💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...69*
........Yadda Ammi tayi kicin- kicin da fuska yasa babu wanda ya sake samun damar tada wancan maganar yayin da Anty Madeena tayi shiru dagangan ta dai fara shirin ta ta 'kasa- 'kasa ba tare da kowa ya fahimci manufar ta ba.
Da wayo sai da tayi abinda sauran masu aikin 6angaren nasa duk suka bari illa Zaitoon, batare da sun farga ba kuwa Anty Madeena tayi nasarar fara saka ta yi masa wasu hidindimu a 'dakin da yake kwance.
'Karshe tayi magana da maigidan ta ta kuma fahimtar da shi game da halin da ake kici ta kuma bashi dalilai kwarara ya kuma.gamsu dari bisa dari, domin dama asali Anty Madeena Zara take awajen sa sam bai ha'da ta da kowa ba, da kansa yazo ya samu Ammi as in shawara ya bata bakomai ba, nan fa kan Ammi ya 'kara 'daukan zafi, gefe guda kuma sai taga a hankali hidimar Rayyan 'din na komawa hannun ita Zaitoonan bata kuma san dalili ba.
Da dawowar Sultan bayan kwanaki biyar da tafiyar sa, Ammi ta zaunar da shi suka yi tattauna...shi kansa da farko yayi na'am da batun ko dan kar a dinga takura shi ma but jin wacce suke magana akai 'din yasa zuciyar Sultan luguden gudu, saurin canza baki yayi yace da Ammi sam Zaitoon bata dace ba, ama bar wani batun auren.gaba 'daya inda hali, taya ma za'a ce Zaitoon za'a aura masa alhali ba sanin asalin ta suka yi ba...cewar Sultan cike da bakin kishin dake ci masa zucia.
Ammi tace ni kaina ina kokonto duk da kuwa na yadda da tarbiyar yarinyar dari bisa dari, amma tsoron kowa ma nk ni a yanzu..bana so in 'debo mana abinda zai zo ya dame mu watarana...."
" Gaskia a dai dakata Ammi, inda hali ma a bar zancen gaba 'daya ni da zai fi, dama dai watace daban ba ita ba,.amma Zaitoon 'din nan sam hankali na bai 'dauke ta da auren 'dan uwa na ba...."Zancen Sultan 'din sai ya tsayewa Ammi a zucia, domin tun ganin yadda Zaitoon ke hidima da shi yasa ta fara sakkowa kan dokin na'kin da ta hau, amma batun Sultan ya sake rikita mata tunani ta yadda hatta su Raihana sai da suka fahimci canzawar yanayin ta karaf 'daya.
Ranar ko magana batayi sosai ba...hakika Rayyan na bukatar matallafi, in dai kuma ba san zuciya zasuyi ba bai kamata suce Zaitoon tana yi masa wasu abubuwa fannin kulawa da jikin sa zuwa wasu abubuwan hakan kawai sbd yana kwance ba, bacin sun san ba muharrami 'yk agareta ba, gefe guda kuma tunanin ta yadda Zaitoon zata kar6i zancen take sai kuma ga maganar Sultan da ya wargaza mata komai.
Ko da Raihana ta tambaye ta damuwar ta bata 6oye mata ba, nan dai Rainahan ta 'dan 'kara mata 'kwarin gwiwa daga baya takaiwa Anty Madeena Zancen suka sake tattaunawa, dan tuni raunin Ammi ya fito fili...dan haka dole ne suma su sake wani yunkuri.
Dama ita Anty Madeena can Sultan haushi yake bata, bayaga haka ma yazo ya gudu Lagos alhali yana ganin Rayyan kwance rai a hannun Allah duk da haka bai damu ba yayi tafiyar sa afterall ai yasan shike yi masa komai amma yayi tafiyar sa.
Saboda irin wa'dannan halayen nasa ya sanya tun farko baya birge ta...shine har zaizo ya wani sake zuge Ammi sbd munafunci...toh shi ina ruwan sa da koma menene hukuncin da suka yanke a junan sa ai bai sjafe shi ba.
A ganin Anty Madeena kenan.
Cikin ranta tace ai in kasan wata baka san wata ba.
Ta 'karashe da jinjina kai tana mai cizon la66a.Maigidan ta taje ta samu da batun shima yaje ya samu Alhaji Rufa'i da yake ma yanzu jikin nasa da sauki sosai anan suka shirya yadda abin zai kasance.
Anty Madeena da Raihana su biyu suka samu Zaitun har 'dakin ta suka zauna a'kasa tamkar basu ne sama da ita ta ta fannoni da dama na rayuwa da kuma shekaru ba.
Cike da laushin murya suke ro'kan ta akan ta amince da auren Rayyan ko dan kula da lafiyar sa ma, ta taimake su, ita ka'dai suke ganin dacewa tattare da ita kuma ita din ce suka fi jin yadda da amincewar su har can 'kasan zukatan su.

YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....