Chapter Fourty

1.9K 176 203
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

10 days later

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE ASOKORO

A yau wuraren qarfe takwas da kwata tana kwance cikin Duvet a kan gadon dakin shi yayinda take kallon shi..

Tsaye yake a tsakar dakin yana magana da Faisal a waya.

Yana daure da farin towel a qugun shi yayinda ta sa ma six-pack abs dinshi idanuwa..

Physique din Sadiq is surely a sight to behold.. ko alama bata gajiya da kallon shi!

A kullum qara gode ma Allah take yi da ya bata shi a matsayin miji... She just likes everything about him- his name, his personality, his attitude, his physique, his everything!!

"Kar ka damu zan zo, Ba dai 9:00am ba??"

Shiru yayi yana shafa gashin kanshi sannan yace "Ya zanyi da ku tunda dan 3 days leave din bazaku bar ni inyi ba"

Yana murmushi yace "Okay toh shikenan.. sai na zo"

Bayan ya kashe wayar ne Hanifa ta yaye Duvet din da ta rufa da shi sannan ta sauka daga kan gadon tayi 'yar miqa wadda ta sa ta banqaro qirjinta..

Sadiq wanda yake kallonta gaba daya ya kasa dauke idanuwan shi daga kanta.. she looked so beautiful and sexy in the Maroon silk nightie din da ke jikinta. Ji yake yi kamar ya manna ta a jikinshi yayi ta kissing din every part of her body amma kuma kash... babu hali!

It's been just 10 days da aka sallame ta daga asibiti.. ten days din da tayi a gidan Naana wanda finally sai jiya ta dawo gida and here just kwana daya yana ji kamar ya watsar da shawarar Nabeeha.. toh wai ya zai yi ne??

Sadiq wanda yayi nisa a tunani bai san lokacin da Hanifa ta qaraso wurin shi ba..

Hannuwanta masu laushin gaske ya ji suna shafa six -pack abs dinshi yayinda ya lumshe idanuwa.. why is she doing this to him?? tabbas he is in trouble!

Hanifa wadda ta kula gaba daya ya kasa motsi ce tace "Baby I love this"

Sadiq dai ko magana ya kasa yi.. he kept wondering how he can survive this for the next fifty days thereabouts.. like is it possible??

Hugging dinshi tayi briefly sannan tace "Bari in je in hada maka breakfast kafin ka gama shiryawa"

Hannuwan ta ya kamo ya riqe sannan yace "please don't.. koma ki kwanta abinki, I will manage" Ya miqa mata wayar shi yace "ke kuma kiyi placing order a kawo miki"

Ta bude baki zata yi magana ne ya sa hannu ya toshe bakin yayinda yace "don't argue with me and do as I say"

Daga nan ya janyota ya mayar da ita ta kwanta kan gadon ya rufe ta da Duvet.

Har ya juya zai shiga dressing room ne ya ji ta kamo hannun shi..

"what now Hanifa?"

"please ka dawo da wuri.. kar ka manta zamu raka su Naana Airport"

"ban manta ba, zan dawo da wuri"

Asali dai ranar da aka sallame ta Naana ta tafi da ita gidanta.. a cewarta tana buqatar kula sossai musamman saboda jikinta da babu qwari.. Hanifa dai bata so hakan ba but Sadiq found it to be a great idea saboda yadda take maqale mishi tun a asibiti ya tabbatar da tare suka yi kwana goman nan da sunyi aika-aika.

A cikin kwanaki goman nan kuwa duk safiya kafin ya tafi ofis sai ya je gidan ya ganta, mostly ma lokacin da yake zuwa tana bacci.. Haka yake zama ya sa ta a gaba yayi ta kallonta yana admiring beauty dinta.. daga nan kuma ya shafa kanta yayi mata kiss a goshi sannan ya tafi. Qamshin turaren shi ke sanar da ita cewar ya zo wanda idan sunyi waya sai tayi ta yi mishi masifa akan meyasa baya tashinta daga bacci idan ya zo.. As usual dai haquri yake bata tare da lallashinta akan he will next time but he never did.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now