Chapter Twenty

1.1K 146 101
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda na ga wasu DVD/CD plates baje a kan gadon tana ta sorting dinsu.. Ko da nayi zooming sai na ga duk plates din waqa ne da kuma na rawa both audio and Video.

She was taking her time to sort them sannan tana sakawa a cikin wata jaka.

Ni kuwa nace ina zata je da su??? ba dai gidan auren nata ba?? Hanifa is surely not serious!!

Wayarta ce tayi ringing yayinda na ga ta lalubo ta da sauri a dalilin ringtone din- Ringtone din Paapa..

Tana answering yace "Baby zo ki same ni a falo na yanzu"

Kai tsaye tace "toh Paapa"

*****************

Zaune yake a bisa one-seater kujera a falon Paapa yayinda suke ta hira kamar ba sirikai ba..

A yau Bayan an gama yinin biki dangin ango dai sun tafi akan washegari zasu dawo su dauki amaryar su..

A daren yau din ne Paapa ya gayyaci Sadiq a dalilin wata muhimmiyar magana da yake so yayi mishi.. well dama dai ko da Paapa bai yi inviting dinshi ba he'd still come don yayi mishi sallama.

A wannan lokacin su Mamy suna can suna hidima da baqin su dukda dai dangi ne..

Hanifa ce ta shigo falon yayinda ta tsaya cak a dalilin qamshin turaren shi da ta ji.. Zuciyarta ce take ta bugawa fiye da na kullum.. jikinta har rawa yake yi wanda ta rasa dalili.

Paapa wanda ya dago kai ya ganta ne yace "ya kika tsaya a nan?? shigo mana"

A sanyaye ta qarasa shigowa yayinda ta nufi wurin Paapa kai tsaye ba tare da ta kalli Sadiq ba.. Shi kam Sadiq tunda ya ji Paapa ya kira sunanta na ga ya fara latsa wayar shi.. Toh fa!

Sanye take cikin kayan bacci na T-shirt 'yar qarama daidai dan jikinta da wandon three quarter.. As usual ta daure gashinta a tsakiyar kai wanda yayi buzu-buzu amma kuma dukda hakan tayi kyau sossai..

Hanifa ta zauna kan kujerar da Paapa yake zaune ta maqale a jikin shi kamar mage tace "Gani Paapa"

"Baki iya gaisuwa bane Baby?? Baki ga mijin ki bane a zaune??"

Turo baki tayi and for the first time ta dago kai ta kalle shi.. Wani irin bugawa zuciyarta tayi a dalilin masifar kyau da Sadiq yayi mata..

Sanye yake cikin wani Yadi off white wanda aka yi ma dinkin half jumper... a yanzu haka fa ba wai ya dago kanshi bane, kawai side view dinshi take kallo amma she could swear bata taba ganin namiji mai kyan Sadiq ba a rayuwarta... toh amma kuma me?? ta tsane shi!!

Hararar shi tayi sannan tace "ban gan shi bane Paapa"

"tunda kin gan shi greet him then.."

"Ina wuni" ta fada in a low tone yadda ta san ba zai ji ba and to her greatest suprise sai ta ga ya dago kai ya kalle ta har yana murmushi yace "lafiya lau Mrs Bunza"

Ran Hanifa ne yayi mugun baci jin ya kirata da sunan da bata so.. Wata muguwar harara ta gabza mishi sannan tace "Ba nace ka daina kira na Mrs Bunza ba?" ta kalli Paapa cikin shagwaba tace "Paapa ka gaya mishi ya daina kirana da wannan sunan"

Shi kam Paapa a ranshi dadi ya ji a dalilin yadda Sadiq din yayi addressing dinta.. Allah ya sani da son ranshi auren nasu ya dore don kuwa yana bala'in son Sadiq toh amma from the looks of it all Hanifa bazata yi lasting a wurin shi ba... idan ma ta gyara hali ya gode ma Allah!!

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now