Chapter Twenty-One

1K 152 65
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

6 days later..

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE ASOKORO

A yau kwanan ta shidda a gidan Sadiq.. tun ranar da aka kawota bata gan shi ba..

Hanifa dai a ranar da aka kawota gidan bayan kowa ya tafi kawai hayewa gadonta tayi abinta tayi bacci..

Washegari ranar Lahadi ne ta samu damar zagaya gidan.. Sossai gidan Sadiq ya bata mamaki.. Bata taba ganin tsarin gida irin shi ba a rayuwarta. Gida kamar Zane.. like 70% na abubuwan da ta gani ma bata gane ko meye su ba.. Babu qarya an narka dukiya a cikin gidan! Aikuwa dai gidan Sadiq ya mayar da ita first class baqauya.. Duk da ta tsani mai gidan sossai gidan ya birge ta.. ji take dama ta kore shi ta cigaba da zama a gidan har abada amma kuma inaaa... hakan bazai yiwu ba.

A yanzu jira kawai take su hadu ta karta mishi rashin mutunci ya sallame ta.

A cikin kwanakin nan shidda kuwa a kullum sai Naana ta aiko mata da abinci breakfast, lunch da dinner.. Har lambar wayarta ta aiko aka bata da saqon cewar idan tana da matsala she shouldn't hesitate to call her!

Ita dai Hanifa tayi saving lambar amma kuma bata taba kiranta ba..

Ni kuwa nace aiki da rashin hankali wurin Hanifa.. ana aiko miki da abinci ai ko babu komai kya kira kiyi godiya!!

A kullum dai idan Zubaida (One of Naana's Maids) ta kawo mata abinci zata tarar da previous dishes (used ones) a bisa dinning.. haka zata kwashe su ta wanke a kicin sannan ta hada ta tafi da su.. Ko sau daya Hanifa bata taba wanke dishes din da ake kawo mata abinci a ciki ba..

Ta ya zata wanke tunda bata iya ba.. tabdijam!!

Hanifa dai dayake ba wani fitowa take yi ba she spent almost 90% na kwana shiddan nan a sashen ta.. Yawanci dai idan ta fito bai wuce ta ci abincin Naana ba ta koma abinta.

Bata ga Sadiq ba a tsawon kwanakin kuma she didn't care at all.. dukda ta qagara ta gan shi suyi rikici a part of her really wants to live longer in the beautiful mansion.

A yau Saturday bayan ta gama breakfast as usual ne ta wuce dakinta tayi wanka....

Ko da na kalli dakin Hanifa sai ganin shi nayi a hargitse.. dukkanin kayan da ta sanya a cikin kwanakin nan shidda suna nan a yashe a dakin.. Hatta qaton gadon dakin jibge yake da kaya, gefen da take bacci ne kawai babu komai..

Tsaye take a gaban Vanity mirror dinta sanye cikin wani black bum-short da wata doguwar rigar material mai black and white pattern with side slits wanda ya kai hips dinta har yana revealing bum-short din da ta sa.. Rigar material din dai see through ce don haka har black color bra din da ta sanya is visible... Babu abinda take yi sai baza qamshi..

Ita dai Hanifa dama can mayyar sa qananan kaya ce, su ma din marassa nauyi.

Dogon gashin kanta wanda yake ta qamshi take tajewa.. Mai karatu sossai Hanifa tayi kyau.. don kyau dai akwai shi, Halin ne kawai sai ahankali..

Ta gama daure gashinta a tsakiyar kai kenan na ga tayi freezing a dalilin qamshin turaren da ta ji- turaren SADIQ.

Da sauri ta juyo ta gan shi tsaye a bakin qofa with his hands folded around his chest.

Rabon da Hanifa ta sa Sadiq a ido tun ranar da Paapa ya gindaya mata sharadin nan a Kano.. Zuciyarta ce take ta bugawa a dalilin mugun kyau da kwarjinin da yayi mata kamar kullum..
Sanye yake cikin grey three-quarter sweatpant da black polo T-shirt, Gashin kan shi da na fuskar shi sun sha gyara sai qyalli suke yi..

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now