💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...106*
........Haka nan kawai ta kwashe da daria batare da ta amsa tambayar sa ba....'kit ya kashe wayar yana fa'din in kin gama dariyar mayi magana.
Sosai ya bawa Zaitoon dariya, shi yana can yana mitar da jin haushin yadda ta tuhume sa kan Marwa ita kuwa duk lkcn da ta tuno sa da yadda ya dan shiga rudu sai kawai tayi murmushi.
Can 'kasan ranta take jin wani farin ciki, tsananin farin ciki ne marar misaltuwa.
Adam kuwa sam bai ma saka maganar cikin kansa ba balle ta dame sa...sai zuwa dare da ta ga bai sake 'kiranta ba sannan ta 'kira shi.
Yana 'dagawa tace
" Yah Adam ba dai fushi akayi da 'kanwa ba...?"
" Fiye da fushin ma in anayi dole zanyi ai don 'kanwar ta 6ata raina..".
" Kai Yayah!".
" Yes mana..kawai ki wani mai da ni abin wasan ki..".
Idanu ta zaro tana dan toshe baki.
" Yayah ba haka bane fa...kawai ina jin farin ciki ne sosai, kasan in akaji cewa an samu cigaba dadi akeji...".
Cike da mamaki yace
" Farin ciki?..Jin 'dadi?..duk na mene?"
Adam tunanin sa zata ce sbd kiran da yai mata ne.
Sai kuma yaji sa6anin haka.
Tace
" Ina mk murna...indai marwa ce inayi mk albishir 'din babu kai bb samun matsala in ba wata kaddarar ba..babu kai babu korafu da iznin Allahu...kuma baka da matsala tsab zan bk ita insha Allah.."
Ta karashe tana yar daria.
Gishi ya dafe.
Sai yanzu ya gama fahimtar kaf inda ta dosa.
" Yah Subhanallahi.."
Ya furta a fili.
" Zaitoon ba dai ni yarinyar nan kika raina har haka ba...wai me kike nufi ne?
Wani darian ta kuma tana mai yanke wayar.
" Indai tayi tsami maji komai Yayah".
Ta Fa'di hakan ne a fili still with a bright smile on her face.
Shi Kansa Shaheed murmushin yayi bayan tunanin Yan dakikan lkc da yayi kasake da wayar a hannun sa.
" Zaitoon kenan" ya fa'da Yana ajiye wayar.
Lokaci lokaci Kuma sai maganan Zaitoon ke zuwan masa rai hakan nan kawai bai san dalili ba.
Har aka kwana biyu kwata- kwata bai ji zuciyar sa cikin salama ba.
Throghout those days abu guda ke masa yawo a zuci.
Kawai sai yanke shawarar sake Kiran Zaitoon.
Koda ya dago wayar Kuma na take batare da ya san dalili ba haka nan kawai akalar yin 'Kiran ya canza daga Zaitoon zuwa Marwa.
Bai tashi sanin yayi 'kundumbala ba sai da yaji wayar ta fara ringing.
Sai Kuma ya fara tunanin me zai ce da ita toh.
Firgigi yayi lkcn da ya tsinkayi sassanyan muryar ta da akoda yaushe yake Jin ta cikin sanyi tayi Masa sallama.
Bai amsa ba sayMi a karo na biyu kafin ya amsa ta. shima wata kamilalliyar muryar da shi kansa bai san yana da ita ba bai ma san yaushe yayi hakan ba sam.
Sun gaisa kamar yadda suka saba, sama sama, sai yace Mufeeda fa..?
'Dan jim tayi sannan ta amsa shi" ai bata nan, ba a kawo ta ba".
" Ohh tana ina ne har haka?
" Wajen Anty."
" Zaitoon...?".
" No.. Antyn mu fa.."
" Ok.. Ina so inji muryar ta ne ya za a'yi kenan yanzu..?"
Yatsine fuska tayi sosai cikin ranta take ayyana" ji wani kalan dangi anan".
Ina dai 'diyar tamu ce bata kowaba.
Tana cikin tunanin taji ya sake fa'din " yaushe za'a ha'dani da ita?"
" Babu rana gaskia dan basan actual ranar da zasu zo ba".
" Common please...ki yi tunanin wata hanyar mana, dagaske i really missed my daughter".
"...toh fa, ai kuwa sai dai in sun zo...".
" adai duba...baza a min alfarma ayau a ha'da mu ba...?"
Baki ta tura sosai.
" Mufeedan fa ba ma magana ta iya sosai ba..."
" Nasani...ni dai please ki ha'da ni da ita ayau...ina jiran 'kiran ki..kinji".
Bata amsa masa ba daga inda take sai ma 'karawa bakin ta tsayi da tayi...shima jin shiru ya sashi cire wayar daga kunnen sa sannan ya kashe ta...fuskar sa yalwace da murmushi.
ESTÁS LEYENDO
BINTEEE ( 'Yata ce)
Ficción GeneralSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....
