Chapter Eleven

952 168 78
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

3 days later!!

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

Zaune yake a ofis dinshi yayinda yake qoqarin kammala project dinshi na online course din da yake yi.

It's been 3 months kenan da yayi registration na wani advanced course mai suna Strategic Business Analytics a ESSEC Business school na qasar France. Sadiq dai yayi Online business courses dayawa, wannan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya zama professional when it comes to business dealings. A yanzu haka wannan particular course din ba kowa ne zai iya yin shi ba domin kuwa sai kana da wasu special qualifications.. Course din yana da bala'in wahala sannan ga tsada. Lokutta da dama Sadiq yakan yi da-na-sanin yin course din saboda yana draining mishi energy da time sossai.. though he has gained alot from it don kuwa it's an advanced business strategy wanda yake applying in both companies that he is running toh amma dai kawai ya gaji.

Ranar Saturday da Sunday ne za'a yi presentation na final project through Zoom wanda daga shi an gama sai karbar certificate. Sossai ya qagara a gama ya huta.

He has spent alot of his time and energy, infact harda sleepless nights in order to get his project done.. Yanzu haka yana finishing touches ne and going through to correct the minor errors he's made..

Hanifa ce ta shigo office din kai tsaye ba tare da tayi sallama ba balle ta qwanqwasa qofar.. ita dai Suzan tun tana zuwa tana ba Sadiq haquri akan yadda Hanifa take shiga ofis dinshi har ta daina tunda dai ta kula 'yar mai kamfanin ce kuma da alama bazata taba dainawa ba.

Wasu files ne na gani a hannun ta yayinda ta qaraso wurin shi tana hararar shi ta zauna ta tura mishi su gaban shi a wulaqance ba tare da tace komai ba.

Har yau idan Hanifa ta tuno yadda Sadiq ya barta ta kwana a Cell ji take yi kamar ta shaqe shi.. A yanzu haka sai gabza mishi harara take yi wanda bai ma san tana yi ba!

Sadiq wanda as usual bai dago kai ba balle ya kalleta ne yake mamakin halin banza irin na Hanifa.. and this brought him back to the conversation he had with her Dad 3 days ago.

A ranar dai Sadiq ya lallaba Paapa ne ya ce mishi zai yi tunani akai and he will get back to him.. he couldn't say no amma kuma its definately a NO.. Babu yadda za'ayi ya dauki yarinyar da ya tsana ya kai ta gidan shi.. dukda kuwa dalilin yin haka is something he'd love to do amma still.. Tsanar da yayi ma Hanifa is just out of this world.

Addu'a yake yi akan Allah yasa kar Paapa ya qara dauko mishi zancen wanda in less than a month da ya rage mishi ya tattara yayi tafiyar shi..

Hanifa wadda take zaune tayi zooming takardun da suke gaban shi da kuma manyan litattafai na Business.. hakan ya tabbatar mata da lallai karatu yake yi.

Bata ankara bane ta ji wayar shi tayi ringing yayinda ta ga ya duba..

Video call ne from his Mini-Me

Answering yayi tare da saita wayar da kyau a kan phone stand yadda zata dinga ganin fuskar shi.. Ko da na leqa, fuskar wata kyakyawar cute yarinya na gani, tana yanayi da Sadiq amma ta fi shi haske.

"Assalamu alaikum" ta fada cikin zazzaqar muryarta mai masifar dadi.

"wa'alaikis Salam Asma'ul Husna sarauniyar mata" ya fada yana murmushi.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now