💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...93*
.......Bani da matsalar komai yanzu sai damuwar rashin makusanta na.
Kuma akai- akai Hamma ke kawo magunguna, madara da Glucose 'din yarinyar, ko baya gari kuma ba'a fasa kawowa domin ya riga yayi magana da Mai Chemist abokin sa.
Hatta kayan sallahn mu ni da Aishatu duk ya tanadar mana tuntuni.
Kewa guda ta ke damuna a hlin yanzu shine kewar gidan mahaifi na, su 'din dole na ne, bani da tamkar su, ko da su basu nemi inda nk ba tunda ni ina nan da lafia ta dole zan neme su.
Hakan yasa na yanke shawarar ziyartar gidan mahaifi na da wata safia sbd kawai in hadu da Abbahn mu yasa na fita da sassafe.
Da sallama ta na shiga..Iyami ce 'tsakar gidan " Wa alaik..."
Sai kuma tayi shiru ta ha'de rai ba'ki'kirin tana bina da wani mugun kallo." Lafia ..?"
Ta jefa min tambaya.
" Nazo gaishe ku ne Iyami"
Na bata amsa ina 'daga 'kafata zuwa ciki.
" Wa yace miki yana bukatan gaisuwar ki anan gidan...? Gayyar 'kasantar..gantalallu mabiya lunguna...?"Sam zagin Iyami na yau 'din bai shiga zucia ta balle ya dame ni, burina kawai in ida nufi na inyi gaba.
Kujera da na gani gefe nayi 'kokarin zaunawa ina mai bin cikin gidan namu da kallo yadda duk 'kazance...ko irin gyaran shirye- shiryen sallah da ake yi din nan banga alamun ana da niyyar yi cikin gidan ba.
" Iyami Abban mu na nan kuwa..?"
" Kin bada ajiyar sa ne..ko kuwa dan kin tmraina ni kk tambaya ta shi, ai naga alamun yanzu raini ke 'dawainiya dake tunda kin riga kinsan waye 'da namiji ba dole ki fitsare idanun ki ba..."Ban bi ta kan maganar tata ba kawai na mike na nfi inda tsintsiya yake na 'dauko domin tsaftace gidan kamar yadda na saba kafin barina gidan.
Da sauri Iyani ta hayyako min tana masifa ta kwace tsintsiyar ta.." ai da in bari ki share min ki zazzaga min burbudin karuwanci na kwammaci datti ya hadiye mu ni da yara na, maza kama hanya ki bar gidan nan, bukatar ganin ki ma babu mai yi balle marmarin aikin ki..."
Wannan hayagaga ta Iyami ita ta fito da Khausar da ke 'daki ita da Ummaru hk ma Abban mu.
A hnkli nace
" Haba Iyami...wai dan Allah mance matsayi na cikin gidan kk yi ne...ni 'din fa 'diyar ku ce kuma a tunani na ba'a ta6a canzawa tuwo suna..."
Da gudu naji an rungume min 'kafafu..ko da na kalla sai naga Ummaru ne..." Yaa Zaituna..."
Ya furta cike da farin cikin sa.
Ina kakalo murmushi na dube shi.
" Yah Zaituna Iyami tace wai bazaki sake dawowa ba sbd kin zama karuwa nayi ta neman ki banganki ba...ashe zaki dawo, Yah Zaituna kar ki koma kinji...?"
Kai na 'daga masa ina mai shafa kansa daidai lkcn da wani zazzafan hawaye ya sakko min.Sam ba aimin adalci ba, kokadan ba'a kyauta min ba a gidan nan..indai har za'a zauna a tsarawa yaro 'karami irin Umar wannan maganar toh me ne kuma za'a aikata da zan bani mmk.
Iyami na kalla sai ta kya6e baki ta kawar da kanta...bani da wata kalma da zan fadiwa Ummaru domin wanke kaina amma nasan watan wataran zai fahimta.
Khausar na duba ta banko min wata uwar harara dai dai lkcn da sautin muryar Abban mu ta doki kunnuwa na.
" Sakar min yaro da Allah...me ma ya kawo gidan nan...?"
" Abbah"
Na furta ina zubewa bisa gwiwoyina na rushe da kuka.
" Abban mu nice fa Zaituna...!"
" Sai akayi yaya...bani da wata ala'ka da mutun irin ki balle mai irin sunan ki, na riga na cire ki cikin yaran gidan nan tun daga ranar da kk kwasowa kanki abin kunya, kuma daga yau 'din nan ko a hanya kk ha'du da jinina kk yadda magana ta hada ku wlh ban yafe mk ba, kije can da 'diyar ki..kije ta zame mk dangi amma ba ahali na ba...kin zame mana abin kyamata domin haihuwar irin ku bata da wani riba..."
" _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...haba Abbah! Dan Allah ka sassauta min Abban mu, wlh bani da alaka da yarinyar nan indai kuma akan ta ne kk kokarin cire ni daga cikin yaranka Abbah na hakura da yarinyar a mayar da ita gidan marayun na amince amma Abbah kar kai min mugun baki akanta, wlh bani ce na haife ta ba kaddara ce kawai ta hada mu..Abba tausayin ta nk ji sosai agabana aka harbi mahaifiyar ta..._!..

YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....