Chapter Six

1K 174 70
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Days later

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA

A yau da daddare suna zaune a main dinning na gidan- Paapa, Mamy, Hafeez da Sadiq..

Tun bayan sallan Isha'i Sadiq ya zo gidan yayi dropping ma Paapa wani file a dalilin zai je Abuja washegari don haka bazai je ofis ba.

Paapa ne yayi insisting akan lallai ya zauna yayi dinner kafin ya tafi tunda dai ba mata gareshi ba balle ya sa ran idan ya koma gida zai tarar an dafa mishi abinci.

Da farko Sadiq ya dage akan bazai tsaya ba amma Paapa wasn't ready to accept No for an answer don haka ne ya haqura ya zauna.

Luckily enough dama Hafeez ya dawo tun shekaran jiya and they had the opportunity to meet for the first time.. Kun san halin maza babu ruwansu.. tuni sunyi blending da juna.

A yanzu haka idan ka kalle su yadda suke cin abinci suna ta hira zaka rantse dama sun san juna.. though they share some things in common- personality, Harvard University, MBA- probably shiyasa sukayi saurin fahimtar juna.

Paapa da Mamy sun ji dadi sossai yadda suke hira suna sharing experiences dinsu..

"Kana nufin Professor Wilson yana nan???" Sadiq ya tambaya cike da mamaki

"wallahi yana nan" Hafeez ya fada yana dariya.

"I swear mutuminnan yana son boko.. dukda ya tsufa bazai je ya huta ba? na tuno lokacin fa da qyar yake tafiya.. that was 6 years ago"

"aikuwa yana nan.. a hakan yake lectures"

"But he is very good.. gaskiya duk wadanda suka samu privilege na zama students dinshi should consider themselves lucky.. he is a great mentor"

"Oh yes i agree with you.. I think shiyasa ma Harvard suka riqe shi" Hafeez ya fada yana murmushi.

"So tell me, yanzu da ka gama meye plans dinka??" Sadiq ya tambaye shi.

"For now gaskiya nothing saboda ina so qwalwata ta huta..."

Tun kafin Hafeez ya qarasa magana ne Sadiq ya kalli Paapa yace "Sir, I disagree with this. ina ganin yakamata ya fara aiki a Bugaje Industries ASAP.. shine perfect mutumin da yakamata yayi replacing dina.."

ni kuwa nace what?? replacing kuma??

Paapa yace "ai dama wannan yana daga cikin burina.. Hafeez da Hanifa suyi aiki a kamfani na. But tunda ka kusa tafiya I think Hafeez should still join and idan ka gama coaching Yahaya shi kuma sai yayi coaching dinsu"

"Okay Sir"

Hafeez wanda yake sauraron su ne yace "ikon Allah... You people are deciding for me when I am seated right here.."

Paapa wanda yake murmushi yace "ai tun kana qarami na sani cewar duk decisions din da nayi taking akanka baka bijirewa and I am sure this won't be an exception.. one of the reasons why I so much like you Son. Burina dama shine da kai da Hanifa kuyi taking over idan kun gama karatu.. it's good kun dawo kafin Sadiq ya tafi atleast zaku koyi one or two things and afterwards Yahya zai qarasa muku so it's a yes from me" ya kalli Mamy yace "You?"

Murmushi tayi sannan tace "Yes from me too.. Allah ya saka da alkhairi"

"A big YES from me too.." Sadiq ya fada yana murmushi harda kashe ma Hafeez ido daya.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now