💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*Wattpad@
Serlmerh-md🅿️ *...35*
........." Ba wannan nake son ji ba Malam...kana nufin Alhaji bai sanar da kai komai ba? bai ambaci suna na ko sau 'daya cikin maganar sa ba...?".
Cewar Hafeez cike da nuna rashin jin dadin sa a fili.
Adam na dariyar shakiyan ci yace" Ji wani zance kai kuma, meyasa zai ambace ka bayan gani kuma gaban sa....?"Wannan karon cike da jin haushi Hafeez ya kai masa naushi ya goce yana dariya sosai.
" Ka dallah malam sakar min mara...ba dai so kake kaji ba? Toh ya sanar da ni ya baka ajiyar kundin tarihin ahalin sa...kaga nima zan samu dangi nan kusa".
Murmushi Hafeez yayi yana hararan sa yace.." Shine sai ka wahal da ni..?"
Ba 'karamin dadi Hafeez yayi da wannan annuri da farin cikin da ga abokin sa a ciki...fuskar sa cike da fara'a yace" Toh bayan haka fa...?"" Babu komai"
Inji Adam yana tafiya Hafeez ma kokarin jerawa da shi ya sake fadin" Ka tuna dai...".
" Ka manta asali ni ba gwanin mantuwa bane...?""Ai shikenan, amma dai ba kundin tarihi ka'dai Alhaji ya bani ajiya ba, har da kundin tattalin arzikin sa gaba 'daya ma'ana dukiyar sa wacce ya mika ta kacokam ga 'dan sa 'kwaya 'daya tilo wato _Adam Shaheed Jibrin 'Dan Maliki.._ ."
" Wasa kake ".
Adam ya fadi cike da nuna rashin kulawa ga maganar.Ganin hakan yasa Hafeez fizgo hannun sa cike da kufula yace" meyasa kake maida komai wasa ne Adam? wannan batun fa ba na 'kananun ku'di nake maka magana ba, ina maka magana ne akan 'dimbin dukiyar mahaifin ka da ya tara ya kuma mallaka ta gareka...".
Ganin kamar Hafeez 'din dagaske yake ya sa Adam 'dan 6ata rai yana dakatawa da tafiyar ya fuskanci Hafeez 'din da kyau.
" Kafi kowa sanin bana bukata meyasa ka kar6i ajiyar sa..? ka maida masa abinsa".
Ya bashi amsa da iya gaskiyar sa sannan ya cigaba da takawa, wannan karam da 'dan saurin sa.
Cike da jin haushi Hafeez ya fara fa'din" Ba za'a maida ba Adam, bazan maida masa komai ba, wai anya kana cikin hankalin ka kuwa..?"
" Kafi.kowa sanin matakin da hankali na yake ba sai na maimaita ba maka ba, kamar yadda kafi kowa sanin ba dukiyar sa ta kawo ni gareshi ba?"
" Shi kansa ma yasan wannan ba ma ni ba, amma duk da hakan bai sa ya kasa mallaka maka ba...".
Fuska Adam ya had'e sosai ya wani 'kankance idanu yana duban Hafeez yace" wai dagaske kake ne...?"
Kai Hafeez ya jinjina masa alamun tabbatar wa.
" Ka mayar masa dukiyar sa Hafeez kwandalar sa bana bukata, ka manta ire- iren hanyoyin da yabi wajen tara dukiyar ne...?"" ban manta ba, amma ai da ka nutsu ka saurare ni bazaka furta hakan ba..."
" Ni dai dan girman Allah Hafeez ka maida masa kayan sa, burina a duniyar in samu yardar Allah mahalicci na na rabu da duniyar lafiya, na kuma san hakan bazai ta6a yiyuwa ba har sai na bi mahaifana, bana da mahaifiya sai mahaifi, na kuma yi kokarin wajen ganin na gyara mu'amala ta da shi ko a yanzu na mutu bazan ji bakin ciki ba, domin nasan tsakani na da Abbah na babu wata matsala...ban ta6a kwa'dayin dukiyar sa ba tun abaya ma, so mai yasa zanyi kwadayin rike ta a yanzu....wlh Hafeez bana bukatar komai daga cikin dukiyar sa, ka maida masa abinsa ba mamaki lokacin da Allah yayi fitowar sa suyi masa amfani..."." Ta ya zan mayar bayan ba hannu na suke ba...?"
" Toh mecece damuwar ka kuma..tun da ba hannun ka suke ba? ka 'kyale ni da maganar hakan nan dan Allah Hafeez, ka mance kawai.."
" Tamkar amana ya bani Adam, sannan ni Alhaji ya wakilta matsayin jagoran da zan isar da ita gare ka saboda yadda dani da yayi da kuma sanin kusancin da ke tsakani na da kai amma komai na wajen Lauyan sa....nan ya zayyane wa Adam duk yadda suka yi da 'Dan Maliki, yadda ya kasafta dukiyar sa kashi kusan biyar, kaso hudu duk ya mallakawa gidajen marayu da sunan Adam kaso guda kacal ya rage yace na Adam 'din ne, ya kuma tabbatar musu da cewar babu haramun cikin wannan kaso gudan dai- dai da 'kwayar zarra.
" Duk da yake munanan harkoki masu yawa Alhaji ke yi amma bai yadda ya sirka dukiyar sa da ta haramun din ba, kowacce da ma'ajiyar ta ka yadda da ni Adam..".
Hafeez ya karasar da taushin murya.
" Toh me ze hana duk a ha'da akai gidan marayun...?"
Adam ya tambayi Hafeez da iya gaskiyar sa.
" Baza'a kai ba Adam, wannan mallakin ka ne, ka daina yankewa mutum hukunci bisa halayyar sa ta baya domin lokaci yana koyar da su darasi kuma ya kan canza su, ina tabbatar maka da cewa matukar ka sake bijire wa wannan lamarin zaka zo kayi dana sani watarana, dana sani ma marar amfani".
Cike da jin haushi Adam yace..." Fata kake min ko me ne hakan Hafeez?".
Hannaye ya 'daga sama" ohh no..gaskiya kawai na fa'da maka...".
Tafiya suka cigaba da yi babu wanda ya sake furta wani abu.
Hafeez 'kasa- 'kasa yace" mutum sai shegen taurin kan tsiya ana baka kana 'kin kar6a".
Abinda kawai ya bawa Hafeez mamaki shine yadda kaso guda cikin dukiyar Alhajin yaso bashi tsoro dukiya ce bata wasa ba da ya tabbatar matu'kar abokin sa ya mallaka ya gama da babin talauci a rayuwar sa, duk wani fadi tashin neman sa sun 'kare hatta jikokin sa sai sun an tara musu, dan shi kansa Alhaji Jibrin sai da ya bashi kyautar 1ml matsayin nasa tukuicin na zama da 'dan sa da yayi da zuciya 'daya, ya bawa Lauyan sa ma tasa kyautar haka ma Hajia Talatu.
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....