EPILOGUE

2K 181 148
                                    

7 years later!

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE ASOKORO

A yau Saturday, Wata yarinya na gani zaune a kan daya daga cikin kujerun dinning room na gidan yayinda ta natsu tana kallon wani abu a tablet dinta. Dogon gashin kanta wanda aka yi ma kitson kalba ya rufe gefen fuskarta don haka ban samu ganin fuskar nata ba da kyau amma dai fatar jikinta da na hango tamkar na baturiya saboda tsananin haske.

Mai karatu ko da na matsa ta bayan ta sai na ga tutorials take kallo na Mathematics a uLesson Educational app.

Murza idanuwa na nayi don in qara tabbatar da abinda na gani a tab din. Tabbas Mathematics ne amma kuma wannan maths din da nake kallo ya fi qarfin wannan yarinyar don kuwa idan ban yi kuskure ba maths ne wanda yakamata a koya ma yaro dan JSS 1, ita kuwa duk saurin ta bata wuce primary 3 ba, idan ma ta kai kenan.

Tayi nisa a karatun ta ne biyu daga cikin Maids din gidan Zakiyya da Ramatu suka shigo riqe da breakfast a hannuwan su yayinda suka fara jerawa a kan dinning table din.

Ramatu wadda take qoqarin gyara ma jug na fresh orange juice zama ce tsautsayi ya gifta wanda har yasa ta bige ma yarinyar tablet dinta ta kife..

Aikuwa da sauri yarinyar ta dago ranta a bace...

Hasbunallahu wani'mal wakeel.. abinda na fada kenan da na ga wannan yarinyar.

Kyakyawar gaske, fara sol kamar baturiya.. Da ka ganta zaka gane 'yar Hanifa ce domin kuwa kamar su daya.

"are you mad??" yarinyar ta fada cike da rashin kunya.

Ramatu wadda da alama ta saba da halin yarinyar da sauri ta dauki Tablet din tana qoqarin gyarawa.

"Yi haq..." bata qarasa magana ba ta ji an watso mata ruwan juice a fuska..

"Ayra!!!!!!"

Gaba dayan su suka juya suka kalli bakin qofar inning room din.

Hanifa na gani tsaye a bakin qofar dinning din yayinda ranta yake a matuqar bace..
Mai karatu dukda ranta a bace yake tayi masifar kyau, ta qara haske, tayi 'yar qiba and most importantly sai glowing take kamar wata mai dauke da jaririn ciki.

Tana riqe da hannun wata 'yar qaramar yarinya kyakyawar gaske wadda bazata wuce shekaru uku ba, itama din kama take da Hanifa da Ayra amma bata kai su haske ba.

"what is happening Ayra??? why did you pour the juice on her??"

Ramatu wadda aka yi ma wanka da ruwan juice kuwa tana tsaye tsamo-tsamo cike da takaici yayinda Zakiyya take gefenta cike da tausayin wulaqancin da yarinyar ta yi ma abokiyar aikinta..

"Mummy she pushed my tablet from its stand..."

"shine zaki zuba mata juice a jiki??? ba na hana ki displaying wannan munanan halayen ba?? what are you trying to become Ayra???" Hanifa ta fada yayinda ta qarasa shigowa dinning din.

Ayra tana turo baki tace "Mummy ni fa I don't like these maids.. I will tell Daddy to send them away because they are all stupid..."

"shut up" Hanifa ta fada cikin fadan da bata taba yi mata irin shi ba yayinda ta dago hannu zata kwasa mata mari but instantly went against it.

Ayra wadda ta zabura jikinta ya fara rawa ta fashe da kuka.

Ita kanta Hanifa hankalinta ya tashi domin kuwa she has never shouted on the kids like this before balle har tayi yunqurin Marin su..

A guje Ayra ta ruga da gudu ta bar dinning din.

"Ayra... Ayra... Ayra come here.." Hanifa ta kira yarinyar amma inaaa, tuni ta fice.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now