P29

72 8 5
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...29*

           .........Cak ya tsaya yana jin zuciyar sa na harbawa da kai kawo jin yadda mahaifin nasa ya kira sunan sa abinda bai taba ji ba.
" Kar ka manta da cikakken sunan ka da kuma waye mahaifin ka a duniyar nan..."

"...Tun ina yaro ma ban ta6a mantawa ba balle yanzu.."
..." Well..kaje kayi sana'ar da duk kake ganin tayi maka bazan hana ka ba, amma ina sake jaddada maka cewa kai 'din jinin 'Dan Maliki ne kuma wani 6angare na rayuwar sa kar ka ta6a mancewa da wannan, ka kuma kula...".

Adam bai ce da shi komai ba  kawai ya fice daga palorn bayan ya juyo ya dube shi sau 'daya, da ace yana cikin mood mai kyau babu abinda zai hana shi murmushi da jin kalaman 'Dan Maliki amma baya cikin wannan yanayin a wannan lokaci, hanyar da yasan zata fitar da shi daga gidan ma gaba 'daya ya tunkara yana jinsa wani sakayau babu nauyi.

A bakin gate ya tarar da Hafeez tare da gate man yayin da sauran securities 'din Alhajin ke gefe suna sha'anin su.
Bai ce da Hafeez komai ba shima da ganin sa kawai ya taso suka fice yana wa gate man 'din sallama..daga haka suka bar gidan ma gaba 'daya inda suka bar 'Dan Maliki cike da zullumi da nadama matsananciya, sosai jikin sa yayi sanyi, raunin da bai ta6a fuskanta bace ta ke shigan sa a wannan lokaci, ji yake tamkar ya sulale ya 'dora hannu aka yayi ta ihun ta6argazar da yayi ta aikatawa, abu 'daya da a kullun yake gode Allah akai shine da bai tsaya duban halayyar sa ba ya bashi yaro nagartacce mai zuciya irin Adam.
Babu ta yadda halayyar su tayi kama, shi'din tamkar kishiyar halayyar sa ya kwaso, babban abinda ya birge shi ga Adam 'din shine yadda koka'dan dukiyar sa basu dameshi ba, burin sa kawai ya tara nashi da gumin sa.

Daga gidan Maliki basu zame ko'ina ba sai gidan su Adam Shaheed nan ma direct 6angaren sa.
Hafeez ne yasa hannu ya bu'de 'dakin da suka shiga kuma ya maida ya rufe harda saka makulli.

Adam kam kan kujera ya zauna yana dafe goshin sa, kadan kadan yake jin kwanciyar hankali na shigan sa, sai dai yasan mawuyaci ne ya samu kwanciyar hankalin gaba 'daya, wancan abin da ya gani ya kuma yi kokarin dannewa can kasan zuciyar sa bazai ta6a barin sa ya samu cikakken farin ciki ba.
" Meyasa ne?
" Why Alhaji?
" Da wannan shekarun?
" Kuma yaran cikin ka..?
Hafeez ne da ya taho kanshi ya tsaya ya dakatar masa da tunanin da fadin..." kasan me nake ji kuwa...?"
Dago idanu yayi gami da bude su akan Hafeez 'din tare da lumshewa ya kuma budewa nan take alamun ina jin ka.
Hafeez da ya san ma'anar hakan sai cigaba yayi da fa'din..." Ji nake tamkar in ta dukan ka har sai ka suma"!
Hafeez ya furta cike da jin haushi.
Waro idanun yayi kan fuskar Hafeez da alamun tambaya amma bakin sa ya gaza furta wata kalma.
"...ka bani haushi sosai, meyasa ka kasa tauna kalaman ka, ka kasa sassauta furuci da sautin muryar ka gare shi? Meyasa zaka sashi agaba kana furta duk abinda yazo bakin ka? Kaman ta mahaifi yake agare ka ne, ka manta cewar shine aljannar ka.."
Ran Hafeez dagaske ya 6aci sosai da yatsa ya nuna Adam sannan ya cigaba da fadin" bari in fada maka wani abu Adam wallahi duk lalacewar masa tafi kashin shanu daraja, duk tsiya mahaifin ka ne, duk lalacewa da mugun halin sa mahaifi yake a wajen ka, nasan kuma kasan girma da darajar da iyaye suke da shi a wajen mu iyaye iyaye ne hara abada ba'a ta6a canzawa tuwo suna, kayi maza ka nemi yafiyan sa kafin lokaci ya kure maka ina fada maka".
Ya karasar da daga murya.

Adam Maida idanun sa yayi ya rufe sannan ya bude su kan fuskar Hafeez ganin yadda ya dauki zafi ne ya sashi bu'dan baki da 'kyar ya fara magana..." wai duk wannan zafin ran akan maganar nan ne?
Hafeez harara ya banka masa batare da ya furta komai ba.
murmushin gefen baki Adam yayi sannan cikin sigar lallashi yace" ka kwantar hankalin ka zanyi duk abinda kace amma ba yanzu ba, for now ka barshi nasan ban kyauta ba amma dole tasa nayi hakan, ya rayu ne kaf din rayuwar sa babu mai fada masa gaskia a yanzu kuma da nake da damar hakan bai kamata in yi wasa da wannan damar ba..."
Shiru yayi na dan wani lokaci yana jin tukuki cikin ransa amma ya zai yi ya zam masa dole ne ya nema masa rufin asiri.
Sai da ya kawar da kai gefe tamkar bazai yi magana ba sannan a hankali cike da rauni ya 'kira sunan Hafeez.
Duban sa yayi gami da sauraron abinda yake son fada masa.
" Hafeez nasan kai amini kake a wajena dan tabbas ka wuce aboki musamman a yanzu da muka yi tarayya wajen ganin abu guda, Hafeez ina rokon dan Allah abinda muka gani gidan Alhaji..."
Bai ma jira ya karasa ba ya tare shi da fadin" kar ka damu kasa a ranka tamkar  batare da ni kaje gidan ba, I promise u...u won't regrets trusting me..".

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now