Chapter Twenty-Seven

1.2K 156 182
                                    

RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO

A yau Saturday, its exactly 4 days da Sadiq ya qwace mata waya..

Hanifa dai tun daga wannan ranar tayi ma kanta alqawari bazata qara yin aikin gidan ba, idan ma zai kashe ta ne ya kashe ta qarewar mugunta.. Tun tana sa ran zata ga ya zo yayi mata magana har ta cire... abinda kawai take yi shine wanke plate dinta na Indomie idan ta dafa..

A kullum da safe, da rana, da dare indomie take dafawa tana ci tunda dai shi kadai ta iya.. shima din improving take yi domin kuwa tun baya dadi har ya dan fara yin dadi (tabbas practice makes perfect)

Inda tayi sa'a shine akwai Chocolate dayawa a gidan.. Ta tabbatar cewar Sadiq is a fan of Chocolates domin kuwa idan ba haka ba babu abinda zai sa ya siya foreign and expensive chocolates da yawa ya ajiye a gida.. it seems to be something they both like in common.

A dalilin ta sani cewar idan ya ankara da tana ci mishi zai iya kwashewa ya boye ne tayi sauri ta kwashi dayawa ta kai dakinta.

A yanzu haka gaba daya rayuwarta babu dadi. Ita gashi dama ba mai kallon TV bace balle ta kunna tayi kallo. Wayarta ita ce take debe mata kewa, Hanifa tana bala'in son wayarta domin kuwa a nan take ganin sabbin collections na kaya da turarruka da sauran abubuwa.. Yanzu kuma da babu ya zata yi????

Tun daga wannan ranar bata qara ganin Sadiq ba.. Ko motsin shi bata ji ba. Wani lokacin ma takan yi tunani ko yayi tafiya ne.. abinda dai ta sani shine the next time da zasu hadu she will make sure tayi provoking dinshi har ya furta mata saki..

A yau kwana biyu kenan da take jin jikinta babu dadi.. ta danganta hakan da boredom domin kuwa babu abinda take yi banda Sallah, wanka, cin indomie da chocolate sai kuma bacci. Gaba daya jin jikinta take yi very weak.

*****************

Kwance take a kan gadon ta cikin Duvet wuraren qarfe hudu da rabi na yamma.. Yau din dai throughout tana kwance a kan gado, lokacin sallah ne kawai take tashi sai kuma da rana when she went to the kitchen to make indomie for herself.. Gani nayi ta tashi zaune yayinda tayi stretching hannuwan ta, she is definately feeling weak!

Gani nayi ta sauka ta shige dressing room dinta tayi shirin wanka..

Hanifa dai ko da ta shiga bathroom shigewa tayi cikin jacuzzi bath tayi zaman ta a cikin ruwan turarruka masu qamshin gaske.. tayi kusan tsawon minti arba'in sannan tayi wankan ta fito.

Ko da ta zauna gaban Vanity mirror gani nayi tana ta bin jikin ta da mayyukanta masu qamshi kala-kala.. Bayan ta gama sai na ga ta fara fesa turaruka suma.. A yadda na ga Hanifa tana baza turaruka a jikinta kai ka rantse zata je turakar mijinta ne..

Ni kuwa nace ba dai Sadiq ba!🤣

Ina kallonta na ga ta dauko wadannan turarukan da Anty Anisa ta bata.. Suma gani nayi ta fara bin jikinta da su tana ta shafawa.. Aikuwa nan da nan na ji wani qamshi mai bala'in dadi ya tashi.. wannan qamshin dai daban yake da duk wani qamshi da ka sani mai karatu!

Man gashinta masu qamshi ta shiga shafawa a kanta yayinda ta janyo comb tana tajewa.. Haka ta saki gashin nata wanda ya kwanta a gadon bayanta da kafadun ta... Gashin yayi kyau sossai sai qyalli yake yi.

Miqewa tayi ta nufi closet dinta sannan ta bude wadrobe na qananan kayanta..

Gani nayi ta janyo wata white material loose shirt dress gajera wadda idan aka dunqule ta za'a iya saka ta cikin kofin shan ruwa.. Daga nan kuma ta koma gefen inner wears dinta ta dauki set na red bra da pant ta dawo gaban dressing mirror ta sanya.. shirt din is very transparent gashi iyakar tsawon ta rabin cinyar ta.. Gaba daya jikinta a bayyane yake a cikin wannan rigar don kuwa zan iya cewa da ita da babu ita uwa su daya..!

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now