Chapter Nineteen

947 136 78
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Kamar yadda aka tsara, Abbu (Hanan's Father) ya zo Nigeria sun hadu da su Big Daddy (Yazeed's father) da Dad (Faisal's Father) da Barrister mijin Hafsat, Yazeed da Faisal sun je Kano neman auren Sadiq.. Paapa da abokanen shi sun karbi baqin nasu cikin karramawa. Dayake dai harka ce ta girma komai anyi shi cikin tsari.. A nan suka nemi a sanya ranar biki Sati biyu kacal...

Paapa ya dan yi mamakin jin sun buqaci ayi bikin so soon amma kuma daga baya sai yayi tunanin qila shi Sadiq din wants to just quickly fulfill his wish ne and send her back kamar yadda ya umurce shi..

Sun jaddada ma Paapa cewar basu buqatar komai na daga kayan daki da sauran su tunda dama ba addini ya tsara lallai sai anyi haka ba.. All necessary formalities were done and it became official- Auren Sadiq da Hanifa nan da sati biyu!

Hankalin Hanifa ya tashi jin cewar an sa ranar bikinta in 2 weeks- bikinta da maqiyin ta SADIQ. Sossai abun ya dame ta.. gaba daya ma ta zama confused.. Tabbas tana da plan din da zata yi executing a gidan Sadiq amma kuma dukda haka jikin ta yayi sanyi... Ko me yasa???

Hanifa dai ta gaya ma su Paapa cewar Sadiq ya bata blank cheque na lefen ta da hidimar biki amma kuma ta gaya musu cewar bata son lefen don haka bazatayi amfani da kudin shi ba..

Shi kam Paapa babu abinda ya dame shi da wannan dukda kuwa yayi mamakin ace yadda Hanifa take da son kashe kudi sannan an bata blank cheque amma ta qi amfani da shi? Unbelievable!!

Could it be a sign na cewar Sadiq ya fara gyara ta kenan tunda a dalilin shi for the first time she has uncountable money at her disposal amma kuma she refuse to spend???

Well, a wurin Paapa dai whatever the case may be, tayi daidai tunda dama auren ba lasting zaiyi ba don haka gwara kar ta kashe mishi kudi a banza (even though deep down within him yana so auren yayi lasting coz he knows Hanifa will never get a good husband kamar Sadiq din)

Mamy kuwa ta lallabe ta ko da kadan ne ayi lefen amma sam ta qi.. Gyaran jikin ma da za'a yi mata cewa tayi bata so, a cewarta wa zata gyara ma jiki bayan ko hannunta bazata taba bari ya taba ba balle....

toh fa!

Kai gaba daya komai na shirye shiryen bikin Hanifa ta qi tayi participating. Mamy da dangin mahaifiyarta su suke ta kidan su suna rawar su..

A bangaren Sadiq ma babu wani abinda yake yi na shirin bikin.. He was so occupied with work da kwata-kwata ya manta cewar zai yi aure.. kai har tafiya yayi a tsakanin wannan lokacin..

Shima dai kamar yadda ya fadi ma Naana baya son wani event don haka kawai da zarar an daura auren shikenan..

Tuni IV na daurin aure ya fita.. ya bi ko ina a qasar Nigeria. Dukda abin low-key ne sai da aka samu 'yan nacin da suka zaqulo hotunan Sadiq da Hanifa suka baza a social media.. tuni suka zama talk of the town..

Kowa yana murnar bikin Sadiq a cikin dangi amma banda Asma'u. Gaba daya ko maganar bikin bata so ta ji balle sunan Hanifa... Ita kuwa Hanan ta zama indifferent about it, a part of her is happy for him and a part is not!! Ta sani cewar tunda ba auren shi zata yi ba bai kamata tayi mishi baqin ciki ba dukda shi din ba son auren yake yi ba..

Ana saura sati daya bikin ne su Jameela da Nana Fatima suka iso Nigeria.

Sossai suka dinga qorafi jin an ce babu event din da za'a yi har a bangaren amarya.. Har kiran Sadiq suka yi suka sanya shi a gaba suna ta masifa amma kuma ya dinga basu haquri..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now