Chapter One

1.7K 196 64
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT-KANO STATE

Zaune yake a cikin motar shi qirar BMW M340 baqa wuluk sannan sabuwa gal wadda ya faka a parking lot na airport din.

Babu abinda yake tashi a cikin motar sai wani asirtaccen qamshin da humidifier take fesowa wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadin gaske.

Maganar gaskiya ita ce mamallakin motar nan ya kwana biyu yana hawan ta don haka ba wani abu ya janyo ake yi mata kallon sabunta ba, bala'in tsabta ne na mai ita. A yanzu haka da nake kallon interior na motar babu datti ko alama.. infact the car is spotlessly clean.

Magana yake yi a waya through CarPlay. It's exactly 10:30am.

"...Yes Sir yanzu na karbi saqon" ya fada cikin muryar shi mai dadin ji wadda ga dukkan alamu zata yi tsada domin kuwa yadda yayi maganar zaka tabbatar ba mai yawan yin magana bane.

On the other side of the call ne na ji yace "toh ko dai zaka tafi gida ne abinka tunda na ga yau Saturday kana buqatar hutu plus bazaka rasa one or two things da kake son yi ba.. in yaso sai driver ya je ya dauko ta"

"No sir, it wont be necessary ai. Tunda ina nan din I can wait. Ba kace flight din su zai sauka by 11:00am ba?"

"Yes Son, 11:00am tace"

"it's just a thirty minutes wait.. uhm, amma baka fadi mun sunan ta ba"

Dariya na ji mutumin yayi sannan yace "ban fadi maka ba ko kuma ka manta??"

"Sorry Sir na manta ne.. My bad"

"it's okay Son.. Hanifa Aliyu Bugaje, shine full name dinta. Nima insha Allah zan biyo flight na gobe in dawo.. I am practically done here kuma ma garin ya ishe ni"

murmushi yayi yace "amma Sir, Milan is a great City fa"

"Yes it is but there is no place like home Son"

"Yes I agree with you Sir.. Allah ya dawo da kai lafiya"

"Ameen"

Bayan sunyi sallama ne yayi disconnecting call din sannan na ga ya shiga Note din wayar shi yayi rubutu kamar haka:

Hanifa Aliyu Bugaje..

Ni kuwa nace like seriously?? kenan ya rubuta sunan don kar ya manta??? is the name that hard to recall??? babbar magana!!

Yana disconnecting call din karatun Al-qur'ani cikin muryar Abdurrahman Sudais ya cigaba automatically... da alama abinda yake ji kenan before the call.

Gani nayi ya kwantar da seat dinshi yayinda ya kishingida yana jiran 11:00am.

***********

Wuraren qarfe Goma sha daya ne da minti uku jirgin su ya sauka. Yana zaune a cikin motar shi ya ji saukowar jirgin amma bai fita ba domin kuwa ya san ko ya fita sai ya jira saboda formalities da ake yi kafin arrivals din su fara shigowa don haka he chose to sit in the car and wait a little more..

Exactly 11:20am ina tsaye na ga ya bude qofar motar ya fito..

"Hasbuballabu wa ni'mal wakeel" abinda na fada kenan.

Wani kyakyawan gaske na gani. Dogo ne ba mai jiki ba. shi ba fari ba sannan ba baqi ba amma da ka kalli fatar shi babu abinda kake gani sai tsabar hutu... irin hutun nan da ake haifan mutum da shi. Gashin kan shi da fuskar shi baqi wuluk sun sha gyara sai qyalli suke yi.. in all dai wannan gayen ya hadu iya haduwa, tun daga gashin kanshi har zuwa yatsar qafar shi babu abin kushewa.. asali ma irin mazan nan ne wadanda idan ka kalle su zaka kasa dauke idanuwan ka daga kansu saboda kyau da kwarjini.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now