they love him so much.

Da qyar dai ya samu ya lallaba su suka koma bakin aikin su don ya samu damar shiga meeting din da ya zo.

Abin mamaki kuwa ko minti ashirin ba'a yi ba da zama meeting din Sadiq ya fahimtar da inyamuran komai a game da deal din wanda nan da nan suka amince suka yi signing necessary documents and finally Bugaje industries sukayi bagging deal din!

Sadiq wanda yake murmushi yace "ai inyamuran nan ka rabu da su kawai, Shegen son kudi garesu sannan kuma suna son top quality.. lokacin da muka yi taking over Bunza Oil & Gas ni da Faisal we faced alot of problems from them.. we had to sit and study them sossai in order to be able to relate with them smoothly.. but gaskiya mai wuyan shine ka samu kayi convincing dinsu... afterwards, you will enjoy doing business with them. Yanzu ka ga a dalilin wadannan?? zaku samu contracts dayawa from the east... just wait and see"

"kai.. gaskiya suna da wuyan sha'ani.."

"and I am sure zaka iya handling wanda suka fi wannan taurin kai next time.." Sadiq ya fada yana murmushi.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now