Chapter Thirty-Four

1.3K 165 124
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA

Zaune suke a falon Paapa... Hanifa maqale da shi yayinda Mamy take zaune a gefe.

A yau ne Paapa ya dawo daga tafiyar da yayi.. Sossai yayi murnar ganin 'yar shi Hanifa, Haka itama tayi murnar ganin shi.. Sallah kawai yayi ya ci abinci shine suka zauna a falon yayinda Hanifa ta fara yi mishi tambayoyin da ta zo mishi da su.

Actually she just wanted to hear from him why exactly he got her married to Sadiq... She didn't plan to tell him irin zaman da take yi da Sadiq da kuma yadda Naana ta tilasta mishi zama da ita.. Ta sani cewar idan har Paapa ya gano cewar Sadiq yana zaune tare da ita against his wish zai iya interfering and she might be at the losing end.

"......na aura miki Sadiq don ya hora ki sannan ya dawo mun da ke.. The truth is Baby I didn't know what to do with you.. A dalilin rasuwar mahaifiyar ki tun kina jaririya ya sa nake tausayin ki, shi ya sa muka dauki soyayyar duniyan nan muka dora akan ki which I guess is what you took advantage of.. kina wulaqanta mutane sannan ga rashin ganin girman su. Na kasa hora ki da kai na because I have a soft spot for you. Ganin Sadiq ne kadai yake taka miki birki a dukkanin abubuwan da kike yi kuma na kula shi kadai kike shakka shiyasa na hada ku.."

Hannun Hanifa ya kamo sannan ya cigaba da fadin "Mun yi da Sadiq idan har kika gyara hali zai sallameki ki dawo gida wanda deep down within me I didn't want that to happen.. Na so ku fahimci juna auren ku ya zauna har abada domin kuwa Sadiq is the best husband that you can ever get a rayuwarki.. he is like a son to me kuma na tabbatar ko bayan rai na zai riqe ki cikin amana.. I am sorry I..."

"thank you Paapa" ta fada tana murmishi.

Cike da mamaki Paapa ya kalli Hanifa sannan ya kalli Mamy wadda take murmushi yace "ban gane thank you ba, aren't you angry"

"Not at all Paapa, kawai fa na tambaye ka ne just to clarify everything.. if i had known this before now, I would've been angry for sure but yanzu I feel grateful for what you did.. the truth is I have fallen in love with him kuma insha Allah bazamu rabu ba.."

"What??" Paapa ya tambaya cike da mamaki yet again.

Mamy wadda take murmushi tace "Oya go on and tell him the biggest suprise.."

Hanifa wadda take murmushi tace "albishirinka Paapa"

"Goro" ya fada cike da qaguwa na son jin abinda zata ce

"Fari ko baqi??"

"Baby please... just tell me"

"No Paapa.. me zaka bani idan nayi maka albishir din"

"Duk abinda kike so a rayuwar ki.."

"Ka kusa zama grand-Paapa..."

"What??? dagaske Baby??" ya fada yayinda ya zaro idanuwa yana kallon Hanifa

"Yes Paapa, I am pregnant"

"Masha Allah Baby, Alhamdulillah My Baby zata haifo mun Grand child. I am so happy to hear this news... come here"

Ya janyo ta ya rungume ta sannan ya cigaba da fadin "Allah nagode maka zan ga jika na kafin in mutu.."

Hanifa wadda take murmushi sai gani nayi tayi breaking hug din da sauri sannan tace "No Paapa please ka daina maganar mutuwa.. kana nan tare da mu. Sai na haifo maka jikoki guda ashirin"

"what?? ashirin Baby???" ya fada yayinda yake dariya.

Mamy ma dariya take yi yayinda tace "Lallai kam.. ashe Hanifa kina son yara haka??"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now