Chapter Fourteen

1K 139 39
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ASALIN ABUBAKAR SADIQ BUNZA!

Alhaji Muhammad Bunza asalin mutumin qaramar hukumar Bunza ne a Kebbi state. Yaran shi sun kasance su uku- Sa'ad wanda shine babba, Sai Mariya itace ta biyu sannan Abubakar wanda shine qarami.

Alhaji Muhammad a wannan lokacin ya kasance attajiri don haka ne yaran suka taso cikin gata da wadata.

Sunyi karatun boko da islamiyya mai zurfin gaske.

Sa'ad da Abubakar a turai suka yi karatun su na jami'a. Ita kuwa Mariya dayake mace ce sai tayi nata karatun a nan qasa Nigeria.

Sa'ad wanda a yanzu yara suke kira Big Daddy ya karanci Medicine a qasar Germany. A dalilin bala'in qoqarin shi a wannan lokacin ne babban asibitin Berlin suka bashi automatic appointment inda suka dauke shi a matsayin babban likita. Albashi mai yawa suke biyan shi.. Cikin shekaru shidda ya tara kudade masu yawan gaske. Wannan kudaden ne ya dinga turowa nan gida Nigeria inda aka fara gina mishi wani qaton asibiti a cikin garin Abuja. Dayake harka ce ta kudi, nan da nan aka gama gina asibitin.. aka zuba kayan aiki masu kyau da quality sannan aka dauki ma'aikata, likitoci da nurses first class har daga qasashen qetare. A lokacin da asibitin nashi ya zama ready to start operating ne yayi sallama da Berlin wanda suka yi yarjejeniya akan whenever they need his assistance zasu kira shi.. ya amince da hakan matuqar he is free. A yanzu haka dai Shine mamallakin shahararren asibitin nan da yake cikin garin Abuja mai suna Asokoro District Hospital.. Sa'ad yayi aure a lokacin da ya dawo Nigeria, ya auri matar shi mai suna Rahinatu (Mummy) wadda ta haifa mishi yara guda uku. Jameela, Yazeed da Hafsat

A dayan bangaren kuwa Mariya wadda a yanzu yara suke kira Mom tayi karatun ta a Usman danfodio Univerity inda ta karanci English. Dama tun tana qarama mahaifinta da aminin shi suka yi alqawarin hada yaran su aure (wato ita Mariya da yaron aminin mahaifinta Aminu) Faduwa ce ta zo daidai da zama domin kuwa ko dama Aminu (wanda a yanzu yara suke kiran shi da Dad) yana son Mariya don haka da kan shi ya nemi soyayyarta kuma ya samu. Aminu dai a qasar Ingila yayi karatu inda ya karanci Political science. Bayan ya kammala masters dinshi ne ya dawo gida inda ya fada siyasa. Sossai ake damawa da shi a harkar siyasa, Ba tare da bata lokaci ba kuwa aka yi bikin shi da Mariya tunda dama a lokacin itama ta gama karatun ta. Sun haifi yaran su guda biyu Nana Fatima da Faisal. Bayan shekaru da dama ana damawa da Aminu a harkar siyasa kwatsam sai ranan ya fito takarar gwamnan jihar Kebbi... dayake dai mutumin arziki ne kuma talakawa sun shaida irin qoqarin da yake yi aikuwa kamar wasa ya lashe zaben. Aminu dai sai da yayi shekaru takwas a matsayin gwamnan Kebbi state sannan ya sauka.. daga nan ne ya tattara iyalin shi suka koma Garin Abuja inda harkar siyasar tashi ta koma. Yanzu haka ya riqe muqami kala-kala a cikin gwamnati, har yanzu yana shanawa a cikin gwamnatin qasar nan.

Abubakar kamar yadda kuka sani a Stanford yayi karatunshi a qasar America inda ya karanci Petroleum Engineering. Shima din dai ko da ya gama kamfanin ExxonMobil ne suka bashi aiki.. it's one of the biggest Oil & gas producing company a USA. Dayake Abubakar yana da qwalwa sossai ba qaramin amfani yayi musu ba haka shima ba qananan kudade suka dinga biyan shi ba.. Nan da nan yayi masifar kudi na fitar hankali.. a lokacin da ya nemi barin su ya dawo gida hana shi suka yi.. a tunanin su ma kudin da suke biyan shi ne basu ishe shi ba don haka suka ninka mishi. Mai karatu ba sai na yi maka bayanin irin kudaden da ake samu a bangaren mai ba, musamman a turai wanda in dollars suke biya. kafin a ce kwabo Abubakar ya zama billionaire. Dama tun kafin ya tafi turai karatu yana da budurwar shi mai suna Haleema.. asalin ta bafillatanar Adamawa state ce, aiki ne ya kai mahaifinta Kebbi state. Abubakar dai ganin ExxonMobil sun qi sakin shi ne yayi planning kawai ya dawo a daura mishi aure da Haleema sai ya dauke ta su koma can. A can din ta cigaba da karatu don kuwa dama bata gama ba. Sun zauna a America har tsawon shekaru Ashirin da biyu... tsakanin su da Nigeria sai dai hutu. Sun haifi yaran su guda biyu- Abubakar Sadiq da Asma'u. A lokacin da suka dawo qasar Nigeria ne suka yi settling a Abuja inda ya kafa Oil Producing company dinshi mai suna Bunza Oil & Gas wanda cikin qanqanin lokaci yayi fice ba a Nigeria ba har wasu qasashe na qetare. Kafin ace wani abu gaba daya Nigeria babu state din da bazaka gidajen man shi ba. Bayan 'yan shekaru ne Alhaji Aminu (Dad) mijin Mariya (Mom) wanda yayi zurfi a siyasa yayi mishi hanya aka gabatar da sunan shi a wurin shugaban qasa wani lokacin da za'a nada sabbin ministoci. Kamar da wasa kuwa duk yayi passing interviews dinshi yayinda Senate suka yi approving musamman ganin achievement dinshi a qasar America. Nan da nan aka nada shi Minister of Petroleum na qasa wanda sai da yayi shekaru hudu sannan ya sauka a yayinda aka canza gwamnati. Shekara biyu da rabi da saukar shi ne suka yi accident shi da mai dakin shi akan hanyar su na dawowa daga airport bayan sunyi tafiya zuwa qasa mai tsarki don yin Umrah.. a sanadiyyar wannan hatsarin ne suka rasa rayukan su! Allah ya jiqan su da Rahama.. Ameen.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now