Chapter Thirty-Eight

1.6K 175 211
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

3 Days Later

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

Zaune suke a dinning room yayinda na ga plates na wani lafiyayyen Chicken and Cheese salad neatly served a gaban su.

Ko da na kalli fuskar Hanifa gani nayi ta sa ma Sadiq idanuwa as she looked very worried.

Sadiq dai tunda ta ajiye mishi plate dinshi babu abinda ya ci.. sai jujuya fork din hannun shi yake yi.

A yau dai kwanan su uku da dawowa daga Dubai. A ranar da Asma'u ta ba Hanifa labarin relationship din da yake tsakanin Hanan da Sadiq sossai ta damu don kuwa har suka dawo Nigeria she was worried.. she had to calm herself and look at the positive things that are happening between them recently and she assured herself akan lallai burinta yana iya cika matuqar ta cigaba da pushing don haka ne ta saki ranta tayi doubling effort dinta wurin neman soyayyar shi.

Tunda suka dawo ta kula Sadiq yana nuna damuwa sossai akan al'amuran ta.. Again, ga wata kulawa ta musamman da yake bata.

Da safe tare suke zama suyi breakfast wanda har hira suke yi. Dukda dai Hanifa does more of the talking while he does more of the listening! the only time da yake magana shine idan ta tambaye shi sai kuma idan ta fadi abin dariya ya fashe da dariya.. Hakan na yi ma Hanifa dadi don ko babu komai ta ga change.

Da rana kuwa tana shirya lafiyayyen lunch ta aika mishi accompanied with a white Rose and a card message mai dauke da kalaman soyayya masu dadi.

Sadiq yana enjoying kalolin girkin da Hanifa take yi mishi, haka yana son white roses din da take aiko mishi... Card messages dinta kuwa zama yake yayi ta karantawa over and over again kamar wanda yake neman wani abu a cikin kalaman nata amma bai gani ba.. he keeps getting confused about what he feels for Hanifa.. abinda ya sani dai shine yana enjoying company dinta sossai.

Sadiq yana kiran Hanifa a waya sau uku idan yana office. Yana kiran ta don ya ji lafiyarta da na cikin ta wanda hakan yana masifar yi mata dadi.. this alone shows cewar ya damu da ita!

Da dare kuwa idan ya dawo lafiyayyen dinner dinshi is waiting.. haka zasu zauna su ci suna hira wanda as usual yake yabawa and after then kowa ya nufi sashen shi sai da safe.

Hanifa would love to spend more time with him amma kuma ta haqura ta bi komai ahankali.. afterall it's just 3 days da dawowar su daga Dubai don haka tana hoping things would get better.

Hannun shi ta taba tace "Baby what's wrong with you?? meyasa baka cin abincin?? ko baka so ne? in dafa maka wani??"

Sadiq dai tun yana jin haushi idan ta kira shi 'Baby' har ya daina.. infact yanzu ya ma saba and he is beginning to even like the name.

"No Hanifa.. it's not the food, kawai na gaji ne"

"kayi aiki dayawa kenan yau Baby, don Allah ka daina stressing kanka" ta fada cike da damuwa yayinda ta ja kujerar ta kusa da shi ta karbi fork din hannun shi tace "Yakamata ka ci ko kadan ne.. it wont be good for you to sleep on an empty stomach.. let me help you"

Ko kafin Sadiq yayi magana har ta kai salad din saitin bakin shi tace "open your mouth" kamar dai yadda ake yi ma qananan yara idan ana so su ci abinci.

Ba tare da ya bude baki ba na ga ya sa mata idanuwa yana mamaki.. what's she trying to do??? feed him??? since when???

"Baby open your mouth ko in dura maka by force"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now