Chapter Thirty-One

1.2K 180 157
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

LATE ALHAJI ABUBAKAR MUHAMMAD BUNZA RESIDENCE-ASOKORO

Zaune yake a kan kujera one-seater na babban falon gidan yayinda yake sauraron Naana wadda take ta masifa...

Hanifa ce zaune kan kujerar da take opposite shi yayinda ta sa mishi idanuwa..

It's been more than three weeks since she last saw him.. Yanzu haka tunda ta sanya mishi idanuwa ta kasa daukewa a dalilin wani bala'in kyau da yayi mata.. Gani tayi ma kamar ya qara kyau da haske. How can she not fall deeply in love with the handsome guy in front of her??

Sadiq dai yau da safe jirgin su ya sauka daga Cairo.. Ko da Rabi'u ya je airport dauko shi ya sanar da shi cewar Hanifa tana gidan Naana. Sadiq yayi mamakin jin haka amma ya basar..

Ko da suka iso gida kuwa sashen shi ya nufa yayi wanka sannan ya kwanta don ya huta.. Da rana bayan Zuhr ya fita ya je Cilantro yayi lunch sannan ya dawo gida..

Bayan Sallan Asr ne Naana ta kira shi a waya tace ya je gidanta tana neman shi.. Ya sani sarai magana zata yi mishi akan Hanifa.. ba tare da yayi mata gardama ba yace zai je bayan Sallan magrib.

".....na ji labarin tun da safe jirgin ku ya sauka kuma ka je gida baka tarar da matarka ba wanda na tabbatar Rabi'u ya fadi maka inda take amma saboda rashin mutunci ka qi ka zo ko?"

Ran Sadiq a bace yace "toh me kike so inyi Naana, ni nace ta zo nan din??"

"Ba kai kace ba.. mu bar wannan maganar for now, meye ke faruwa tsakanin ka da Hanifa??"

"tunda qara ta kawo miki I am sure she must have told you everything.. duk abinda ta fada haka ne kuma kamar yadda na fadi mata idan na dawo sakinta zanyi.. now that I am back zata tattara kayan ta in mayar da ita gidan su"

Hanifa wadda zuciyarta take ta bugawa ce hawaye suka fara wanke mata fuska..

Abinda ta kula shine tunda Sadiq ya zauna a falon bai ko kalli gefen da take ba balle ya kalli fuskarta.. its obvious ma irritating dinshi take yi.

"Babu inda zata je" Naana ta fada cikin masifar da bata taba yi mishi irinta ba

Sossai Sadiq yayi mamakin yadda Naana take yi mishi masifa saboda Hanifa.. Wait why is she even saying Hanifa bazata je ko ina ba when the last time he checked she was dying to leave his house and go back home?? what has changed all of a sudden??

Ran shi a bace yace "saboda me zaki ce haka Naana??"

"Saboda hakan ba daidai bane.. yanzu kai saboda rashin mutunci duk irin amintar da ta kasance a tsakanin mahaifinka da Alhaji Aliyu Bugaje sai kawai ka saki 'yar shi ka mayar mishi saboda wani quest for revenge dinka na banza? kai baka tunanin yadda mahaifin nata zai ji idan ka sakar mishi 'ya??"

"wai Naana what makes you think cewar Paapan nata zai ga rashin kyautawa na ne?? wai baki san tun farko ya bani auren ta don in hora mishi ita bane sannan in mayar mishi da ita???"

"what???" Hanifa ta fada hankali a matuqar tashe yayinda ta miqe tsaye dafe da qirji.

Kenan dama Paapa ne ya sa shi ya aureta don saboda ya hora ta?? afterwards kuma ya sake ta??

Naana wadda ta zama confused ce tace "ban gane shi ya baka ita ka hora ta ba.. how can a father do that to his child??"

Murmushin takaici Sadiq yayi sannan ya fara bata labarin yadda suka yi da Paapa...

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now