💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)**Salmerh MD*
🅿️ *...11*
'Bangaren Adam Shaheed kuwa sai da ya shafe kwanaki biyu ras idanun sa basu ga hasken rana ba, sai da abokin sa Hafeez ya azazzale shi da mita kafin ya shirya ya fito, sai dai kafin ya je wajen Hafeez 'din ya yanke shawarar fara zuwa wajen Zaitun bfore ya wuce wajen Hafeez 'din dan ba karamin kewar ta yayi ba, gashi ya hana ta fita ya hana ta zuwa aiki yace kar taje ko'ina, kuma yana da tabbacin matu'kar ya hana 'din toh Zaitun bazata je ko'ina din ba kamar yadda ya bukata...in haka ne kuwa yasan jin shiru daga gare shi bai kamata ba sam domin haka na iya haifar mata da wasiwasi akan sa.
Haka ya isa kofar gidan da niyyar 'kara mata 'kwarin gwiwa dan har yanzu bai cire rai da samun ta ba yana ji aransa da iznin Allah Zaitun tashi ce.
Ba yau yasan halin Hajiyar sa ba, lokaci guda take hawa tamkar kumfa in kuwa ta sauka shikenan komai yake wucewa a wurin ta...yana kyautata zaton nan da 'dan wani lokaci Hajiyar zata sauko daga dokin na'kin da ta hau za kuma ta amince da kudurin sa na auren Zaitun, tunda batun aure ne ya 'dauko ba sa6on Allah ba.Komai da yake yi cikin sanyi yake yin sa, dan shi ka'dai yasan irin halin da yake jin zuciyar sa ciki...kamar kaine ace rana guda za'a raba ka da wani abu mafi soyuwa a wajenka a zuciar ka..abin ba sauqi, balle Zaitun da ya dauki duk buri da farin cikin rayuwar sa ya 'daura a kanta, be ta6a kallon kowace mace da sunan soyayya ba sai Zaitun, akan ta ya sanin zafin so akan ta yasan 'kauna ta asali da ta boge, amma rana tsaka Hajiya na neman tarwatsa duk tubalin da ya fara ginawa.
Yaro ya aika kamar yadda ya saba kullun amma sai bai fahimci amsar da yaron ke san sanar da shi ba..." an ce wai bata gidan tun jiya...."
Abinda yaron ya sanar da shi kenan matsayin amsar aiken da yai masa.Take yaji bugun zuciya mai tsanani.." tun jiya kuma...?"
Ya sake tambayar yaron yana mai kankance idanu cike da rashin yadda da maganar.
" Erh Hajja ce tace a fa'da maka...".
Guntuwar tsaki yaja jin cewa Hajja ce duk ji yayi ma bai yadda da zancen ba gaba 'daya, ai duk yana da lbrn yadda Hajjan ta tsani Zaitun, baya raba 'dayan biyu wani makircin Hajja ta shirya kuma.
" Amma kai kaga alamun tana gidan ne...?"
Ya sake tambayar yaron.
Sai cewa yayi.." a a ni dai Hajja ka'dai na gani kuma ita ta fa'da min..."
" Toh fa..! Kaga dan Allah koma kace wai afa'da maka inda taje..sai kazo ka fa'da min kaji?...".
Haka yaron ya koma cikin gidan, can sai gashi ya sake fitowa Hajja tafe a bayan sa da guntun mayafin ta aka...
Hango Hajja bayan yaron ya sanya Adam maida hankalin sa gareta batare da ya sake bi takan yaron ba..." aww kaine ashe...yaro ai mutuniyar taka bata nan tun jiya Hajiyar gidan tazo da kanta ta sallame ta babu kuma wanda yasan inda ta nufa..."
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..sallama kuma kamar yaya?...ban fahimce ki ba wlh Mama..."
" Koranta Hajiya tayi daga gidan inajin dai wani laifi tayi mata.."
" Subhanallahi...wai kina nufin Hajiyata ce tazo har gidan nan..kuma ta kori Zaitun..?"
" Tabbas...".
Kansa ya dafe da hannun 'daya.
" Hajiya kin kashe ni..."!
bai san lokacin da hakan ma ya fito bakin sa ba saboda tsabar ka'duwan da yayi.. dafe kirjin sa yayi gami da zama bisa dakalin kofar gidan yana jin kamar ya fasa ihu ko zai sami sauqin zuciyar sa.Hajja kam ciki ta koma tana mita 'kasa 'kasa" Jimin kinbabbe, santalelen yaro da kai ka tsaya lalacewa karkashin waccan banzar..."
Itakam Hajja ai barka tayi ma da faruwar wannan lamarin, dan a cewar ta an yada kwallon mangoro menene abin damuwa ban da kayi farin ciki 'kuda sun bar ka...yarinya duk tabi ta hana kowa zaman lafiya.
Shi kan sa Bbn Abdul ba karamin tashin hankali ya shiga ba da Hajjan ke sanar masa yadda abin ya kasance..." ke kuma Hajja sai kika barta ta tafi batare da kin bincika kinsan inda zata je ba?"
Yayi maganar ne cike da alhini gami da haushin rabuwa da Zaitun din adaidai lokacin yake tsaka da kaunar kasancewa tare da ita.Wani zabura Hajja tayi tayo kansa da masifar ya yake so tayi da ita ne bacin masu gida ne da kansu suka sallame ta...ana me zata tsaida ta.
Bbn Abdul bai ko sake tanka Hajjan ba ya tafi 6angaren su yana me fatan Allah ya sake nuna mishi Zaituna a lokacin ne zai fito fili ya nunawa Hajjan cewa shifa dagaske yake son ta ba wasa ba.
Wannan shine yadda suka yi da Bbn Abdul akan Zaitunan....wanda duk Hajjan tana kan hanyar komawa gida take sake tariyowa, ai kuwa sai jan wata doguwar tsaki tayi ta fara magana a fili ita kadai..." Yarinya sai kace 'kanwar ifiritu".
Sam ta rasa itan wace iriyar yarinya ce, bayaga haka ace duk wadannan zabga- zabgan mazajen na shiga rudu saboda rashin ta?...( Adam da Bbn Abdul).Adam sai da ya shafe kimanin rabin sa'a zaune a wajen batare da ya motsa ba hannuwan sa daya dafe da saitin zuciyar sa bai sauke ba, shi kadai yasan abinda yake ya kuma san damuwar da hakan ya haifar masa...bai ta6a kawowa aransa Hajiya zata aikata hakan ba.
Iya tunanin sa ya kure na inda Zaitunan zata shiga a fa'din garin amma bai tunano komai ba bai tuna kowa da yasan ta sani ba, gashi bata da waya taki yadda ya sai mata wayan dan acewar ta ita wa take da da har zata yi magana da shi a waya...yau ga ranar wayar ai.
Daga nan bai zame ko'ina ba sai gidan Hajiya wajen Hafez 'din ma fasa zuwa yayi gaba 'daya, 'dakin sa ya shige ya kwanta, tun yana tunani har tunanin nasa ya toshe baki 'daya..sallah ka'dai ke iya tada shi.
Ko da Hajiya ta dawo ma bai iya ya tanka ta ba, toh me zai ce mata? Abinda ya faru ya riga ya faru bazai iya dawo da lamarin baya ba, kuma yasan duk Hajiya na yin hakan ne a tunanin ta sbd ta tseratar masa da mutuncin sa..dan haka bai 'kara tada maganar ba kawai yake jinyar zuciyar sa a tsaye ko abinci ba iya ci sosai yake ba...kafin wasu kwanaki har ya zabge ya rame sosai.
Hajiya da fari share sa tayi ta fita sabgar sa a cewar ta yayi ya gama fushin da kansa ma ze sauko ne, sai daga baya kuma da kanta ta fuskanci abin fa ba fushi ne kadai da alamu hatta lafiyar sa ma da ta jima tana tattali ya samu gi6i, sai kuma taji ta damu._Salmerh_ 😘

ČTEŠ
BINTEEE ( 'Yata ce)
BeletrieSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....