💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...47*
.......Koda Mummyn Amrah ta yiwa Ammi magana, Ammi bata ce da ita komai ba illah hakuri da ta bata, sai dai jin tana cewa mai aiki- mai aiki cikin maganar ta yasa Ammin tabbatar mata da cewar yarinyar ba wai mai aiki ce kawai kamar kowa ba, tace 'yantacciya ce a wurin ta tamkar 'diyar cikin ta take kawai ta bari ne tana taimakawa Amrah da wasu ayyukan na cikin gida dan haka itama Amrah bata da damar da zata ringa wulakanta tata son ranta.
Haushi sosai mahaifiyar Amrah taji hakan yasa ta kashe wayar batare da ta sake tankawa Ammi ba.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan lamarin babu wani abu da ya sake shiga tsakanin ta da Amrah, hasalima daina ganin ta tayi, ko ta shigo aikin ta basu haduwa da Amrah har ta kammala ta bar sashen ita kamma sai tafi sakewa da hakan, saboda ba kaunar tashin hankalin nan take yi ba sam a dole take biye mata...baya ga haka ma Ammi ta sake bata hakuri gami da garga'dan ta kan biyewa Amrahn, ta kuma fahimci Ammi, musamman sbd cikin da suke matukar tattali da Amrahn ke 'dauke dashi, kusan kaf ahalin ta lura duk wata kauna da soyayyar su kan cikin suka mika ta, ita kuwa bazata so tayi ta mata musu rai a banza ba, dan ta lura indai akam cikin nan ne toh kuwa ba sauki zata samu daga gare su ba duk kuwa da irin 'daga mata 'kafa da Ammi take bazata iya kawar da kai kan gudan jinin jikan ta da suke daukin zuwan sa duniya ba...hakan yasa ta yanke shawarar kiyaye komai da zai iya hada ta da Amrah kuma Alhamdulillah itama Amrah kamar tasan nufin ta sai ta ja baya.
Bayan kwanaki biyu...
Zaitun na kitchen tana ha'da musu abincin su na dinner ta fara jiyo hayaniyar Amrah, da sauri ta waiga ta ga Moopy na nan kitchen tana wasan ta kasan ta tiles, hakan ya tabbatar mata da cewa ba da ita take yi ba.
Ajiyar zuciya ta sauke gami da hamdala a fili.Ka'dan da ka'dan ta fara jiyo hayaniyan na kusanto wa kitchen inda take.
Bata fahimci komai cikin maganar Amrah kasantuwar amsa kuwwa da maganar ke yi kuma ba cikin natsuwa Amrah ke maganar ba.
Har sai da Amrah ta iso bakin kitchen tana masifar wai Zaitoon ta fito mata da sarkar ta data sace mata in ba haka ba wallahi sai ta sa an mata 'daurin da babu uban da ya isa fitar da ita.Sosai Zaitun tayi mamaki jin wai ita Amrah ke tuhuma da sata satan ma na sarkar Zinare ita kam me zata yi da wani abu wai shi sarka a rayuwar ta.
Duk kuma yadda taso fahimtar da Amrah abin ya faskara kokadan bata bata damar hakan ba sai ma sake azalzalar ta da take tana kumfar baki.
Abin takaici ko da mai gidan yaji hayaniyar su ya sakko ma ko tankawa Amrah bai yi ba balle ya tsawatar mata kan sharrin da take shirin kullawa Zaitun.
Kokarin ficewa ma yayi daga 6angaren Amrah ce tayi saurin dakatar da shi da fadin" Baby kace ta fito min da sarka ta in ba haka ba wlh sai na sa an 'daure ta..."
Ta karashe maganar tana wani jijjiga kamar wata jaruma.
Kallon Amrah yayi cikin ido sosai, bai ga alamun gaskia ko 'yar ka'dan tattare da ita ba, yasan ba mmk huce takaicin ta yasa ta biyowa ta wannan sigar...ba yau yasan Amrah ba, ba tun yau ya karanci yanayin ta ba.Ga Zaitun ya maida duban sa da take tsaye wuri wuri da idanu waje, kallo 'daya yai mata ya 'dauke kansa ganin yadda idanun ta suka cicciko..." Ki bata abinta in ke kika 'dauka pls bana son wannan hayaniyar...".
Tamkar zatayi aman wuta haka take jin zuciyar ta, wai yau ita Zaitun Ahmad Kyari ake tuhuma da sata? sharrin sata fa..?
Shin shi talaucin hauka ne? Ko kuwa rashin galihu ne haukar? Koko rashin gata kawai yasa akai mata wannan sharrin?
Saboda rasa abin fa'da kawai sai ta ringa bin su da kallo 'daya bayan 'daya hawayen ma ya kasa gangarowa.
Ba abinda yafi tsaya mata arai irin furucin Rayyan, a tunanin ta shi din yafi Amrah hankali, a tunanin ta zai dakatar da 'kudurin Amrah ne, amma sa6anin hakan sai ma biye mata da yayi..kenan sun taru sun ha'de mata baki ne, ko dai dama bakin su 'daya, ba mamaki tare suka yi shawarar hakan dan su tozarta ta dama tasan duk ba kaunar zaman ta gidan suke ba...baya ga haka meyasa daga fadin magana har ya hau ya yadda.
M
Toh ita a zaman tan nan idan ta saci sar'ka mai zata yi da shi? ina zata kai sar'ka cikin duniyar nan, in satan zata yi meyasa bata yi tun abaya ba sai yanzu..?
Meyasa basa ta6a fahimtar ne wai?, kan abubuwa da dama sai sun 'kalubalance ta?.
Shin zama da su dole ne ko kuwa 'daure ta akayi tare da su.
CZYTASZ
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....