Chapter Thirty-Five

1.4K 183 141
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUNZA OIL & GAS
ABUJA CENTRAL

Tsaye yake a mini lounge dinshi gaban centre table yayinda yake riqe da wani cute bouquet na white Roses da wani qaramin kati.. Wasu beautiful warmers masu kyau na gani a kan centre table din.

Ko da na leqa katin da yake hannun shi wani rubutu na gani mai shegen kyau kamar haka..

I don't want to set the world on fire, I just want to start a flame in your heart.. I love you with all of my heart Baby!
Your wifey Hanifa

Sadiq ya karanta message din da yake kan card dinnan ya fi sau ashirin.. it's as if he is looking for something a message din amma ya kasa gano shi.

Ni da na kalle shi sai na gan shi kamar a rude yake.. toh fa!

Gani nayi ya ajiye card message din a gefen warmers din sannan ya koma ya zauna kan kujera still holding the bouquet.. Resting bayan shi yayi a kujerar yayinda ya daga kanshi sama ya rufe idanuwan shi..

A yau tunda ya bar gida he wasn't himself a dalilin Hanifa.. For the first time in his life ya shiga ofis dinshi ya zauna amma ya kasa yin komai tun safe. He is doing nothing but think about her.

Farkon haduwar shi da ita ya tuno- kalolin wulaqanci da rashin mutuncin da tayi mishi wanda har ya kai su ga yin aure. Tabbas Sadiq ya tsani Hanifa tun farkon haduwar su saboda a rayuwarshi baya qaunar mutum mai girman kai ji-ji da kai da wulaqanta mutane.. bai taba tsanar wani ba a duniyan nan kamarta.. again, tayi mishi laifin da ta bata mishi rai sossai wanda a dalilin haushinta da ya ji ne yayi accepting proposal din Paapa na ya aure ta.. he did that for one reason- to teach her a lesson.

He didnt even teach her the lesson he wanted to because shi din ba mugu bane tun asali but still he made life a bit difficult for her a gidan shi. A lokacin da yake daf da ya sallame ta kuma wannan qaddararren al'amarin ya faru tsakanin su wanda ta samu ciki and then everything changed.. Naana ta tilasta mishi zama da yarinyar da ya tsana a rayuwar shi and now she has fallen hopelessly in love with him..

A yau duk girman kai, ji-ji da kai da gadara na Hanifa ta sauke su a gefe tana roqon shi ya so ta. She is so much in love with him da har take zubar da hawaye non-stop a dalilin shi. she even went ahead and forced herself ta koyi abubuwan da bata iya ba wanda ta san yana so just to impress him.. if there is one genuine thing he believes right now is Soyayyar da Hanifa take yi mishi.

Sadiq bai taba yin soyayya ba, bai taba son wata mace da sunan soyayya ba.. A halin da ake ciki a yanzu tabbas he doesn't hate Hanifa anymore, tausayinta yake ji. He realised this after their little drama this morning.. Bugun zuciyarta ya tuno a lokacin da ta rungume shi, it felt like zuciyarta zata faso qirjinta and all because of soyayyar da take yi mishi.

Abinda Hanifa take nema a wurinshi bazata samu ba.. He doesnt feel love for her and he doesn't want to hurt her. The question now is- what can he do to help ease her pain??

"Hmmmm.. Romeo ina can ina fama da clients ashe kana nan ka riqe flower ka yi nisa a tunani.."

Bude idanuwan shi yayi ya ga Faisal tsaye a gaban shi riqe da card message din da Hanifa ta rubuto yana karantawa yana murmushi.

"Wow.. na ga alama wurin ku zamu zo koyon soyayya mutumina.. You mean this card and the bouquet are only here to accompany your lunch?? I am sure you guys will outshine us in Dubai"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now