Chapter Twenty-Four

1.2K 147 110
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

Hanifa tana shiga dakinta ta fashe da dariya... Ji nayi tace "ai tunda na gano abinda baka so ka shiga uku, its gonna be a tit for a tat henceforth.. idan ka gaji sai ka sallame ni"

Gaban Vanity Mirror dinta ta tsaya ta daure gashinta sannan ta dauko dan kwalin lace dinta ta daura.. Simple Accessories ta fitar suma ta sanya.. Dukda she decided to go simple sossai tayi kyau, Dama kuwa kyakyawa ce!!

Closet dinta ta koma ta janyo wani qaramin gyale Golden color daga cikin wadrobe dinta sannan ta nufi wurin takalmanta ta dauko heel golden color mai kyan gaske ta sanya

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Closet dinta ta koma ta janyo wani qaramin gyale Golden color daga cikin wadrobe dinta sannan ta nufi wurin takalmanta ta dauko heel golden color mai kyan gaske ta sanya.

Feshe kanta ta qara yi da turaruka sannan ta dauki wayarta ta fito...

Sadiq wanda ya ji motsin fitowarta ko daga kai ya kalleta bai yi ba na ga ya miqe tare da daukar wayoyin shi.. Hanifa ta bi bayan shi tana ta dalla mishi harara har suka fito..

Suna fitowa ta ga wata dalleliyar latest Mercedes-Benz Maybach baqa wuluq tana ta qyalli parked a daidai porch din gidan.. Plate number din motar dauke da BUNZA 007.. da alama dai an dauko ta daga wurin motocin da ta hango ne a parking lot din gidan wanda bazata iya qirga yawan su ba idan ba ta je wurin ba.

Wani driver ne ya fito daga cikin motar ya miqa ma Sadiq key cike da girmamawa yace "sai kun dawo Sir"

Sadiq wanda yayi mishi murmushi yace "thank you Rabi'u"

Da sauri Rabi'un ya zagaya ya bude ma Hanifa yayinda ya russuna yace "Sannu Hajiya"

Hanifa ko kallon shi bata yi ba ta shiga mota.

Aikuwa bata gyara zama ba ta ji Sadiq yace "baki ji ana gaishe ki ba???"

Turo baki tayi bata ce komai ba.

"fita ki amsa shi sannan ki shigo"

Wani irin kallo tayi ma Sadiq amma kuma ta kasa magana.. Babu shakka threat dinshi na jiya ya shige ta.

Fita tayi daga motar ta kalli Rabi'u tace "sannun ka" sannan ta dawo ta shiga motar shi kuma Rabi'un ya rufe.

Aikuwa tana shiga Sadiq yace "idan na qara ji an gaishe ki baki amsa ba I will deal with you"

Hararar shi tayi ta gefen idanuwa yayinda ta cigaba da bin harabar gidan da kallo..

"what a beautiful mansion with an ugly owner" ta fada ta qasan maqoshi.

Ko da suka bar gidan suka hau hanya tafe suke amma sam kamar ba cikin mota suke ba.. Motar is so comfortable.. Ga qamshin humidifier da na turarukan su da suka gauraye da sanyin AC suka bada wani yanayi mai masifar dadi.. Most importantly tuqin Sadiq wanda yake yi cikin natsuwa.. Ita fa dama Hanifa abinda take so kenan, ta shiga mota a tuqa ta, Yanzu haka bata qi suyi ta yawo har gobe ba a cikin garin Abuja..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now