💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...65*
........Shi da Huzaifa suka zauna agaba, motar shiru babu wanda ke motsin kirki balle doguwar magana, shi dama Huzaifa ba hira suke yi da Rayyan ba yayin da Amrah ke nan tana zullumin abinda ya samu Rayyan da duk zaton ta baya jin dadin jikin sa ne, tuni ma ta mance da batun 'danta ganin an 'dauki tsawon kwanakin nan babu wanda ya tanka akai sai ma wasa da aka maida lamarin ana tsokanar sa mai kama da kanin Daddyn sa.
A tunanin ta a haka zancen zai wuce batare da kowa ya zarge ta ko Sultan ba.Rayyan kam gaba 'daya duniyar ce ma yake jin take juya masa, motsin kirki baya 'kaunar yi sam...bai tashi sanin sun iso gida bama sai da yaji karar horn sannan ya dan bude idanu.
Suna isa wajen parking Sultan kuma na fitowa daga sashen Ammi shima ya nufo wajen parking din dan motar sa na wajen.
Da alamu ya zo gaisar da Ammi ne.Tun tsayuwar su da Rayyan ya bu'de idanu akan Sultan suka fara sauka, take jiyoyin kansa suka motsa, suka 'kara 'karfi, idanun sa suka 'kara rinewa sosai, bai san mai ya sa ya kasa dauke idanu akan sa ba, be san meyasa yk jin yayi tackallon Sultan din ba, sa6anin Amrah da ko ji da ganin ta baya 'kaunar yi kwata kwata, sai dai can 'kasan ransa yake ji tamkar zai iya ganin wani abu da zai iya 'karyata duk wancan bayanan da ke cinsa a zuci...amma ko alamar hakan bai fara gani ba balle ya saka rai da gani, sai ma 'kara dulmiyar dashi suke da dawo masa da wasu abubuwa da abaya tunanin sa bai ta6a basa hakan ba.
.....Kallon Sultan yake yana kissima abubuwa, tamkar tashin tsuntsaye haka abubuwa ke shawagi game da Sultan a kwanyar sa...mamaki, al'ajab, rashin yadda, tsana, da wasy abubuwan da bama zai iya lissafawa ba, ha'ki'ka in Allah ya baka zucia mai kyau toh tabbas ka du'kufa wajen gode masa dan yayi maka kyauta, kyauta mafi inganci da alfahari...me ya yiwa Sultan har haka? Me yasa Sultan zai ci masa amana, cin amana mafi muni irin wannan...baya so ya zafafa abinda yake ji kamar yadda baya so ya gina wani shinge tsakanin sa da Sultan shingen da ya tabbatar dukkan su bazasu ji dadin sa ba, har gobe yana 'kaunar sa domin ba'a koya musu ki ko nuna bambanci tsakanin su da shi ba, 'kaunar juna da mutuntawa aka koya musu shiyasa yake 'ko'karin danne ransa yake danne abubuwan da ke taso masa baya so su fashe, baya ga haka idan ya biyewa umarnin zuciyar sa hukuncin da zai yi musu bazai yi musu da'di dukkan su ba.
Amrah ce ta fara fitowa a motar sai kuwa Sultan da ya riga ya kusa isowa kusa da su ya washe ha'kora.
Huzaifa na hanzarin fita dan zuwa bu'de masa motar Rayyan ya dakatar da shi.
Sultan kuwa wajen su ya nufa yana fa'din.." Maman Boy daga ina haka...?, Hope lafiya dai kam...?"
Yayi maganar yana bu'de fuskan yaron dake hannun Amrah at same time yana kashe mata ido 'daya sai ta saki murmushi tana bin hannun sa da kallo, duk suka sauke idanun su kan fuskar Arfan atare.Duk faruwan hakan akan idanun Rayyan ne, zuwa yanzun sun daina ma bashi mamaki, sai dai baya jin duk cikin su akwai 'daya da zai iya nasarar illata masa zuciya sun yi kadan, bazai zauna abanza su nakaskta masa kwarin zuciyar sa ba.
A hankali Amrah batare da ta dube shi ba tace" Tare muke da Baby fa..".
" Wani Babyn..?"
Ya tambaya yana 'dage gira.
" Sorry...I mean Rayyan...".
Ido ya 'dan fitar" Ohh...shine baki bani signal da wuri in je in kwashi gaisuwa ba..?"
Ya 'karashe maganar da kar6an Arfan dake hannun ta ya nufi motar da Rayyan ke ciki, dai- dai shima ya sa hannu ya bu'de motar caraf idanun su suka sau'ka kan cikin na juna, kowa kallon da yayiwa 'dan uwan sa cikin zuciya daban yake.
Yayin da fuskar kowa ke 'kokarin lullu6e wani abu da shi 'kadai yasan ma'anar ta." Yah..Barka da war haka..."
Kallon sa kawai Rayyan yake bakin sa ya ma kasa motsi balle ya amsashi, ji yake tamkar ya sha'ke shi amma har yanzu bashi da ikon yin hukunci bisa ga abinda bayi da hujja 'kwa'k'kwara ta zahiri a hannun sa da kai tsaye zai ce Sultan na fita da matar sa, zargi ne kawai, zargin ma da bai kai yayi tuhuma akansa ba tukunna, he still need more evidences.
ESTÁS LEYENDO
BINTEEE ( 'Yata ce)
Ficción GeneralSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....