P107

90 7 4
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...107*

               .......Yanda kuwa ake shirin bikin Marwa abin har zai baka mamaki..gagarumin shiri ake na gani a fada babu kama hannun yaro.

Babu wanda ya yadda aka barsa abaya wajen shiri.
Haushin Zaitoon 'daya Marwa Bauchi za a akaita ba Nan Kano ba, tayi tayi da Adam kuma ya barta nan Kano amma yaki.
Yace an'ki wayon, yace meyasa ke ba a barki can wajen Innar ki ba aka kawo ki nan..in haka ake yi ai kema can za a barki..".
Tace" ai ni qin amincewa akayi amma nafi son can, kuma itama Innar ba yadda zata yi ba kasani...".
" Toh nima naqi amincewa, kuma ina da tabbacin itama Ammi ba yadda zatayi abar Marwan anan ba...gara dai akawo min amarya ta nan kusa da ni da Hajiya ta yafi min".

Har ta 'dan yi fushi da shima ta daina daukan wayar sa na kwana biyu kuma sai ta zo basar sanin ya fita gaskia...ba hujja gare ta ba.
Dama ita mace bata da zabi, duk inda kaddarar aure ya kaita dole taje kuma ta zauna...tadai san dole Marwa zatayi kewar gida sosai, suma kuma zasu yi kewar ta, shiyasa tun yanzun take jin tausayin ta.
Domin a kaf din tarihin Marwa da ta sani tun tashin ta har kawo girman ta bata ta6a barin gaban Ammi ba, har auren ta na farko tare suke, kusan ma tare da Ammin take rayuwar ta kuma har yau basu rabu.

Ana biki saura 1week suka dawo, ranar kam Zaitoon ansha farin ciki domin saukan bazata sukai musu.
Adama Ammi nata mita da fadan me suke jira acan ne har lokacin basu dawo ba, ga Adam ma ya ishi Zaitoon har ya yi niyyan tafia amma Zaitoon ta hanashi sbd Marwa ta sanar da ita abinda ya sa basu taso tuntuni din ba sakamakon gyran jiki da ake yi mata.
Da kyar ta samu Shaheed ya bar batun tafiyar nan.

Ai kuwa ganin yadda kowa ya damu da batun amarya bata Kano ga masifan Ammi dan ita kan ma cewa tayi abar gyaran jikin nan kawai su taho, hakan yasa suka yi musu diran bazata.

Gidan ya cika makil baki na nesa da na kusa.
Yadda kuwa Marwa ta sha gyaran jiki tayi matu'kar kyau tamkar ba ita ba inka dube ta har ji zakayi tamkar ba ita ba.

Tun daga ranar Zaitoon ta fara tsokanar ta da suna amarya bata sake kiranta da wani suna sabanin hakan ba.

Tana dariyar mugunta ta kira Adam tace albishirin ka.."
Yace" goro fari tass...kar kice min gimbiya ta ta iso".
" Wani gimbiya, ana maganar kyakykyawa, kazo gida yau kaga wata yar kykkyawan babe agidan mu..".
'Yar daria yayi
" Kice kyakykyawa ta ta iso mana Zaitoon, nakira ai bata 'daga ba...".
Baki ta kama tace
" Kai ya Adam ya akayi ka sani alhalin muma zuwan bazata akai mana..".
Daria sosai kawai yayi ya yanke wayar.
Ana fitowa a sallahn maghrib daga nan masallacin yayo gidan.

Marwa tana tura baki ta iso inda yake.
" Shi kuma fushin na menene?..
Ya tambaya yana duban fuskar ta.
Bata ce komai ba sai ma sake jade rai da take.
" Gimbiya ko in koma ne naga alamun sam ba ayi farin cikin gani na ba..".
" Fisabilillahi ko hutawa baza'a bar mutun yayi ba sai ka wani zo...".
" Taya kk tunanin za'a bar mutum ya huta bacin an 'kyan:kyasawa bawan Allah kykkyawa ta dawo..".
" Mamin Mufee ko?"
" Ni dai ban ce ba..".
Ya bata amsa yana daria.
" Amma dai koma waye ne ai ni ya taimake ni ne da kallon wannan kyakkyawan bai  wuce ni ba ayau".
Murmushi kawai tayi...a hankali tace" Ina yini..?"
" Lafia kalau..hope kun dawo lafia..?"
" Alhamdulillah.
" Ya cikin gidan?"
" Suna kalau..".
" Kinyi kyau Marwa ta, kin yi kyau sosai...".
Yayi maganar yana kjingina bayan sa jikin kujeran motar da yake zaune.
Kai ta kara sunkuyar wa sosai.
Shi kuma ya cigaba.
" Wai da ma ke kina tunanin zan iya sanin kin dawo ayau kuma in kasa zuwa ganin ki ne..ai sai in kwana ina firgita cikin bacci..in ma na iya baccin kenan".
Daria sukai dukkan su.
Marwa ta kuma sunkuyar da kai tana murmushi take fadin.
" Toh me ne a ciki...sai ince maka mun kwana ne a hanya bamu samu isowa da wuri ba ai....".
" Dan kawai a cuci bawan Allah ko...".
" Hmm.."kawai tace sannan ta cigaba.
" Amma dai  tsakani da Allah Yah Adam 'kamshin nan naka fa yayi yawa, yanzu haka ka taho tun daga gida kana wannan 'kamshin har zuwa nan...?"
" Toh me zai yi..kin mance Ango ango nake yanzu...".
" Ya dai yi yawa, ai sai ayi ta waigowa ana duban ka idan ka gifta..".
Acikin motar...?"
Ya tambaya da Mamakin kalamanta.
" Ko dai an kishi ne 'yar yarinya"
Baki ta tura gaba..tana kya6e baki tace.
" Kishin me zanyi ni kuma..kawai dai ina fa'da maka ne sbd babu kyau..?"
" Ni fa namiji ne ba mace ba Marwa..ko kin manta?".
Shiru tayi, tayi tsam da ido tana duban sa, sai kuma ta sunkuyar da kanta 'kasa tana mai jin kunyar za'kewan da tayi.
Sam sai ma ta rasa me yasha kanta ne ma haka.
Yana daria yace
" Hafiz dina yana gaida ki, kinsan tare muka zo, kuma bazamu koma Bauchi ba sai da Amaryar mu.
Hmm kawai tace..bata sake wata doguwan magana ba har suka rabu.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now