💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...95*
........" Abin kunya dan'kare cikin rayuwar ki amma har kina da guts fin tsomawa mutane baki cikin maganar su...?"
Ko zancen Anty Madeena na farko bai kai wannan soya zuciyar Amrah ba.
Sosai taji babu da'di ta kuma ji 6acin rai gami da fargaba matsananci ya kamata.
Fargabar ta 'daya ce na rashin sanin ainihin abinda Anty Madeena ke nufi da maganar ta, tsoro take ji kar ace tasan ko da guda ne daga cikin sirrin ta.
A zuciye ta tashi rungume da yaron ta mayafin ta na take mata baya tayi waje fuskar ta tamkar ba'kin hadari mai shirin zubda ruwa.
Tsaki Anty Madeena taja bayan ficewar Amran...sai dai tun ma kafin ta gama dawo da kallon ta cikin Parlon Ammi tace" Baki kyauta ba Madeena..ai bazata ji da'di ba ke kanki kin sani...".
"...so what rabu da ita dan Allah Hajia Aseeya, ina cikin yanayin farin ciki bana so takaicin ta ya canza ni...yarinyar bata da kunya ne sam...".
" Amma dai ko ba komai ai 'dan dai da take magana akai 'din ai shi dolen mu ne, sbd jinin 'dan mu ke yawo a jikin sa...ni shaf mancewa nayi da shi ma shiyasa na fa'di waccan maganar....".
" Ai dole ki mance tunda karere ne bb ha'din jini...".Cewar Anty Madeena a zafafe tana mai kawar da kanta.
Duban hakika Ammi tayi mata tana mai son gano manufar maganan, a hnkl ta kirayi sunan ta sau 'daya tak..Anty Madeena yi tayi tamkar bata san Ammin tana yi ba.Marwa ce ta mi'ke kawai ta kar6i Mufeeda dake hannun Ammi sannan ta 'dago hannun Zaitoon suka yi waje, ganin hakan yasa Badi'a da Imrana ma suka biyo bayan su aka bar Ammi da Anty Madeena ka'dai.
*****
Tunda ya fita ya bar parlorn yake jin zuciyar sa cikin wani irin yanayi da shi kansa bazai iya pointing takamamme halin da yake jin ta ciki ba, yana jin farin ciki tabbas da bayyanar wannan sirrin, amma ya rasa dalilin da yasa farin cikin nasa ya kasance ragagge.Ya kwanta a 'dakin sa yaji baya da natsuwa sam, hakan yasa ya fito duk da ciwon hannun sa yk hakan bai sa ya gaza tu'ka kansa da kansa a mota ba.
Can gidan sa ya wuce yana sake tunowasu abubuwa da suka shu'de shekaru ka'dan baya.
_Nadia_ !
Sunan ya gifta masa cikin kwanyar sa.
Sai ya lumshe idanu ya kuma bude su nan take.
Wannan karan lips 'din sa ne ya motsa wajen furta sunan Nadia akaro na biyu.
Kai ya girgiza a hnkl yana jin wani irin cikin ransa.Ashe tsakanin su bai 'kare ba..!
Ashe zai cigaba da ganin wani abu da ya dangance ta tare da shi...?
Har ya isa gidan tunanin da ke ransa kenan kuma koda ya shiga gidan ma still dai Nadian ne.Sosai ya 6ata lokaci wajen tunani a wancan gidan, amma abinda yake 'daure masa kai shine rashin sukunin zucia...da 'kyar ya iya gano inda matsalar damuwar tasa take.
Ba'kin ciki 'dacin rai yake ji da kuma tsananin kishin da ya jima bai tsinci kansa a cikin sa ba.
Yanzu da ya tabbatar da cewa erh da gaske Aishatul Mufeeda 'diyar sa ce sai yafi jin haushin abinda Amrah tayi masa fiye da baya.
Sultaan...!
Wannan karan sunan da ya gifta masa cikin 'kwakwalwa kenan.
Sai ya rintse idanu da 'karfin gaske yana jin zuciyar sa na harbawa.A yadda yake ji a halin yanzu baya ji akwai abinda yafi tsana da 'kin jini irin Sultan...Sultan yayi masa abubuwa masu dama da ya tabbatar daga yanzu har zuwa ranar da ransa zai bar dunia mawuyaci ne ya iya mancewa da su.
Duk yadda yaso ya kawar da tunanin cikin ransa kuwa sam ya gagara yin hakan.
Wata zazzafar wuta mai tiriri yake ji take ruruwa masa a zucia game da Sultan, tiririn da gaba 'daya yy nasarar lullu6e duk wani farin cikin da yake ciki.
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....