P43

72 13 4
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...43*

                  .....Ta 'kofan kitchen Zaitun tabi ta wuce 'dakin ta bata kuma san lokacin da suka bar 6angaren ba.
Babu wanda ya san abinda ya faru tsakanin ku hatta da Marwa Zaitun bata bawa labari ba..haka kuma bata fasa zuwa dan yin aiki ba.

Bayan kwana Biyu Ammi ta tafi Abuja Marwa taje Zaria yin clearance na makarantar ta.
Zaitun sam sai taji gidan yayi mata fili sosai sbd bata ganin Marwa yanzu, sanyin ta ma sai ya 'karu, yanzu duk abinda Amra zatai mata bata ko 'daga idanu ta dube ta ma balle mayar da martani.

A hankali Mufeeda ta fara er zazza6i, tun abin bai yi zafi ba har zazza6in ya shiga jikin ta sosai, Zaitun ta rasa yadda zata yi da yarinyar.

'Daya cikin sabbin masu aikin gidan ne ta bata shawarar bata paracetamol amma still jikin sai a hankali.

Zaitun kuka sosai take zaunawa tayi haka duk dare ita kanta sai da tayi 'yar rama.
Ko 6angaren Amra ba zuwa take yi ba yanzu ita kadai tasan damuwar da take ciki.
Gashi har yanzu Ammi bata dawo ba haka Marwa ma...Sultan ma yanzu ba sosai yake shigowa ba.

Tana kwance a 'daki da wani yammaci da bama tasan wace rana bace ma tana sharar kwalla da tunanin mafita sai ji tayi ana mata sallama wai ana kiranta a Parlor.
Tayi niyyan barin yarinyar amma sai taji tsoron barin ta ita ka'dai, gani take kafin taje ta dawo Moopyn zata iya tafia ta barta saboda yadda zafin jikin ta yayi tsanani.

Jikin ta na 6ari ta fito idanun ta duk sun fito sbd yawan damuwar da take ciki.

Tana fitowa Rayyan bai ma bari ta gama 'karasowa ba ya fara fa'din" kin kuwa san aikin ki anya a gidan nan?"
Da jin hakan tasan mene laifin ta hakan yasa taja ta tsaya tayi 'kasa da idanun ta tana addu'ar Allah yasa yayi mata uzuri.
Cike da marairaita tace" Dan Allah kayi ha'kuri wallahi yarinya ta ce bata ....."
Bai bari takai aya ba ya tare ta da 'daga mata hannu, dama yasan a kullum excuse dinta kenan.
Ya gaji da wannan kalmar akoda yaushe, komai yarinyar ta yarinyar ta yarinyar ta, shi me ruwan sa da wani batun yarinyar ta, aiki aka 'dauke ta kuma ta yadda zata yi meyasa zata bar masa muhalli da kazanta kusan kwanaki uku yanzu, ko ina yayi 'kura babu kyan gani.

Kici kicin yayi da fuska yace
" Akan wata 'diyar ki ne bazaki je ki tsabtace min muhalli ba...?"
Yatsa ya 'daga ya nuna mata yana daga tsayen yace.." Wallahi idan kk kuskura kk kaini bango bazaki ji dadin hukunci na ba, bana son iskanci da rainin wayo, kullum da an ta6a ki yarinya, yarinya, ke ko kunyar fa'di bakiji? akanki aka fara haihuwa ne ko me...?"
Ammi ce da ke tsaye bakin 'kofar shigowa tayi saurin dakatar da shi da fa'din " Rayyaan...?"

Ransa a matu'kar 6ace ya waigo jin muryar mahaifiyar sa da be yi zato ba...'dan lumshe idanu yayi sannan ya juya ya isa gareta cikin natsuwa.

Handbag dake hannun ta ya kai hannu ya kar6a batare da ya yadda sun ha'de ido ba yace" Welcome Ammi".

Duk yadda Ammi ke kallon sa da 'ko'karin son ganin 'kwayar idanun sa sam ya'ki amincewa...ko wlcm da yy mata ma 'kin amsawa tayi.

Ganin hakan ya sashi fahimtar ranta ya 6aci ne da kalaman sa.
Bai yi mamaki ba bcuz shi da kansa ba ze iya fa'din tsawon lokacin da take tsaye a wurin ba.
Zaitun kam goge hawayen ta tayi da tun 'dazun ke gangaro mata tana sake ta6a fuskar Moopy dake rungune saman kafa'dar ta tana mai jin 'dumin jikin ta na sake ratsa nata jikin..tsananin tausayin Moopy ne ya cika mata zuciya banda wannan ba'kin suna da ake bi mata yarinya  da shi, duk duniya zata iya ha'kuri da komai amma bazata ta6a iya jure zagin Moopy da sunan shege ba..domin ta fahimci duk kalaman sa jurwaye yai mata, bai fito fili ya fadi kalmar ba amma duk dai hakan yake nufi while ita 'diyar ta ba shegiya bace kamar yadda suke tunani.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now