Chapter Seven

1K 161 75
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO CENTRAL

Cikin satin nan Hanifa ta koma aiki a kamfanin mahaifin nata yayinda Hafeez shima ya fara aiki a kamfanin.

Both Hafeez da Hanifa suna aiki tare da Sadiq ne. Kamar yadda office din Hanifa yake kusa da na Sadiq haka shima ofis din Hafeez yana kusa da nasu.

Asali dai tunda Hanifa ta dawo ko sau daya Sadiq bai nemi tayi mishi wani aiki ba.. haka itama bata nemi ya koya mata wani abu ba.. Gashi dama tun ranar da yayi mata fada take ji kamar ta shaqe shi ya mutu ta huta.

Tun da ta dawo tayi dedicating time dinta trying to find out information about him wanda har yanzu babu sa'a.

Hatta HR ta je neman personal info dinshi amma bata samu ba a dalilin komai yana computer din Musbahu (head HR) and she couldn't get access for now.

Shi kuwa Hafeez tunda ya fara aiki a kamfanin, a ofis din Sadiq yake yini suna aiki tare..

Hafeez dai sossai ya mayar da hankali akan aikin dayake yana da qwalwa tuni yayi picking....

Ya rage ma Sadiq aiki sossai.. A da sai Sadiq ya yini yana aiki, baya samun time din hutawa balle ya dan rage aikin project na Online course dinshi da yake yi amma yanzu he gets enough time to even handle stuffs outside of the company...

☆☆☆☆☆☆☆

A yau Thursday Zaune suke a lounge na ofis din Sadiq wuraren qarfe biyu na rana.. basu dade da dawowa daga Sallar Azahar ba- Sadiq, Hafeez, Yahaya da Musbahu yayinda suke tattaunawa akan Bonus da compensation da za'a biya month-end da kuma production expenses da za'a yi next month (more like a budget)

Paapa ne ya qwanqwaso qofar ya shigo. Cike da girmamawa duk suka miqe yayinda yace "please sit"

Gaba dayan su suka zauna.

"where is Hanifa??" yayi tambaya

"tana ofis dinta" Hafeez ya fada kai tsaye

"Why is she not part of the meeting?"

Gaba dayan su dai shiru sukayi.. he expected that anyway.

"Hafeez je ka kira ta"

"toh Paapa" ya fada yayinda ya miqe da sauri ya fita.

Gani nayi Paapa ya samu kujera ya zauna..

After 2 minutes ne Hafeez ya shigo cikin sallama with Hanifa trailing behind him.

Tun kafin ta daidaita tsayuwarta ta ji Paapan nata yace "Baby meyasa kika zauna a ofis dinki bayan ana meeting anan? are you not a part of the meeting?? aren't you aware??"

Hanifa wadda tayi mamakin tone din Paapa da yadda ya daure fuska yana mata magana ne ta bi ta rude.. tabbas idan tace bata sani ba qarya take yi domin kuwa duk wani meeting din da ake yi ana notifying ta Google calendar and anyi this time don haka she cant lie cewar bata gani ba..

Gani nayi ta daga kai ta kalli Sadiq wanda yake duba wani file da yake hannun shi yayinda ta kalli su Musbahu wadanda duk ita suke kallo.

"uhm Paapa dama yanzu zan shigo.. I was tidying up some things ne"

Paapa ya miqe tsaye yace "daga yau idan har ana meeting kuma an gayyace ki duk abinda kike yi ki bar shi kiyi attending meeting.. now join them"

"okay Paapa" ta fada a sanyaye yayinda ta nufi kujera da take nesa da ta Sadiq ta zauna.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now