Chapter Thirty

1.4K 169 140
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

LATE ALHAJI ABUBAKAR MUHAMMAD BUNZA RESIDENCE -ASOKORO

Zaune take akan kujera yayinda take yi ma Asma'u wadda take zaune a qasa Oiling gashinta.

A yau dai kwana uku kenan Asma'u tana fama da Naana akan tayi mata oiling gashinta amma tana zamewa.. Ita dai Naana hankalinta ne yake mugun tashi a duk lokacin da Asma'u ta nemi tayi mata Oiling din, ba don komai ba sai don mugun cika da gashin nata yake da shi sannan kuma ga tsawo.. a galabaice take gama mata oiling din.

"Yarinya sai naci na bala'i, maimakon ki je salon suyi miki kin maqale mun zaki sa duk in gaji.." Naana ta fada cikin masifa.

Asma'u tana dariya tace "Yi haquri Naana.. wallahi bana jin zuwa Salon din ne.."

Door bell suka ji anyi ringing yayinda Zubaida ta fito da gudu ta je dubawa..

Naana da Asma'u ne suka ga Zubaida ta shigo tare da Hanifa tana biye da ita..

Cikin sallama Hanifa ta qaraso yayinda Naana ta amsa sallamar tace "Hanifa?? ashe kin dawo daga Kanon??"

Hanifa wadda ta zama suprised jin maganar Naana ce tace "Kano kuma Naana??" ta qaraso ta duqa har qasa tace "Ina wuni"

"Lafiya lau, tashi ki zauna"

Hanifa ta miqe ta zauna a kan kujera one seater. ita kuwa Asma'u ko kallonta bata yi ba balle ta gaishe ta.

"aikuwa Abba yace mun kin je Kano" daga nan ta bata labarin yadda suka yi da shi- lokacin da tayi ta mishi fada don bai je da Hanifa America ba.

Hanifa dai bata yi mamakin qaryar da ya shirga ma Naana ba domin kuwa dama there is no way in hell zai je da ita..

"toh meyasa yayi mun qarya??" Naana ta tambaya.

Ganin Hanifa tayi shiru tana ta wasa da yatsun hannuwanta ne ya sa Naana ta kalle ta da kyau tace "Hanifa me ke faruwa ne??? Ni na ga ma kamar kin rame.."

Asma'u ce ta dago kai ta kalli Hanifa.. Tabbas ta rame amma kuma ai duk abinda ya sameta ita ta janyo tunda rashin mutunci ta sa a gaba.. it means Yayan nata yana hora ta yadda yakamata kenan.

Naana cikin damuwa tace "kin yi rashin lafiya ne?? why didn't you call me tunda kina da lambar waya na???"

Hanifa wadda ta rasa me zata ce sai kawai ta fashe da kuka..

Aikuwa nan da nan Hankalin Naana ya tashi yayinda Asma'u tayi shiru tana kallonta.. kenan tayi hankali ta gaji da horon da yayanta yake yi mata ne ko me???

"Zo nan Hanifa... come to me" Naana ta fada yayinda Asma'u ta miqe tsaye ta bata wuri.

Hanifa ta taso ta dawo wurin Naana ta rungume ta yayinda ta cigaba da rusa kuka..

Zubaida ce ta shigo da abubuwan motsa baki dayawa a tray wanda tun kafin ta ajiye Naana tace "Zuba mun ruwa Zubaida"

Da sauri Zubaida ta ajiye tray din ta bude Goran swan ta zuba a glass cup ta miqa ma Naana sannan ta fita cike da damuwa na ganin halin da Hanifa take ciki..

Naana wadda take rungume da Hanifa ce tace "sha ruwa.." yayinda ta kai cup din saitin bakinta ta sha..

Asma'u ce ta karbi glass cup din daga hannun Naana sannan ta ajiye yayinda take tsaye tana kallon ikon Allah.. what a drama queen she thought!

"Stop crying and tell me, me ke faruwa?? kar ki ji tsoro ko tunanin wani abu, tell me everything that's going on"

Hanifa wadda ta daina kuka ce ta kalli Naana sannan ta kalli Asma'u..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now