💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...75*
.......Baya ya koma ya kwantar da bayan sa jikin gado yana sake zurfafa tunani, shaf sai ya mance da cewar 6oye kansa yake, ya kuma manta cewar da Ammi ta fita bai kuma rufe 'kofar ba, bazata kawai yaji an turo 'kofar gami da sallama ciki- ciki.
Da sauri ya 'dago kansa gami da bu'de idanun, duk da yake tun kafin ya 'dago idanun ya fahimci wanene, dirowar bazata da yai masan shiyasa shi 'dagowa a gaggauce, nan kuwa idanun sa sukayi arba da babban aboki kuma aminin sa wato Dr Fawwaz, 'dan 6ata rai yayi yana komawa dan daidaita kwanciyar sa.
Yayin da Dr Fawwaz ya waro idanu sosai yana kallon sa gami da nuna shi da 'dan yatsa ya ma rasa kalmar da zai furta.
Da 'kyar bakin sa ya iya tattaro abin fadi har ya furta sunan" Rayyan".
" What..?
Ya tambaya a dake batare da ya dube shi ba.
" ....Wai kaine nake gani ahaka ko kuwa idanu na ke min 'karya....?"
'Karamin tsaki Rayyan yaja na neman magana ya kuma watsa masa harara yana mai juya mai baya yace..." A a ka manta...kanka kake gani haka ba Rayyan ba....!"
" Yah Subhanallah..."
Fawwaz yace out of excitement...ai da gudu ya tafi gare shi ya rungume shi sosai yana sakin hamdala gami da daria bayyananniya....Ture shi Rayyan ya fara da hannun sa 'daya mai lafiyar yana fa'din" Kai...kai..wai miye haka ne, 'karasar dani kake so kayi kome...?"
Fawwaz ko ta kansa bai bi ba balle ya ya fahimci abinda yk nufi, farin cikin da ke cin sa ya rinjaye komai a lkcm.Sai da ya gama bayyana farin cikin sa gami da godiyar sa ga ubangiji kafin ya fara zolayar Rayyan wai shegen kaya wannan irin nisan tafiyar da kayi duk kabi ka sa hankulan mu sun tashi fa, gaskia ka shirya sai mun ci tarar ka"
" Wani karon in zan tafi ai tare zamu kwantar da hankalin ka...!"
Hannaye Fawwaz ya 'daga da sauri yana fa'din " A a...a a bawan Allah rufa min asiri ban gama ha'de guzuri na ba tukunna...".
" Matsorracin banza..."
Cewar Rayyan...yana 'yar daria,
Fawwaz yace" naji dai...ai da gaskia ta,...Ya jikin naka toh, yau dai an hutar da bayin Allah daga damuwar zucia da ta zahiri..."'Ko'karin zama Rayyan ya yayi yana bawa Fawwaz umarnin rufo 'kofa da hannun sa yk fa'din" Ni kuma sai da na 'kwammaci ban ma tashin ba sbd damuwar da na tarar...".
" Damuwa kuma...kamar wace iri..."
Cewar Fawwaz da ke dawowa daga rufe kofar idanun sa akan Rayyan." Kassarani da kuke son yi mana..dan na san komai gudunmawar ka ya faru...".
'Yar daria Faweaz yayi gano abinda yake nufi yana zama gefen sa yace" Kanka ake ji kuma yanzu..".Nan Rayyan yai masa takaitaccen bayani akan yadda yake jin hannun nasa.
Atare suka yi aikin duba hannun atare da taimakon junan su, nan kuwa gano inda matsalar take sun kuma fahimci mafita 'daya gare su in dai ana so hannun ya dawo daidai kamar da toh sai an sake yi masa aikin gyara karayar dake a hannun.
Rayyan yace sam shi dai ba yanzu ba tukunna, ya kuma ro'ki Fawwaz akan dan Allah ko Ammi ta bu'kaci su koma asbiti yasan 'karyar da zai mata ya waske, yasan da zarar anje asbiti sai an ri'ke shi shi kuma bai son zaman can dai- dai da ta yini guda ne wai da sunan jinya.Sun sha hira sosai da Fawwaz kafin suka rabu kowa zuciyar sa na masa da'di da ganin 'dan uwan sa..a bakin Fawwaz ma yaji wasu abubuwan da shi bai san da zaman su ba, kamar tsawon lkcn zaman da yayi a kwance, yanayin jinyar sa, auren su da aka 'daura da Zaitoon a masallacin Uthman bn Affan da ke nan cikin unguwar ta su da irin hidimar da ta yi ta faman yi masa..da dai sauran abubuwa.
Sosai ya sake tsunduma cikin yanayin zurfafa tunani.
Ko yaso hana kansa tunani abin gagarar sa yake, a yanzu babban damuwar sa 'diyar sa ne, yadda zai bayyana wanzuwar ta ga kowa shine damuwar sa, ko ciwon hannun sa bai dame sa kamar yadda lamarin Mufeeda ke damun sa ba...burin sa a kullum shine yaga ya 'yantar da 'diyar sa ta dawo 'diyar sa a zahiri, ta kuma rayu tamkar ko wani 'da a gidan mahaifin sa, yana so ya gatanta ta ya 'daga darajar ta fin wanda akayi mata abaya.
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....