💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*Wattpad@
Serlmerh-md🅿️ *...28*
.......Idanu Adam ya lumshe wani zazzafan hawayen na sake 6ul6ulo masa, batare da ya bu'de idanun ba ya cigaba da fa'din..." tun ina saka rai akan watarana zaka zo gare ni ka nuna min kauna da kulawa kamar yadda naga ake bawa sauran mutane kamata har nazo na fara fahimtar so na ne kawai baka yi shiyasa baka ta6a damuwa da lamari na ba, baka ta6a tuna cewa ka bar marayan yaro a hannun wata mace ba, baka tunanin yaro na yana rayuwa cikin duniya ban san halin da yake ciki ba, baka damu da lafiya ta ba, ci na ko sha na duk ba sune gaban ka ba, baka damu da ilimi na ba baka damu da yanayin tarbiya da halin rayuwa da zan iya fuskanta ba, baka damu da amanar da Allah ya dam'ka maka akaina ba, dukiyar ka ka'dai ce agaban ka, burin ka kawai shine ka tara arziki, kayi rayuwar ka duk yadda kake so batare da tuna cewa Allah na ganin ka ba, shin baka jin kunyar duk abubuwan da kake aikatawa ne Alhaji? Meyasa ka za6i wannan hanyar wajen salwantar da ni dama dukiyar ka batare da tsoron Allah ba? batare da tuna cewa ni har dukiyar taka duk 'din mu amana Allah ya baka ba?
Ka wofintar da ni ka barwa duniya ni ka za6i wa'dansu daban suka maye maka gurbi na, kuma na tabbata da mahaifiya ta na raye bazata ta6a yin watsi da ni da lamari na kamar yadda kai ka aikata ba, sau da dama na kan tuhumi kaina da zamtowa 'daa agare ka a mafi yawan lokuta na kan ce dama ba kai Allah ya za6a min matsayin mahaifi ba dan na tabbatar kai kanka baka shirya kar6a ta matsayin 'daa a lokacin da Allah ya azurta ka da samu na ba, sai da kaga na girma? Ciwo na ya ri'ka? 'Kunci ya gama mamaya ta? na gama gwagwarmayar rayuwa ta, na bar dukkan 'kalubale da na fuskanta abaya, karfi na ya fara kawowa na fara mantawa da damuwa da rashin ka kusa dani, lokacin da na fara burin gina rayuwa ta da halali na a lokacin ne zaka ce zaka tallafi rayuwa ta..? ka 'dauka ni 'din bani da zuciya cikin kirji na ne..? shin inada laifi ne idan nace bana bukatar komai daga gare ka? Alhaji ka bani amsar tambaya ta ina so in ji amsa ta daga bakin ka ne shin inada laifi ko guda anan....?".
Ya 'karashe maganar yana jin 'karin nawi cikin kirjin sa saboda rarrabuwar numfashi daya fara fuskanta, maganar ma da 'kyar ya 'karasa ta amma dan 'karfin hali ya dage sai yayi, inda ya 'karashe da wara idanu kan Alhajin yana faman dafe 'kirji sakamakon tari da ya sarke shi.
Hafeez da ya fahimci yana jin jiki da sauri ya iso gare shi yana kokarin kwantar masa da hankali, yasan dama lafiya ba isan Adam din sosai tayi ba amma taurin rai irin na Adam har na bashi tsoro wani lokaci, duk yadda yake da dauriya ji yadda yake dafe kirjin sa da gani kasan bisa dole yake hkn, ya da'de yana fama da ciwon zuciyar da babu wanda yasan farkon sa sai Allah mahalicci.Hannun sa da Hafeez ya kama yayi saurin fisgewa..." ka barni Hafeez, ka barni in tambaye shi abinda ya da'de yake damu na cikin zuciya ta, ban ta6a ganin halitta mafi tsananin son kai irin wannan mutumin ba ka bar ni in tambaye shi ya bani amsar tambaya ta.."
" Haba Adam! haba dan Allah baka ganin halin da kake ciki ne baka ganin yanayin kane? kar fa ka manta condition da kake ciki fa..."Cewar Hafeez ga Adam cike da kulawa.
" Ba wannan ne damuwa ta ba Hafeez, please let him answer my question, ya tsangwami rayuwa ta, ya hana ni fuskantar rayuwata, shi lokacin da ya fara tashi rayuwar waye ya taka masa birki, ko akwai wanda ya ce lallai lallai dole shi zai za6a masa sana'ar yi ?"
Idon Hafeez cikin na Adam yake masa kallon rashin jin dadin kalaman sa, kai ya girgiza masa gami da lumshe ido yayi kasa da kansa.
Sosai Adam ya fahimci Hafeez dan ba sanin yau ke tsakanin su ba, sani ce mai cike da fahimtar da juna ya kuma san Hafeez da zuciya 'daya yake 'kaunar sa.
Shima 'din 'kasa yayi da nasa kan yana mai zazzafan numfashi yayin da Hafeez ya cigaba da fa'din.." Bana jin da'din kalaman naka Adam, please mu koma gida...".
Ya 'karashe maganar ya tallafo hannun Adam da nufin mi'kar da dashi.'Dan Maliki dake tsaye ne yayi saurin dakatar da shi da 'daga masa hannu gami da fa'din"...Kaga barshi yayi maganar sa, barshi ya amaryar da duk abinda ke ransa, na cancanci kowace irin magana ce daga gare shi a yanzun matukar zai sa ya fuskance ni, kuma shima na tabbatar hakan zai fi sama masa sauki a zuciya..".
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....