Chapter Twenty-Five

1.1K 150 70
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUNZA OIL & GAS NIG. LTD.
ABUJA-CENTRAL

Zaune suke a tsararren lounge na ofis dinshi suna hira suna lunch.. Sadiq, Faisal da Yazeed

Mai karatu ko da na kalli ofis din Sadiq don in kwatanta muku yanayin shi sai na rasa daga ina zan fara don kuwa komai na cikin ofis dinnan abin kallo ne.. Kamar ofis din wani shugaban qasa.

A yau din dai Yazeed yana off don haka bai je asibiti ba.. Ita kuma Nabeeha anjima da yamma zata koma.

Nabeeha dai jin Yazeed yace zai je Ofis din 'yan uwan nashi ne sai tace mishi she will prepare lunch ya tafi musu da shi...

Ban fadi muku ba.. A rayuwar Nabeeha tana bala'in son dafa abinci, Shiyasa a duk lokacin da take off zaka ga ta zauna ta hada lafiyayyen continental dish ta aika har gidan sirikkan ta..

"Gaskiya Beeha ta iya girki amma fa dukda haka bai kai na sweetheart dina ba.." Faisal ya fada cikin tsokana

Yazeed ya harare shi yace "ai baka isa ba, idan har na Baby na bai kai na Asma'u ba toh sai dai su zo daya.."

"Toh ga Sadiq nan sai ya raba gardama tunda dai ya san taste din abincin su.." Faisal ya fada

Da sauri Yazeed yace "wallahi ban yarda ba, ai na san na qanwar shi zai zaba"

"Saboda dagaske din ya fi dadi ba" Faisal ya fada.

Shi dai Sadiq murmushi kawai yake yi ba tare da yace komai ba..

"Bro gaskiya yakamata ka gayyacemu mu zuwa cin girkin amarya, itama mu ji yadda nata yake" ya kalli Yazeed yace "ko ba haka ba???"

Yazeed yana murmushi yace "gaskiya ne wannan"

Sadiq wanda yake murmushi kai tsaye yace "ita ai bata iya ba.."

Cike da mamaki Faisal da Yazeed suka kalli juna yayinda Faisal yace "ban gane bata iya ba.. wace mace ce zata taso a gidansu ta je gidan aurenta sannan ace wai bata iya girki ba?? toh me ta iya?"

Yazeed wanda yake murmushi yace "kai ka yarda cewar bata iya ba?? idan haka ne how does he manage when ya sallami Chefs dinshi"

"Ooh, Baku yarda ba kenan??? toh shikenan.. I am inviting you for dinner at my house tomorrow idan Allah ya kaimu.. kuma na rantse duk abinda ta dafa sai kun cinye shi don bazaku ja mun asara ba"

Faisal da Yazeed suna dariya yayinda Yazeed ya ce "ai kuwa muna nan zuwa mutumina"

Faisal ya kalli Yazeed yace "wai ban baka labarin abinda mutumina yayi ba jiya a gidan Naana"

Cike da son jin gulma Yazeed yace "tell me"

Sadiq ya danna ma Faisal harara yayinda Faisal din yace "ai ba harara ba, ko me zaka yi sai na fada"

Daga nan fa ya ba Yazeed labarin Yadda Hanifa ta sa Sadiq ya dinga bata farfesu a baki..

"...na rantse maka da Allah Sadiq Romeo ne, idan ka ga yadda ya dinga bata zaka riqe baki. The Sadiq that we use to know wanda baya son soyayya dagaske ba shi bane wannan"

Yazeed yana kwasan dariya ne yace "kace dai arranged marriage ya dawo love marriage"

Sadiq wanda yayi clearing plate dinshi ne ya ajiye akan table ya dauki ruwa ya sha sannan ya miqe yace "idan kun gama ku tashi ku bar mun office.. I have work to do"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now