P24

80 12 12
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...24*

             .......Kafa'dar ta taji an dafe daga bayan ta tayi saurin 'daga kai sbd tsoro, nan tai arba da Mufeeda, Mufeedan ta rike a hannun wata babbar mace da bata san ko wace ita ba, murmushi take yi da ganin yarinyar amma idanun ta na zubda 'kwalla, yau ga ta ga Mufeeda suna yiwa juna kallon kallo, bayan tsawon wasu kwanaki wadanda suka kasnce mafi tsananin muni daga cikin rayuwar ta.

Hannu Mufeeda ta mika mata tamkar wacce ta tuno wani abin tana fa'din"..Mammi...".
Da sauri Zaitun ta 'dago nata hannayen ta amshi yarinyar da duka ta taho gare ta tana washe mata baki.

Ita canzawar yarinyar ne ma ya bata mamaki sosai, kokadan bata ga abin da zata ce bai yi ba game da yarinyar.
Garin kar6ar Mufeeda ne idanun ta suka yi arba da Zabba'u da Zaleeha tsaye abayan matar, Zaitun sai ta dan kalle su sannan ta dubi matar.

Dukkan su kuka suke yi kuma tasan kukan bana komai bane face na tausayin 'dan uwan su, aikin shai'dan kenan da kuma sharrin biyewa son zuciya, baya ga haka ga shi da yan uwa masu tsananin kaunar sa, ga mahaifiyar sa mace nagartacciya ga innocent yaran sa masu so da kaunar sa amma ya lalata musu sunan ahali...ya barwa yaran sa tabon da har su mutu bazai goge a garesu ba.

_Yah Ubangiji Allah ka raba mu da son zuciya...kasa mufi karfin zuciyar mu cikin dukkan wani tsanani na rayuwa._

Mahaifiyar Rasheed ta nemi su koma gidan su da Zaitun amma taki amincewa, dan ita yanzu ba wannan bane burin ta, taya ma za ai ta iya ra6ar wani daga cikin ahalin Rasheed, sosai ta yadda da kaddara amma bazata sake kuskuren jefa kanta cikin wata damuwar ba, bazata yadda ta bada gudummawar faruwan kuskure makamancin wanda ta tsallake da 'kyar ba.

Dan hk sai tabawa Hajiyar Rasheed ha'kuri, ta bawa su Zabba'u ma ha'kuri dan tasan sune zasu sa Hajiyan cewa ta roke ta, tana san suna kaunar ta amma bazata iya sake rayuwa tare da duk wani abu daya dangance su ba, bazata iya bin su ba.

Sun so takura mata amma mahaifiyar su ta dakatar da su, acewar ta su barta ba dadi tun bata ra'ayi ba dole bane sai ta zauna da su, ita aganin ta Zaitun din ma tayi tunani, domin zama tare da sun din bazai bar abin ya 6ace mata a zuciya cikin sau'ki ba, gara tayi nesa da su.
Ita Zaitun din ma akaran kanta yanzu bata bu'katar taimakon kowa bata so ta sake ra6ar jikin kowa bata bukatar tallafin kowa cikin rayuwar ta, in kuwa ya kasance dole ne toh gara cikin biyu tayi abu da'ya....

Daga 'karshe kayan ta dake leda tun wanda ranar ta fito da su su ta gani sun mi'ka mata ba da son ran su ba, sosai tayi farin ciki da ganin kayan bayan duk gwagwarmayar da ta sha ashe kayan ta nan nan...daga haka sukai mata sallama suka yi gaba tana kuka suna kuka, kowa abinda ke zuciyar sa daban.

Mufeeda dake hannun ta ta sake rungumewa tamkar wacce za'a 'kwace mata ita,  dagaske tana jin kanta wata iri ne yanzu, tana jin kamar she is no more that Zaitun da ta sha gwagwarmaya abaya, dole ta canza musu salon rayuwa dole ne ta za6i abu guda cikin rayuwar ta, a yanzu tana jin zata iya fuskantar koma menene ya tunkaro ta, tana jin cikin ranta tamkar bata shakkar kowa..dan haka dole tabi za6in da zuciyar ta tai mata game da rayiwar su.

Jin kamar tsayuwar na neman garar ta ne yasa ta koma ta zauna tana maida numfashi, tana tuno lkcn da irin wannan abin ya fara riskar ta tun bayan da aka kulle su bata iya doguwar tsayuwa sai ta fara jin jiri bata kuma san dalili ba.

Ta kai tsawon mintina biyar a zaunen banda aikin kuka rungume da Mufeedan babu abinda yake yi, tun bayan tafiyar su Zabba'u bata sake 'dago kanta ba, wanda tana yin kukan cike da tausayin kansu, gida take son komawa, amma bata da ko sisi da zata iya 'daukar nauyin su da shi, bata da ko sisin da zata dauki 'dawainiyar su da shi ko da ta koma gidan, toh kuma idan taje gidan wajen wa ma zata nufa?, wajen Yah Bukar..kai ina tsinuwar Iyami fa da ta riga ta anbata...?
Gaban mahaifiyar ta...?...toh auren ta fa?, bata so tayi sanadin kashewa mahaifiyar ta aure..daga karshe dole dai ta sake yanke wata shawara ta daban.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now