Chapter Twelve

978 147 77
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

Zaune yake a kan daya daga cikin kujerun lounge dinshi yayinda yake magana a waya.. Wayar ma ajiye ta yayi a kan centre table yayinda ya sanya ta a Speakerphone. Da ganin yanayin shi zaka gane yana cikin damuwa..

Hafeez wanda yake zaune a gefen shi har ya fi shi shiga damuwa. He is a living witness to what Sadiq has gone through in order to compile his project work, he knows the time, energy and sleepless nights he has spent just for this project, infact tun kafin shi da Hanifa su fara aiki a kamfanin nan yake yin project din and just like that Hanifa ta ruguza mishi komai..

"Sir please can I have a grace of one week to see what I can come up with?"

"I am so sorry i really can't help you Mr Bunza, you will have to make the submission before the end of today and do your presentation tomorrow"

Ajiyar zuciya Sadiq ya saki sannan yace "Okay Sir.. merci"

"de rien Bunza.."

Bayan Sadiq yayi sallama da Professor din ne ya koma ya kishingida..

Allah ya sani ran shi ya baci, bai taba yin course mai wahala da cin lokaci ba irin wannan... just when he thought ya gama finally Hanifa tayi mishi wannan lalatar... Yes he has the knowledge amma Certificate din fa???

"Gaskiya Hanifa bata kyauta ba.. instead of ma ta baka haquri sai ta zage ka?? ka tabbatar baka son Paapa ya ji wannan zancen??" Hafeez ya tambaye shi

"what's the point? please ba sai ya sani ba.. bawan Allah yana fama da jikin shi bai gama warwarewa ba all thanks to the stupid garl. kar ka damu.. haka Allah ya so. As for her, ba dai game take playing ba? trust me, she just took on the baddest game player"

Ghen ghen ghen!!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA- GRA

Wuraren qarfe shidda na yamma Sadiq ne zaune a falon Paapa.

Asali dai yana tashi daga ofis ya kira Paapa ya sanar da shi cewar yana so ya gan shi idan da hali shi kuma yace mishi he can come whenever he wants to.

"Ya office din?? hope komai lafiya??" Paapa ya tambaye shi.

"Alhamdulillah Sir, everything is in order"

"Madallah.. thank you very much Son.. Ka taimake ni sossai.. Ubangiji Allah yayi maka albarka"

Murmushi Sadiq yayi yace "Ameen"

"Zuwa Monday Insha Allah nima zanyi resuming.. if not for doctor's orders akan bed rest dinnan, I would have resumed already.. Zaman haka nan babu dadi wallahi"

"Kar ka damu Sir, komai yana tafiya smoothly.. besides, hutun yana da matuqar amfani a wurinka"

"Haka ne Son.. So tell me, to what do I owe this visit da har ka kasa isa gida ka huta??"

Ajiyar zuciya na ga Sadiq ya saki sannan yace "dama akan maganar da muka yi ne 3 days ago"

"Maganar Hanifa???" Paapa ya fada with so much hope wanda didn't go unnoticed by Sadiq.

"Yes Sir, Nayi tunani akai and I am willing to help you change her to a better person.. Zan aureta in tafi da ita kamar yadda ka buqata" Ya fada confusedly.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now