Chapter Thirty- Nine

1.5K 180 157
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ASOKORO DISTRICT HOSPITAL
ABUJA

Motar ambulance ce ta shigo asibitin da sauri yayinda aka fito da Hanifa akan stretcher akayi cikin asibitin da ita..

Sadiq wanda yake biye da su gaba daya a rude yake.

Asokoro district hospital ya kasance one of the best hospitals a garin Abuja, if not the best. It's the biggest Hospital in Abuja. Big Daddy made sure to get the best equipment and staff in the hospital. Everything from the exterior to interior of this hospital is world class.

Mai karatu idan ka ga dakunan cikin wannan asibitin zaka rantse ba asibiti bane.. everything is so beautiful, neat and perfectly comfortable for marassa lafiya.. Maganan warin asibiti kuwa babu shi kwata-kwata don kuwa lafiyayyen qamshi ne yake tashi ta kowanne bangare da lungu na asibitin.

Straight ER aka yi da ita.

Cikin qanqanin lokaci familyn su Sadiq sun hallara a asibitin banda Big Daddy wanda baya qasar..

A lokacin da suka iso kuwa sun tarar ana ta rikici da Sadiq wanda ya qi fita daga ER din ya ba Nabeeha da team dinta damar yin aikin su.. Yazeed tare da wasu doctors sunyi iyakar qoqarin su amma sam.. Sai da Dad (Faisal's father) yasa baki suka lallaba shi shine ya fito..

Ko da ya fito kuwa tsayawa yayi a bakin qofar dakin ya tsugunna ya dafe kai yana ta addu'a.. he looked super worried!

Naana da Asma'u basu taba ganin Sadiq a cikin mugun tashin hankali ba irin wannan.. Gaba daya ya hargitse. they themselves were so worried that they couldn't even console each other properly..

Asma'u ma kuka ta dinga rusawa yayinda Faisal yake lallashinta.

Nabeeha tayi iyakar qoqarinta don tayi saving Babyn Hanifa amma inaa.. she already lost it, she managed to stop the bleeding by performing a D&C procedure on her.. Wannan procedure din could get uncomfortable idan har mutum yana cikin hayyacin shi don haka ne ake yi ma mutum general anesthesia to put you to sleep amma in the case of Hanifa she wasn't even conscious don haka bata ma san abinda ke faruwa ba.

Nabeeha being a very good Gynecologist along with her team performed the procedure cikin qwarewa and it was successful.

Ko da Nabeeha ta sanar da su cikin Hanifa ya zube Sadiq bai damu ba kamar yadda ya damu da wellbeing dinta.. Lafiyarta is his top priority. Ya sani cewar idan wani abu ya same ta he will never forgive himself domin kuwa a dalilin shi ta shiga halin da take ciki.

Hanifa was expected to regain consciousness few hours after the procedure amma kuma she didn't.

Dukkan reports din Nabeeha sun nuna cewar babu wani matsala a procedure din da suka yi.. it has to be something else and so she stepped down and Yazeed was the one that took over from there..

Yazeed yayi duk abinda yakamata don Hanifa ta farfado amma inaa..

Result na tests din da yayi running akanta sun nuna cewar she is absolutely fine.. it looked as if ta shiga Coma amma kuma a very mild one for which there could be a chance tana jin abinda ke faruwa a kusa da ita but he is not sure..

But why isn't she waking up???

Yazeed yayi inviting both Heads of cardiology and neurology na asibitin don suyi running tests dinsu akanta just to make sure her heart and brain are working fine.

They had to wait for the results to come back washegari.

Gaba dayan su jikin su yayi sanyi as they were all worried about Hanifa.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now