Chapter Thirteen

904 151 51
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BRISTOL PALACE HOTEL
NASSARAWA- GRA

Wuraren qarfe Goma sha daya da rabi na safiyar yau yana zaune a kan kujerar lounge na suite dinshi riqe da iPad dinshi..

Yanzu haka tun da sassafe yake ta trying Hanan bai samu ba.. abin mamaki ita ma bata kira shi ba.

A jiya dai dukda sun rabu like there is no tension tabbas yayi sensing otherwise.. tun safe yake so ya fita yayi wasu 'yan shopping amma ya kasa.. Sossai ya shiga damuwa saboda he didn't hear from her this morning. Ya tabbatar maganar auren shi ne yayi hitting dinta hard toh amma his problem is why won't she just accept his proposal a wuce wurin??

I wonder ooo!!

Incoming call ne ya shigo iPad din nashi wanda yake hoping Hanan din ce amma inaaa..

Naana ce.

Yana answering na ga fuskar wata kyakyawar dattijiya ta bayyana a screen din.

Da ganin wannan dattijiyar dai tana hutawa domin kuwa yanayin jikinta ya nuna hakan.

"Angon Hanifa.." ta fada tana murmushi yayinda ya turo baki tace "Naana please stop.."

"ban gane stop ba.. ba ango bane kai ko me??"

"Kawai ban saba da title din bane Naana, kuma ma ai ban zama ba tukun.."

"Zaka saba kuma zaka zama insha Allah Abba.. ai wallahi na ji dadi sossai. tun jiya da daddare da ka fadi mun wannan zancen nake cikin farin ciki.. har salloli nayi cikin dare na gode ma Allah tare da yi muku addu'ar samun zuri'a na gari. Ai kam tunda kace 'yar gidan Alhaji Aliyu Bugaje na tabbatar 'yar mutunci ce.."

Sadiq wanda yake kallonta murmushi kawai na ga yayi ba tare da yace komai ba.. A ranshi kuwa fadi yake yi if only she knows who Hanifa is.

"Ka sanar ma su kawun naka ko??"

"Yes Naana, na sanar musu"

"madallah, yanzu zuwa yaushe suka ce za'a sa bikin??"

"Sai kun dawo Naana, for now dai idan Uncle Nazif ya samu lokaci ya zo Nigeria sai su hadu da Big Daddy da su Yazeed sai su zo neman auren"

"aikuwa hakan yayi daidai.. Allah ya sanya alkhairi. Na dai san amaryar ita zata hada kayan lefen ta da kanta ai ko?? tunda na ga haka ake yi yanzu"

Murmushi yayi yace "Naana duk yadda kuka ga ya dace haka za'a yi"

"ai dacewa kenan.. I am sure amaryar taka zata buqaci hakan. Idan mun dawo sai mu fara shirye shiryen shagalin biki"

"No Naana, daga daurin aure shikenan. You know I don't like those things"

"toh Abba, duk yadda kake so haka za'ayi. Ai dole in lallaba ka kar kace ka fasa"

Fashewa yayi da dariya yace "ai bazan taba fasawa ba Naana... wannan auren da yardan Allah sai nayi shi"

"Ikon Allah, lallai kana son yarinyar nan.. shine nake kiran ka ango kana wani noqewa"

Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.

"Ni da nake nan ina sa ran na gida za'ayi tsakanin ka da Hanan ashe ba haka bane"

Yana murmushi yace "Naana ai Hanan ta dage akan bazata aure ni ba"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now