Chapter Twenty-Two

983 141 95
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

Wuraren qarfe takwas da kwata na dare ya shigo gidan.. Kai tsaye sashen shi ya wuce yayi shirin wanka..

Sadiq dai a yau family house dinsu yayi lunch.. Naana ta dinga yi mishi qorafi akan ya hana a kai ma matar shi abinci sannan shi ya zauna ya ci nata.. Shi kam haquri ya bata tare da fadin tunda kadan ya ci wurinta idan ya koma gida zai ci na Hanifa. Da wannan ne ta haqura ta qyale shi..

Suna Lunch din ne Asma'u ta dawo tare da Faisal.. Aikuwa sossai tayi murnar ganin yayan nata.. Hana shi tafiya tayi har sai bayan Asr sannan suka tafi shi da Faisal..

Ko da suka bar gidan su Sadiq kuwa Faisal ya ja shi Golf Court din Dad a dalilin za'ayi wasa a yau din.. dayake Sadiq yana enjoying Sport din sai kawai ya bi shi suka je.. Daf da Magrib ne aka gama suka wuce masallaci.. basu bar masallacin ba sai da suka yi sallan Isha'I. Daga masallacin ne finally suka yi ma juna Sallama.

Sadiq dai bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin dogon wando da T-shirt ne na ga ya fita.

Kai tsaye dinning ya fara zuwa inda ya san zai gane idan Hanifa tayi abinda ya sa tayi ko bata yi ba..

Aikuwa yana shiga dinning din ya ga kayan breakfast din da tayi tun da safe..

Gani nayi ya girgiza kai yace "like seriously???"

Juyawa yayi ya fita yayinda na ga ya wuce sashen ta.

Hanifa ce zaune a kan Ottoman din gadon dakinta yayinda na ga ledojin Chocolates masu yawan gaske a gaban ta..

Asali dai da rana tayi ta jira ta ga Ammi ta aiko mata abinci amma ta ji shiru, ta shiga kicin din tayi ta zagaye amma ta kasa dafa komai.. bata kuma dafa ba a dalilin bata iya ba! Fridge ta bude ta dauki fruits wanda da qyar tayi slicing dinsu ta ci.. Daga nan ne ta kwashi Chocolates dayawa da ta gani a cikin fridge din ta wuce da su sashenta..

A yanzu haka da dare yayi ta ji shiru babu Dinner shine ta sa Chocolates din a gabanta tana ta ci.. Kamar da safe dai dakin yana nan a hargitse, babu abinda ta gyara.

Muryar shi ta jiyo daga bakin qofa yana fadin "ina wasa da ke???"

Chocolate din da yake hannunta ta saki yayinda tayi saurin miqewa tsaye tana kallon shi..

Sanye take cikin wata Navy blue gajerar sleeveless rigar bacci wadda ta tsaya iya cinyarta.. Rigar dai dukda ba see through bace amma tayi revealing cleavage dinta. Ta hade gashin kanta a tsakiyar kai as usual yayinda take sanye cikin wani slippers mai laushin gaske.. Sossai tayi kyau!

Nan da nan tayi Composing kanta ta harare shi tare da fadin "me nayi???"

"ban sa ki aiki ba kafin in bar gidan nan da safe??"

"Ni fa na fadi maka bazan yi ba... Ko a gidan mu bana yin komai don haka baka isa ka sa inyi abinda ban yi niyya ba"

Gani nayi yayi murmushi sannan ya qarasa shigowa dakin yace "really??"

Hanifa wadda jikinta yake rawa shiru tayi ba tare da tace komai ba...

Bata ankara ba ta ji ya kamo hannunta wanda ta ji kamar yayi mata shocking.. his hands felt very soft kamar na jarirai.. it's actually the first time da Sadiq ya taba ta..!!

Kafin tayi processing abinda ke faruwa ta ji yace "it's time for you to see what will happen to you idan kika tsallake doka na a gidan nan"

Da qarfin tsiya ya ja ta suka fita daga dakin..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now