P102

239 14 4
                                        

💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...102*

.......Wannan maganar ya matu'kar sosa zuciyar Anty Madeena da ma Rayyan kan sa, a wannan ga6ar Ammi ce ka'dai ta iya tankawa da" Ameen Ameen"..tana murmushin da iyakar sa kan fuskar ta ne kawai...domin a fili ta fahimci wani abu guda dangane da shi wanda aka 'kira da sunan wan mahaifin Zaitoonan.

Bayan tattaunawar su tayi nisa ya iso da niyyan duba jikin 'kanin nasa sai kuma ya tarar da su suna kan maganar.

Bata yi jayayya da su ba tace" bakomai..tana mai 'kara neman afuwar su kan shishshigin da suka yi na 'daurawa Zaitoon aure da ba tare da amincewar su ba..."!
Wannan karan Abban Zaitoon ne ya amsa da " ai bakomai...sune ya kamata ma suyi godia..domin yadda ce ta kawo hakan, da basu yadda da ita da tarbiyar ta ba ai bazasu fara ha'da ta aure da 'dan su na cikin su ba..dan haka su ya kamata su gode acewar sa, ai shi aure garkuwa ne, aure 'karin martaba ne da kariya ga duk wata 'diya mace...shi dai a 6angaren sa bai 'kalubalanci hakan ba..sbd tun farko ai laifin su ne, da basu 'ki 'diyar su suka kasa zama da ita ba ai da hakan bai faru ba...toh ina laifin wanda ya tallafi naka, ina laifin wanda ya 'kaunaci naka a lokacin da yafi bu'katan taimako....?"
Ammi tace " hakane...duk da hakan kuwa ya zam dole su gode su nemi afuwar su, dama kuma ba wai sun zo dan su tailasta bane, sun zo ne kawai dan nuna godiya gare su baki 'daya...tace tana fatan ha'duwar su ta kasance musu alkhairi a tsakanin su, alkhairi kuma mai 'dorewa har abada, idan kuma rabuwar kenan tana fatan zumunci ya 'karfafa tsakanin su kar a yada shi, tunda Allah ya riga ya ha'da.

Ta 'kara nuna yabawa da sosai ga Zaitoon acewar ta har abada bazata gaji da gode mata ba domin kuwa tattausan zuciyar ta yasa komai ya faru..taimakon da tayi musu kuma ire- iren taimako ne da bakowa ke jure yin irin sa ba shiyasa ta bawa Zaitoon lamban yabo, dole ta jinjina mata, tayi matukar nuna jajircewa da jarumtaka a matsayin ta na yarinya mai 'karancin shekaru...tace har abada bazasu iya mancewa da ko guda cikin abubuwan da tayi musu ba, shiyasa suke fatan su 'karasa rayuwar su tare da ita amma tunda su mahaifan nata basu amince ba shikenan...su zasu koma..Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gare su baki 'daya.

Yadda Rayyan ya 'kurawa Ammi idanu bisa wannan karkatacciyar maganar ta ta har sai ya baka daria..duba da yadda yy kicin kicin da fuska..amma ba kowa zai iya fahimtar yanayin da yake ba sai wanda ya san shi sosai, lkc guda kuma yaji yy nadamar biyo sun da yayi ma duba da yadda ko kadan Ammi bata damu da shi damuwar da zai iya shiga ba take wani magana, meyasa tun farko da ya ajiye su bai koma ba ne? yace da yasan wannan shirmen za'a yi wlh da bai biyo su ba...kawai ya barsu da Fawwaz.

'Kirr ya tsaida idanun sa akanta so ma yake su ha'de idanu amma Ammi ta'ki bashi wannan damar sam.

Cikin su babu wanda yace komai, Anty Madeena ma na son tace wani abu amma ta dake ta hana kanta tankawa.

Gefe guda wata uwar harara take bankawa Rayyan da zaka rasa gane ko ta mecece.

Zaitoon dai na nan zaune har a lkcn bata bar share hawaye ba...bata san takamammen yanayin da take ciki ba a halin yanzu illa bugun da take ji zuciyar ta nayi mata, bugu kuma da 'karfin gaske, bata kuma san dalilin hakan ba, ta dai san tana farin ciki, yau ga ta ga ahalin ta, ga ta ga mahaifi da mahaifiyar ta ga kuma 'yan uwan ta nan duk kewaye da ita amma ta rasa dalilin wannan damuwar da take ji ke sake taso mata sabuwa...da kyar ta samu ta lalu6o dalilin bai wuce na fargaban tafia da Mufeeda da take tunanin za'ayi ba ne ya sanya ta jin hakan.

Sai dai lkcn da aka tsaida magana akan su zasu wuce amma zasu bar mata Mufee na kwana biyu in yaso zuwa lokacin da za'a zo 'daukan ta idan sun yanke shawara to sai a san wani mataki ya dace a 'dauka in ma takardar sakin ne ko kuma cigaba da zaman su, za6in naga iyayen Zaitoona ne.

BINTEEE ( 'Yata ce)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang