Chapter Seventeen

959 145 58
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

A yau Monday Hanifa tayi resuming aiki.. A yau din kuma tun da safe Paapa yayi tafiya zuwa qasar South Africa a dalilin wani business deal da zai yi sealing.

Hanifa dai a yanzu haka tun daga ranar da Sadiq ya zo suka yi exchanging words sai ta saki ranta.. Abin mamaki shine tun daga wannan ranar ta daina neman hanyar da zata bi ta wargaza maganar auren instead she is now looking forward to auren don kuwa ta riga ta gama shirya mishi kalolin bala'in da zata yi mishi a gidan shi wanda ko kwana uku bazata yi a gidan ba zata fitine shi ya gaji ya sallame ta.

Wuraren qarfe Goma da rabi na safe suna zaune a conference room suna meeting.. Sadiq a matsayin shi na General Manager shine yayi chairing meeting din.. Yawanci kusan yana qara jaddada ma kowa muhimmancin role dinshi ne a kamfanin tunda dai as it is lokacin tafiyar shi ya zo, In less than 2 weeks zai tafi. har ma ya riga ya fara shirya hand over notes dinshi.. Gaba dayan su present a wurin idan ka kalli fuskokin su zaka gane they are sad, mai karatu ba wani abu ya sanya hakan ba sai don kewar Sadiq da suka fara yi tun kafin ya tafi..

Tun qarfe tara ne aka fara meeting din wanda kowa yana nan amma banda Hanifa.. Hanifa dai tana sane da meeting din kuma tana zaune a ofis dinta, Niyyanta shine sai ana daf da gamawa zata shiga ta ga tsiya.. Da alama dai ta shirya fara karta ma Sadiq rashin mutunci tun yanzu.

Aikuwa suna daf da rounding up ne ta shigo conference room din cikin isa da gadara.. Sanye take cikin wata doguwar rigar material mai kyan gaske peach color.. ta yafa gyale a kanta wanda bai hana dogon gashin nata fitowa ba.. sai baza qamshi take yi as usual.

Gaba dayan Unit heads din suka dago kai suka kalle ta cike da mamaki.. Ba tare da tace komai ba na ga ta nufi one of the empty seats zata zauna...

"why are you late?? baki ga meeting notification bane??" Sadiq ya tambayeta.

Hanifa wadda ta qarasa kujera ta zauna ce tace "Yes I did.." yayinda ta danna mishi harara

"So???" ya tambaya fuska a murtuke

"So I decided to come in now.." ta fada cike da gadara.

Gaba daya Unit heads sunyi mamakin attitude din Hanifa, Tabbas sun sani cewar bata jin magana toh amma kuma they thought bayan ta gane ko Sadiq waye zata shafa mishi lafiya..

"Okay Ms Hanifa.. you know the rule" ya kalli Musbahu yace "she should pay a fine of N5000 for coming late.. so take note"

Tun kafin ya rufe baki ta miqe tsaye tace "what???"

Gaba daya kowa ya mayar da hankalin shi kanta.. mamaki suke yi ganin reaction dinta, Babu wanda bai san rule na meeting a ofis din ba.. idan kayi latti ko na minti biyar ne sai ka biya fine na N5000 haka idan wayar ka tayi ringing sai ka biya N3000.. a gaban ta mutane sun sha biyan fines dinnan so why is she surprised don an ce zata biya???

"You heard me right Ms Hanifa.."

"I wont pay a single dime, babu abinda zan biya.. You hear me??" ta fada with so much confidence.

Shi dai Hafeez wanda yake zaune kadan ta rage ya fashe da dariya.. shi fa dama ya san tun kafin ayi auren nan za'a fara drama.

Sadiq ya kalli Musbahu yace "HR deduct it from her salary if she refuse to pay.."

"Nah Mr Sadiq.. ka cire daga cikin kudin sadaki na instead.."

"what???" gaba daya suka fada confusedly.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now