Chapter Twenty-Six

1.1K 151 132
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

Wuraren qarfe takwas da rabi ne suka shigo gidan.

Shi dai Sadiq dawowan shi kenan tun safe.. Ya tsaya yayi sallan Isha'i a masallaci inda suka hadu da 'yan uwan nashi shine suka qaraso gidan tare.

Faisal ne na ji yana fadin "aikuwa sweetheart ta gayyace ni dinner na bata haquri akan zan zo cin girkin amaryar mu"

Sadiq wanda yake murmushi yace "ai da ka sani ka je ka ci nata don kuwa ba lallai ka samu yadda kake so ba anan din"

Yazeed cike da mamaki ne yace "wai kai this one that you keep insisting cewar bata iya girki ba toh wai ya kake yi?? na dai san babu Chefs a gidan and again kai ma baka iya ba.. toh me kuke ci?"

Sadiq yana dariya yace "you will find out yanzu"

Yazeed yace "Okay ooo"

Straight sashen shi suka nufa inda suka zazzauna a babban falon shi..

Faisal ne yace "I swear I love this house.. Kayi mana wayau wallahi"

Sadiq wanda yake murmushi yace "nayi muku wayau ko kun yi mun wayau?? ku da kuka gina manyan gidaje gari guda"

"Kai kuma da ka gina mai underground fa?? I swear gidan ka ya fi kyau" Yazeed ya fada yana hararar shi.

Sadiq yana dariya yace "Toh bro nagode.. Ni bari in je inyi wanka in zo"

"Toh sarkin tsabta.." Faisal ya fada yayinda ya dauki remote ya kunna TV.

Yazeed ne ya fashe da dariya yayinda Sadiq ya girgiza kai ya wuce dakin shi.

***********************

Sadiq ne ya fito sanye cikin qananan kaya na wandon jogger da Polo T-shirt. Yayi kyau sossai as usual. Gashin kanshi da na fuskar shi sai qyalli suke yi yayinda yake ta baza qamshi.

Faisal wanda ya kalle shi ne yace "angon Hanifa har ka fito?? ka ga yadda kayi kyau kuwa?? I swear Hanifa ta tabbatar ta riqe ka da kyau kar 'yan mata suyi mata barna"

Sadiq ya harare shi yace "kai kam baka rabuwa da tsokana, I wonder how my sister cope with you"

Yazeed wanda yake dariya yace "but seriously mutumina kayi kyau, wai fa a haka honeymoon in Nigeria kenan.. if it were to be a turai sai ya kenan?"

"I still can't believe kun qi zuwa Honeymoon qasar waje.. Yes mun sani cewar kace ba love marriage bane amma kuma ai from your little display a gidan Naana the other day we all know cewar both of you are romantically involved.. please take her out of the country ta dan huta mana.." Faisal ya fada

Sadiq wanda ya dan bata rai ne yace "Guys please ku bar maganan nan mu je kuyi dinner"

"Ban gane muyi dinner ba.. banda kai??" Yazeed wanda ya miqe ya tambaya.

Faisal ma wanda ya miqe tsaye yace "baiwar Allah Hanifa, zata sha wahala kafin ta gyara mana kai I swear, mutum ga ka kamar wayayye sannan haifaffen qasar America amma kuma baqauye.. like does it even make sense??"

Yazeed ne ya fashe da dariya yayinda Sadiq ya qara bata rai.

*******************

Sadiq ne ya shigo dinning room din with his cousins trailing behind him..

Gani nayi fuskar shi tayi displaying tsananin mamaki yayinda ya dan yi pause..

Hanifa ce sanye cikin dogon hijabi har qasa mai hannu yayinda take qoqarin arranging warmers din da suke kan table din. Tayi masifar kyau kamar wata balarabiya..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now