Chapter Twenty-Three

1K 137 97
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

Tsaye yake a kan treadmill machine na danqararren Gym din gidan yayinda yake working out..

Its exactly 9:35am...

Sadiq dai tun da asuba bayan da ya dawo daga masallaci ya koma dakin shi ya cigaba da Azkar har qarfe 7:30am na safe...

Normally idan week days ne, the next thing he does is shirin zuwa ofis toh amma today being Sunday sai ya wuce Gym don ya motsa jiki..

Yanzu haka yana daf da gamawa ne wayar shi ta fara ringing..

Gani nayi ya tsayar da machine din sannan ya sauka ya nufi wurin da wayar take...

Mai karatu I had to lower my gaze a dalilin well built body din Sadiq da na hango. His six pack abs, so on point which I am sure yana ji da shi..

Gaba daya jikinshi zufa ne.. Gashin kanshi ma ya kwanta a dalilin zufa.. da alama dai yayi working out sossai..

"Assalamu alaikum Naana ina kwana" ya fada da yayi answering call din.

"Lafiya lau Abba... Ya gida ya amaryarka???"

"She is fine"

"Madallah.. Dama na kira ne in ji lafiyar ku, please ka gaida mun ita"

"Zata ji insha Allah"

"amma dai yakamata ka kai ta gidajen uncles dinka su gaisa.. ko ya ka gani?"

"Yes Naana, I think anjima da yamma zamu je and daga nan ma zamu zo mu gaishe ki"

"toh madallah, Allah yayi albarka"

"Ameen My Naana.. Mini fa???"

"tana sashen ta.. I am sure she is still sleeping"

"okay toh I will call her later"

Bayan sunyi sallama ne na ga ya janyo singlet dinshi ya sa sannan ya kwashe wayoyin shi ya fito ya wuce sashen shi.

*********************

Bayan Sadiq yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya ne ya fito ya nufi sashenta.

Yana shiga dakinta ya ga ko ina tsab-tsab amma kuma bai gan ta ba.. A tunanin shi tana bathroom don haka ne ya leqa closet dinta don ya tabbatar da ta gyara shi tsab..

Aikuwa yana shiga na ga ya tsaya cak yayinda fuskar shi tayi displaying mamaki..

Hanifa ce kwance a qasan closet din tana bacci. Gashinta da ta daure a tsakiyar kai duk yayi buzu-buzu yayinda gajerar nighty dinta duk ta tattare ta bayyana fararen cinyoyinta..

A gefenta kuwa qaton trolley guda daya mai dauke da inner wears dinta kawai ya gani wanda yake a bude.. Da alama dai ta gama jera dukkanin sauran kayanta, Na inner wears din ne suka gagare ta wanda da alama bacci ne ya sace ta...

Tambayar da nayi itace shin tayi sallar asuba kuwa???

Sadiq wanda yake tsaye gani nayi ya juya zai bar closet din a dalilin yanayin yadda ya ga Hanifa.. he just doesn't like seeing her dressed like that..

Har ya fita sai kuma ya dawo.. Da qafar shi na ga ya taba ta alamar yana tashinta daga baccin..

Aikuwa a firgice ta farka ta tashi zaune tana salati.. Daga kai tayi tana kallonshi yayinda take qoqarin gyara gashin kanta.. Fuskarta duk ta kumbura, da ganin ta ma zaka gane lallai baccin bai ishe ta ba..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now