Chapter Fifteen

1K 146 89
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

NAZIF ABU-DAWOOD RESIDENCE
SHEIKH ZAYED CITY- CAIRO EGYPT

Zaune take a kan gadon dakin ta yayinda ta jingina da headboard na gadon tana kallon shi.

Sadiq wanda yake zaune daf da ita yana riqe da bowl na Corn flakes a hannun shi da spoon yayinda shima yake kallonta.

Sadiq dai a jiya ya shiga jirgi zuwa Abuja.. wuraren qarfe shidda na safiyar yau din ne jirgin su ya tashi daga Abuja zuwa Cairo. dayake tafiyar awa hudu ce kacal, qarfe Goma sha daya saura ya shigo gidan su Hanan. A lokacin da ya iso Abbu baya nan, Umma dai bata yi mamakin ganin shi ba domin kuwa ko a jiya da suka yi waya ta sani sarai dukda tayi calming dinshi down ba zai taba haquri ba sai ya zo da kanshi. Sadiq ya tarar Umma tana ta masifa na yadda Hanan din ta qi cin abinci wanda daga nan ne ya lallaba Umma yayi taking charge yayinda tayi tafiyarta ta bar su...

"Please my sweet Hanan try and eat something... you know you slept on an empty stomach last night gashi yanzu ance any moment the doctor will come check on you.. if he finds out cewar baki ci komai ba allura zai yi miki kuma we both know how it will end.."

turo baki ta dan yi sannan tace "toh na ji.. I will eat small"

Murmushi yayi sannan ya kai cokalin bakin ta yayinda ta bude ya sa mata.

"haka kawai kiyi ta sa ni ina surutu.. I swear you are the only one that makes me talk like a parrot"

Murmushi ta dan yi sannan tace "I am sorry Chocopie.."

Haka dai Sadiq ya dinga bata Cirn flakes din a baki.. Idanuwa ta zuba mishi kamar kullum, Allah ya sani tana bala'in son Sadiq.. On top of everything kuma ga kyan shi da yake kashe ta.

Hanan dai tayi nisa a kallon Sadiq da bata ma san ta shanye Corn flakes din ba.

Shi kam da ya kula kamar bata san ta shanye din ba sai kawai ya dago empty spoon ya kai bakinta, ko da cokalin ya shiga bakinta sai ta ji wayam. Da sauri ta kalli cokalin sannan ta kalle shi ta ga ya fashe da dariya.

Turo baki tayi tana hararar shi tace "wulaqanta ni zaka yi???"

"No my sweet Hanan.. na ga kamar baki qoshi ba, ko zaki qara ne??" ya fada tare da kashe mata ido daya.

Murmushi tayi sannan tace "thank you for making me eat Chocopie"

"No thank my face instead.."

"what??"

"you were staring at my face all through, I caught you"

Murmushi tayi tace "toh ai kai ne kayi kyau dayawa Chocopie"

"huh.. not again" ya fada tare da ajiye bowl din a gefe ya gyara zama a kan gadon nata yace "tell me something"

"what"

"me ya faru?? why are you sick?? kar kiyi mun qarya"

Zuciyarta ce ta buga yayinda ta sa mishi idanuwa ba tare da ta san me zata ce mishi ba.

Me zata ce mishi toh?? cewar tana son shi?? cewa kar ya auri Hanifa ya aureta?? Soyayyar da take nema fa??

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now