💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Salmerh MD*
_Wattpad@ Salmerh-md_
🅿️ *...18*
Dr Rasheed ya kasance likita ne a zahirin rayuwa da kuma fahimtar kowa ciki kuwa hadda mahaifan sa da sauran dangin sa, Dr Rasheed ya kasance shine yaro na farko kuma 'da namiji tilo wajen iyayen sa inda yaci sunan kakan sa wato mahaifin baban sa Abdulrasheed, dalili kenan da ya sanya mahaifiyar sa ke kiran sa da Abbah yayin da suke tsananin so da kaunar sa tamkar shi daya Allah ya basu, duk kuwa da kasancewar su masu karancin dukiya hkn bai sa sun gaza wajen samar masa ingantaccen ilimin zamani har ma da na addini ba hkn kuma ya cigaba da wakana har ga sauran kannan sa, sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun daidaita tarbiyar yaransu yadda ya kamata kuma Alhamdulillahi basu samu tsaiko game da hkn ba, sai dai wasu lokutan rubutacciyar kaddara ta kan yi tasiri ga rayuwar mutun ne sa6anin yadda ake zaton, duk kokarin ka baka isa gyarawa mutun zuciya ba sai abinda Allah mahaliccin sarki ya tsara kuma yaso gani game da bayin sa, san zuciya da kuma babban buri na son tara abun duniya su suka yi tasiri a zuciyar Rasheed hkn kuma ya sanya shi karkacewa daga tubar da iayen sa suk 'dora shi batare da sun sani ba, lokaci guda ya fada mummunar harka ta fashi da kuma garkuwa da yaran manyan mutane ana biyan sa makudan kudade.Yana da yaran da yk aiki da su guda biyar kacal wadanda su kadai ya aminta da su, kuma da su kadai yake aiki, su kadai ne suka san cewa yana wannan harkar a zahiri bayaga wasu manya da suka kasance masa jagora.
Rasheed yana da wani tanfatsetsen gida da ko mahifiyar sa sai da tayi mamaki lkcn da ya mallaki wannan gida duba da cewa aikin likitan ci kawai yk, kuma mahaifin sa me karamin karfi ne su kansu gidan da suke ciki shine ya canza musu kafin ma ya siya nasa na kansa, domin ada wani dan madaidaicin gida ne suke zaune kuma ya taso a cikin sa wanda yake mallakin mahaifin sa ne, daga baya ya canza musu muhalli wanda ya matukar basu mmk, da 'kyar ma mahaifin nasa ya amince ya koma gidan bawai dan yana zargin dan nasa ba a lkcn kawai dai acewar sa shi ya saka iyalin sa a ciki su inda suke ma Alhamdulillahi ya ishe su rayuwa, sai dai Rasheed sam yace a a daga karshe dai bayan an kai ruwa rana dole mahaifin nasa ya amince suka koma bayan Rasheed ya hada da wasu manya cikin ahalin su da kuma abokan mahaifin nasa.
Bayan komai ya daidaita ne sai yaje ga mahaifan nasa da batun kasuwanci da yake yi ta kasa da kasa na kayan masarufi ya kuma bayyana musu cewa ya dade da fara wannan harkar, ba laifi sun ji dadi sun kuma saka masa albarka.inda daga karshe sukai masa nasiha sosai akan kiyaye haram cikin lamuran sa.
Dr Rasheed yana da matar aure kwaya 'daya mai suna Hameedah yana kuma da yaran sa biyu mace da namiji...Wildan shine babba wanda ya kasance yaro 'dan shekara hudu da haihuwa sai kuma Naina wacce ba ta ajiye shekara biyu kwarara ba.
Ya kanyi duk wani 6oyayyun harkokin sa ne a gefe kuma babu wanda ya ankare da shi har a yanzu, hatta Hameeda bata san da wannan harkar ba.
Ko da ya kasance yana yawan fitan dare a gidan bata ta6a damuwa da hkn ko bin diddigi ba sbd tasan yanayin aikin sa ta kuma san hkn na iya faruwa duk da yk itama din ba wani karatu me zrfi ke gareta ba, a yanzun ne take makarantar kuma yajin aiki da jami'oin gwabnatin tarayya ke yi dole ya dakatar da ita, tsananin kaunar da take yi masa kuma ya sanya a mafi yawan lokuta Hameeda bata ganin laifin sa balle ta tahume shi ta kan yawaita yi masa uzuri.Dr Rasheed shine ya jagoranci harin da aka kai gidan Hajjaju a wancan lkcn, kuma bakin wani abokin aikin sa yaji komai akan Hajjajun, kuma kawai sunyi zancen ne as in hira dan yana yawaita ganin ta cikin asbitin kusan ma nanne kadai asbitin da tafi mu'amala da su, ya kan ganta amma be san wace ita ba sai lokacin da ta kai Zaitun sannan sai kuma yaga dacewar ziyartar gidan badan komai ba sai dan kawai ji da yy ance tana matukar murza Naira iya son ranta sbd da manyan alhazai take harkokin ta.
Sai akayi rashin sa'a kuma gidan ya fado cikin unguwar da yake 6oyayyar harkar sa shima dan hk suka shiga gidan nan ya tabbatar dagaske ne Hajjajun bata wasa ba ce, sun kar6i abinda ya kaisu karshe kuma da kansa ya kafa mata dokar tashi a unguwar bisa dole cikin wasu kididdigaggun kwanaki...ba dan komai yy hakan ba kuma kawai sbd shi ya tsani harka irin wannan, duk da yk shi laifi laifi ne, hk kuma zakunci zalunci ne ba'a raina shi amma ta wannan 6angaren kam ya kiyaye, duk abubuwan da yake aikatawa bai ta6a keta haddin kowacce mace ba, baya cin zarafin su bai kuma bari yaran sa ma sun aikata hkn ba.
Duk yaran nasa sun kasance fasihai ne ta 6angarori daban daban, kamar su sanin na'ura, sani da kutsawa cikin manya da sauran su.
Duk da hakan Dr Rasheed baya ta6a saka rayuwar su cikin hatsari komai ya kan yi kokarin cusa kansa ne da kansa ba tare da victims 'din sun san cewa shine da kansa zuciyar 'kungiyar ba, ya kance shine yy burin tara arziki dan hk dole shine da kansa zai farauci abinsa da kansa, ko kar6an kudin fansa mafiya yawa da kansa yk zuwa dan baya so ya saka rayuwar kowa cikin ha'dari sai dai bisa dole.
Lokacin da ya sace yarinyar Alhaji Modu asbitin su aka kai shi jinya sakamakon hawa da jinin sa yy, hawa mummuna, kuma shine likita me kula da shi, ta fannin aikin sa ya kan nuna tsatsan kula da tausayi.
Tsayuwa yy sosai kan Alh Modu duk da kuwa yasan shi din wanene ya kuma san menene ma'kasudin ciwon, amma hkn bai hana shi sakin rai yy aikin sa yadda ya kamata ba.
Haka ya dinga bashi treatment tsakanin sa Allah sai dai ya kan ce da iyalan sa ya kamata a daina daga masa hnkl haka nan, duk wani abu da suka san yana tada hnkln sa su sarara masa sbd kiyaye lafiyar sa, domin in jinin sa ya 'kara hawa makamancin hakan yana iya rasa lafiyar sa koma ransa gaba daya.
Matar sa da sauran yaran sa kam sai kuka...da kyar mahaifiyar ta iya bu'dan baki tace " Dr. wlh yarinyar mu ce ta 6ata yau kwana biyar kenan bamu san inda take ba"
Ido Rasheed ya zaro cike da tashin hnkl kamar gaske yace" Subhanallahi... har kwana biyar bb wani lbr kuma?"
"..mun barwa Allah dai mun kuma kai report ga hukuma amma har yanzu bb wani labarin komai..."
" Innalillahi....ya kai har karshe, wannan kam dole hnklin sa ya tashi Allah buwayi ya bayyana ta..".
Dr Rasheed baya wulakanci kuma ya tsani mutum mai wulaqanci..sannan yana tausayi da kuma kyautatawa.
Da rana idan ka ganshi a office zaka yi tunanin duk duniya bb wanda ya kaishi hankali da natsuwa amma idan kasan abinda yk aikatawa a 6oye zaka yi matukar mamaki.Ya kan yi anfani da beard, face mask ga glass, bakaken kaya, bakaken jackets da handglove sosai kamannin sa suke canzawa ko ka san shi da wuya ne ka iya gane shi cikin wannan shigar idan yayi.
Salmerh😘
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....