Chapter Five

1K 180 64
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Days later!!

BUGAJE INDUSTRIES
KANO-CENTRAL

A yau kwana uku kenan da Hanifa ta fara aiki a kamfanin mahaifinta.

Kamar dai yadda ta tsara, kwana biyu kawai tayi a Dubai. Sai da Paapa ya qara mata 1million naira saboda qorafin da ta dinga yi. Tayi shopping na kayan sawa masu kyau dukda babu yawa tunda kudin babu yawa.. Hanifa duk yawan kayan da take da su a closet dinta basu ishe ta ba.. kullum burin ta shine ta sa sabon kaya don haka ne kullum tana kan shopping.

Hanifa ta so a bata ofis din Sadiq amma sam Paapa ya qi. Asali dai an bata wani ofis ne a kusa da na Sadiq din tunda dai she will be working in his department.

Paapa ya sa an gyara mata ofis din to her taste dukda dan qarami ne babu laifi an qawata shi da kayan zamani na gani na fada.

Hanifa dai tayi qorafi sossai wanda dai as usual da lallashi Paapan nata ya shawo kanta.

Kamar yadda Paapa ya buqata tayi aiki tare da Sadiq, ta amince. For now ta ajiye dream dinta a gefe, her immediate buri a yanzu shine ta wulaqanta Sadiq din.. she made it her personal mission to screw him a kamfanin.. ta tabbatar babu wanda baya da skeleton a closet dinshi don haka ta qudiri niyyan gano wani abu negative about him that she can use against him and finally idan ta kore shi then she can start working properly in 'her Paapa's Company'

toh fa...

A kwana ukun da ta fara aiki a kamfanin sau daya ta ga Sadiq.. shima tana tsaye a floor dinsu ta hango shi yana fita daga kamfanin.. according to yadda ta ji ana production ne shiyasa almost all important heads na departments din kamfanin suka zama very busy... don haka shi da ita basu hadu one on one ba.

A cikin kwanaki ukun nan da ta fara aiki a kamfanin kuwa ta takura ma ma'aikatan kamfanin.. Hanifa dai komin tsufan mutum idan kayi mata ba daidai ba sai ta wulaqanta ka.. tunda ta zo kowa yake qoqarin yin taka tsan-tsan domin kuwa babu wanda ya shirya barin aiki a sanadiyyar ta.

A yau din dai bata shigo ofis ba sai wuraren qarfe Goma. Tana sane cewar lokacin zuwa aiki a kamfanin qarfe takwas ne kuma ta sani cewar akwai punishment for late coming.. infact babu wani rules and regulations na kamfanin da bata sani ba tunda an bata terms and condition of service na Kamfanin kuma ta karanta.

As usual dai tunda ta shigo ma'aikatan kamfanin suka dinga gaishe ta wanda ko kallo basu ishe ta ba.. tana tafe cikin isa da gadara (wai ita 'yar mai kamfani)

Sanye take cikin wata Black stylish jumpsuit.. tayi masifar kyau a cikin kayan.. sai baza qamshi take yi. Bayan tayi signing-in ta wani e-machine ne tayi proceeding.

 Bayan tayi signing-in ta wani e-machine ne tayi proceeding

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now