Chapter Eighteen

956 144 51
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Abin mamaki tun daga wannan ranar Hanifa bata qara zuwa ofis ba.. abinda ya faru ya tsaya mata a rai wanda ya sanya ko kadan bata so ta hadu da Sadiq, gani take yi kamar idan suka hadu he will make fun of her with regards.. abinda bata sani ba kuwa shine tun ranar da abun ya faru ya manta tunda dai ko kadan baya sa al'amuran Hanifa a kan shi..

Dayake dai Sadiq yana ta shirin barin kamfanin he didn't even care ko Hanifa ta zo ko bata zo ba.. kai a dalilin how very much busy he has become bai ma san cewar Hanifa bata zuwa aiki ba...

Dawowan Paapa daga South Africa ne ya kula bata zuwa and da yayi mata magana sai ta ce mishi tana mura ne kuma ta saukar mata da zazzabi.. Da wannan ne Paapa yasa ta rubuta request na sick-leave ta aika office din...

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

One week later!!

A yau ne Sadiq yayi sallama da Bugaje Industries.. Sendforth lafiyayye aka yi organizing mishi..

Gaba daya ma'aikatan kamfanin were sad a dalilin zai tafi.. A lokacin da yayi farewell speech dinshi kuwa yawancin su sai da suka yi hawaye.. sun saba da shi sossai, Babu qarya Sadiq yayi impacting positively a rayukan ma'aikatan kamfanin.. Yayi upgrading dinsu, a dalilin shi dayawa ma'aikatan kamfanin sunyi discovering potentials dinsu, he was able to bring out the best in alot of them, a bangaren kyautatawa kuwa babu abinda zasu ce sai Allah ya saka mishi da gidan aljannah..

Suzan tayi ta kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.. Sossai take jin dadin aiki da Sadiq, haka shima a bangaren shi ya ji dadin aiki da ita.. Musamman ya ja ta gefe ya dinga lallashinta yayinda ya sanar da ita cewar zata yi aiki qarqashin Hafeez wanda shi zai yi taking over from him sannan ya jaddada mata cewar zata ji dadin yin aiki da shi tunda sun saba.. tabbas ta dan ji sanyi don kuwa ta sani cewar Hafeez baya da matsala. Haka ta dinga yi ma Sadiq godiya tare da yi mishi fatan alkhairi.

Paapa ne ya rufe taron inda ya miqa saqon godiya on behalf of himself and the entire staff of the company zuwa ga Sadiq.. Yayi mishi addu'a sossai tare da yi mishi fatan alkhairi. A qarshe kuwa haka staff din suka dinga presenting ma Sadiq gifts kala-kala yayinda ya cika da mamaki.. Yayi musu godiya sossai na irin karramawar da suka yi mishi.. there is no doubt Bugaje Industries and its entire staff means alot to him..

Ko da zai tafi ya rabu da su Paapa akan zai zo gida da daddare don su qara yin sallama..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA

Wuraren qarfe takwas na dare suna zaune a dinning suna dinner- Sadiq, Paapa, Mamy da Hafeez

"I swear bro ji nake yi kamar in riqe qafafuwan ka don kar ka tafi" Hafeez ya fada yayinda su Paapa suke dariya.

Shima Sadiq wanda yake dariya yace "bro kar ka damu, ai muna tare kuma tafiya na shi zai sa ka gane how very good you are.. trust me"

"Still, you will be missed"

Mamy ce tace "gaskiya zamuyi kewar ka sossai Sadiq.. Allah dai ya saka maka da alkhairi yayi maka albarka sannan ya tsare ka daga sharrin masu sharri"

Gaba daya suka ce 'ameen'

Paapa ne yace "ka yi sallama da Baby kuwa??"

"No sir, dama I wanted to see her saboda I don't think zan samu zuwa tare da Uncles dina next week cos akwai tafiyar da zanyi..."

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now