Chapter Two

1.4K 178 57
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA- KANO

Wuraren qarfe takwas da rabi na dare Alhaji Aliyu Bugaje wanda aka fi sani da Paapa shine yake zaune a danqareren falon shi tare da matar shi Hajiya Binta wadda aka fi sani da Mamy.

A yau lahadi ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa qasar Italy har tsawon kwana bakwai- he actually went on a business trip.

Kusan awa hudu kenan da dawowar shi amma bai ga 'yar lelen shi ba.

Dayake a gajiye ya dawo sai da yayi wanka yayi salloli ya ci abinci sannan ya huta.

A yanzu haka yana zaune da matar tashi ne suna kallon News yayinda suke hira..

"wai ina Baby ne ban ganta ba tunda na dawo?? ko bata gida ne??" ya tambayi Mamy.

Mamy dai tunda Hanifa ta dawo jiya suka hadu sau daya bata qara ganin ta ba.. a yadda ta gan ta ma ta tabbatar akwai matsala don kuwa tun da ta shigo gidan take ta yi ma masu aiki masifa da fada na babu gaida babu dalili. Toh kuma dama dai idan har tana gidan haka zaman nasu yake, babu mai shiga sabgar wani... saboda dai Hanifa ba yarinya bace mai mutunci.. idan baka riqe girman ka ba duk shekarun ka sai ta karta maka rashin mutunci ta wulaqanta ka a banza don haka ne ma Mamy bata shiga harkar ta ko alama.

Tabe fuska tayi sannan tace "tana nan.. tun da ta shigo jiya ban qara ganin ta ba"

Murmushi yayi sannan ya dauki wayar shi yana dialing lambar ta yayinda yace "Ni na rasa yaushe zan gan ki tare da Hanifa zaune a wuri daya kuna hira kamar yadda kowacce uwa take yi da 'yarta"

Murmushi kawai Mamy tayi bata ce komai ba domin kuwa ta sani cewar hakan ba abu bane mai yiwuwa.

"Hello Babyna where are you ga Paapa ya dawo bai gan ki ba??"

Shiru ya dan yi sannan yayi murmushi yace "Yes I am back my Baby, ina falona"

Daga nan ya kashe waya yana murmushi yace "gata nan zuwa amma fa daga jin muryar ta na tabbatar an taba mun ita... bari dai ta zo mu ji"

Mamy dai tana mamakin yadda Paapa ya sangarta Hanifa haka.. Gaba daya yarinyar bata ganin kowa da daraja dukda yawancin iya shegen da take yi ba a gaban shi bane don haka baya sani amma ai still akwai wasu abubuwan da take yi a gaban shi wadanda yakamata ya dinga tsawata mata but sai kawai yayi over looking...

Hanifa ce ta shigo falon sanye cikin wata rigar bacci in and out pink color. Ta cikin dai gajera ce wadda ta tsaya a gwiwarta sai kuma ta saman wadda take kamar robe doguwa ce har tana jan qasa.. tana sanye da takalmi mai laushin gaske shima pink.. da alama hade yake da rigar baccin. Fuskar ta fayau.. Gashin kanta dogo baqi qirin ya kwanta a kafadarta da bayan ta gwanin ban sha'awa.

In all she looked very beautiful.

Cike da shagwaba ta qarasa wurin Paapan nata ta zauna a gefen shi in between shi da Mamy ta kwanta slightly a jikin shi tayi hugging dinshi very tight tace "Oyoyo Paapa... I missed you very much"

Yana rungume da ita yana shafa kanta yace "I missed you too Baby.. how have you been?? ya examz?? yanzu dai finally kin gama da Oxford ko??"

"Yes Paapa.. Na gama da Oxford"

"toh masha Allah Baby.. welcome back"

"thank you Paapa"

"so tell me ya kike.. what have you been doing tunda kika dawo??"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now